Gwamnatin Ta Adana Naira Biliyan 128 Daga Chajin Da Ake Yi Wa Bankuna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Ta Adana Naira Biliyan 128 Daga Chajin Da Ake Yi Wa Bankuna

Published

on


 

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar, tun lokacin data  kafa asusun na bai Daya (TSA) a cikin watan Satumbar  2015, ta samu adana jimlar naira biliyan 128, na chajin da bankuna suka sanya suke karba na don kula da kuDaDen na ma’aikatun da sassa da kuma sauran hukumomin gwamnati.

A bisa binciken da aka gudanar, kuDin chaji da-ban-da-ban harda na kula da kuDi wanda bankuna suka Dora saboda ajiyar kuDaDen gwamnati.

Har ila yau, binciken da aka gudanar a ofishin Akanta Janar na Kasa, ya nuna cewar, kafin fara yin shirin, gwamnati tana zuba naira biliyan huDu don a kula mata da asusun ajiyar ta da-ban-da-ban a wata dake bankuna.

A ranar Larabar data gabata, mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya tabbatar da wannan kuDin naira biliyan huDu da aka tara a bankin ta hanyar (TSA).

Yemi ya tabbatar da hakan ne a jawabin sa lokacin buDe taron Kungiyar Kwararru ta tara haraji ta Kasa(CITN).

A cewar Yemi, “mun jajirce wajen faDaDa wanzar da tsarin na  TSA da kuma tsarin kundin bayanai na albashi wanda aka tsara don tabbatar da ana bin doka da oda wajen kashe kuDaDen ‘yan Kasa.

Ya Kara da ciwar, tsarin na TSA yana da kyau sosai, musamman wajen bin doka da oda sabanin a baya da hukumin gwamnati suke yin ajiyar kuDaDen gwamnati a bankuna barkatai.

Ya Kara da cewar, sakamakon asusun na TSA,gwamnatin tarayya ta tara naira  biliyan huDu a wata,inda da wannan jimlar ta chajin, za ta tafi ne ga bankuna kasuwanci.

Akwai watanni talatin da biyu tsakanin watan satumbar shekarar 2015 da watan Afirilu na wannan shekarar.

A bisa naira biliyan huDu da ake tarawa a wata, jimmalar kuDin da a yanzu aka adana sun kai naira biliyan sha biyu a KarKashin shirin.

Shirn wanda aka fara wanzar dashi a watan satumbar shekarar 2015, an sanya sama da hukumomin gwamnati 900 a cikin tsarin, inda kuma aka rufe asusu guda 20,000 na banki da hukumomin gwamnati ada suke ajiyar kuDaDen gwamnati.

An kuma gano cewar, samada naira tiriliyan takwas aka cire daga bankunan zuwa CBN.

Har ila yau, an kuma gano cewar, shirin ya taimakawa asusun gwamnatin tarayya sama da  17,000.

Wakilin mu ya bankaDo cewa, tun lokacin da aka Kaddamar da shirin shekaru uku da suka shige, jimlar hukumomin gwamnati guda 1,674 aka sanya su a cikin tsarin na TSA.

Akanta Janar na tarayya Alhaji Ahmed Idris a cikin watan da ya gabata sama da naira biliyan 70 mallakar gwamnatin tarayya suke narke a bankunan da suka durKushe a Nijeriya.

A Kasidar da aka gabatar mai taken‘TSA: Madogaro wajen tabbatar da bin doka da oda na kashe kuDin gwamnati, Alhaji Ahmed Idris ya ce, tsarin na TSA ya taimakawa gwamnatin tarayya wajen kawar da matsalolin da suka shafi kashe kuDin gwamnati.

Akantan ya Kara da cewar, tsarin na TSA, ya haDa da dukkan kuDaDen da aka sanya a cikin kasafin kuDi har da na bayar da bashi da bayar da tallafi a KarKashin kulawar gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewar, dukkan kuDaDen da aka karba ta hanyar yin amfani da na’ura, inda aka tara naira tiriliyan 8.9 da kuma kuDin da suka shiga har zuwa yau da hukumin gwamnati guda 1,674 suka zuba.

Ya ce, tsarin na TSA yana da Kudurin magance yawan asusun da ake buDewa a bankuna sama da 17,000, banda sauran asusun ajiya a bankuna da basa yin aiki da gwamnati ta aro don biyan chajin, ganin cewar akwai sauran kuDi a asusun ajiyar banki na hukumomin gwamnati da aka samu tsaiko wajen  tura kuDin shiga da kuma kuDaDen da aka karbo da kuma sama da

naira biliyan 70 na kuDin gwamnatin tarayya da suka suka shige a bankunan da suka durKushe.

Akantan ya Kara da cewar, gwamnatin tarayya tana amfana sosai, sakamakon Kaddamar da tsarin na TSA.

Ya buga misali da cewar ta hanyar tsarin, gwamnatin tarayya ta ci nasara wajen daKile dukkan kuaDaDen da suke fita ba’a bisa Ka’ida ba.

Ahmed Idris ya bayyana cewar, baya ga wannan, tsarin na TSA ya kuma taimakawa gwamnatin tarayya rage karbo bashin da hukumomin gwamnatin tarayya ke yi barkatai da kuma baiwa gwamnatin sukunin adana kuDi dake da alaKa da karbar chaji.

Akantan ya kuma koka akan cewar, duk da nasarorin da aka samu ta hanyar tsarin na TSA, har yanzu akwai Kalubalen da ake fuskanta a wasu cibiyoyin gwamnatin tarayya.

A Karshe Ahmed Idris, ya zayyana wasu Kalubalan kamarbna rashin nuna halin ko in kula na masu ruwa da tsaki akan rawar da suke takawa da umarni masu cin karo da juna da rashin fahimtar alfanun TSA da tura kuDaDe masu da hukumomin gwamnatin tarayya keyi ta hanyar kuDaDen da aka ajiye a bankuna da tarnaKin da ake fuskanta wajen samun bayanan bankuna.

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!