Connect with us

KASASHEN WAJE

Iran Ta Bai Wa Kasashen Turai Wa’adi Kan Nukiliyarta

Published

on

 

Kasar Iran ta bai wa kasashen Turai kwanaki 60 domin gabatar mata da tabbacin cewar za su mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da su a shekarar 2015, bayan ficewar Amurka.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar, Abbas Araghchi ya bayyana haka, yayin da jami’an Iran ke shirin ganawa da wakilan kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya a gobe Talata.

Ministan Harkokin Wajen Iran Jabad Zarif ya ziyarci China a jiya Lahadi, in da ya gana da hukumomin kasar kafin wucewa zuwa Rasha da kuma Brussels.

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Turai da kuma kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da suka jagoranci kulla yarjejeniyar, sun ce har yanzu suna tsaye akan ta.

A bangare guda, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, a shirye suke su yi aiki da kawayensu na Turai domin daukar matakai kan Iran bayan ficewar kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar.

Pompeo ya ce, a shirye yake ya gabatar da sabbin kudirori domin dakile yadda Iran ke ci gaba da fadada ikonta a Gabas ta Tsakiya.

Sakataren ya ce, nan da ‘yan kwanaki ko makonni za su gabatar da sabbin kudirorin da za su yi tasiri kan kasar.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: