Connect with us

LABARAI

Kungiyar Masu Daukar Hoto (ZUP) Sun Ziyarci Sarkin Zazzau A Fadarsa

Published

on

 

A ranar littinin da ta gabata, shugabanni da kuma sauran mambobi na Kungiyar ma su Daukar hoto na lardin Zazzau, suka ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris a fadarsa da ke Birnin Zariya.

Tun farko a jawabinsa, shugaban Kungiyar ma su Daukar hoto a lardin Zazzau, Mista Moris Odemudia ya ce, sun ziyarci mai martaba sarkin ne, domin taya murnar cika shekara 43 a karagar masarautar Zazzau.

A kan haka shugaban Kungiyar ya Kara da cewar, wannan shekaru da mai martaba sarki ya yi shekaru day a kamata, duk wani bazazzagi da sauran al’umma su yi ko yi da shi, na samar da zaman lafiya da kowa ya san an samu a cikin kaDar Zazzaui da kuma Nijeriya baki daya Shugaban ya ci gaba da cewar,dukkanin addu’o’in da aka yi a lokutan cikar mai martaba sarki, da mu aka fara har aka kammala wannan taro ya zuwa kamala taron.Shugaban ya yi amfani da damar day a samu ya ce,Kungiyar ta naDa mai martaba sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris babban uban Kungiyar na har abada.

Shi ko mai martaba Sarkin Zazzau alhaji shehu Idris, nuna jin daDinsa ya yi da wannan Kungiya ta kai ma sa ziyarar ba zato, domin ta ya shi murnar cikarsa shekara 43 a karagar Zazzau.

Alhaji Shehu Idris ya yi kira ga ‘ya’yan Kungiyar, da su haDa kai mashugabannin Kungiyar dominwarware matsalolin da suke addabar wannan Kungiya, kamar yadda y ace said a haDin kai . domin ka das u sanya a cikin massalolin da bai shafe su ba.

A Karshe, mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya tabbatar wa shugabannin Kunhira dab a su duk goyon bayan da suka dace, domin su sami damar tallafa wa mambobinsu da kuma ayyukan da za su ciyar da musulunci gaba

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: