Connect with us

SIYASA

Salon Siyasar Gwamna Masari Abin A Yaba Ne –Dakta Malumfashi

Published

on

 

An bayyana Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, a matsayin gwarzo, jajirtattace kuma Dan siyasa mai kishin Kasa, wanda har abada tarihi ba zai manta da irin gudunmuwar ci gaba da ya kawo ma Kasar nan da Al’ummar Jihar Katsina ba, tun lokacin da yake bisa kujerar Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarraya, da kuma yanzu da yake riKe da muKamin Gwamnan Jihar Katsina.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC, kuma mai neman tsaya takarar kujerar Dan majalisar Wakilai ta Tarraya mai wakiltar Kananan hukumomin Malumfashi da Kafur, a majalisar Dokoki ta Tarraya, a inuwar jam’iyyar APC, Dakta Muktar Yaro Malumfashi, a yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna.

Dakta Muktar ya ci gaba da bayyana cewa, “irin salon siyasar Alhaji Aminu Bello Masari, shi ne babban abin da ya ja hankalina na tsunduma fagen siyasa, domin na ga irin Dimbin ayyukan ci gaban Al’umma da wannan bawan Allah ya kawo ma mutanen Jihar katsina, tun lokacin da yake bisa kujerar Shugabancin Kakakin Majalisar Dokoki ta Tarraya, da kuma Uwa Uba yanzu da Allah ya bashi mulkin Al’ummar Jihar katsina.”

Dan takarar Majalisar Wakilan ya Kara da cewa, “ Na kasance ina koyi da siffantuwa da halaye na mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, wanda a zamanin da ya wakilcin yankin a Majalisar Tarayya, kowa ya shaida irin gudummuwar da ya bayar wajen ci gaban Kasa, domin shi ne ya jagoranci yaKi da batun tazarce na tsohon Shugaban Kasa Obasanjo, kuma Jama’ar Kananan hukumomin Malumfashi da Kafur da kuma Jihar Katsina baki Daya, sun tasirantu da wakilcin shi a wancan lokaci, hakanan Jama’ar Arewa suna Allah san barka. Amma tun bayan barin Aminu Masari Majalisa, Kananan hukumomin Malumfashi da Kafur suka shiga cikin tasku, saboda rashin iya wakilci na waDanda suka biyo bayan Masari, amma da yardar Allah idan na kai ga wannan kujera Jama’ar Malumfashi da Kafur za su zamo abin alfahari da kwatance a tsakanin sauran Kananan hukumomin dake Jihar Katsina baki Daya.”

Darka Muktar Yaro Malumfashi, ya kuma Kara da bayyana cewa, “A ko da yaushe idan na juya da kallon irin yadda rayuwar Jama’armu na Kananan hukumomin Malumfashi da Kafur dake Jihar Katsina, musanman Matasa ke dake Kara shiga cikin wani mawuyacin hali na koma baya ta fuskar ilimi da rashin ayyukan yi, wanda hakan ya biyo bayan rashin samun kyakkyawan wakilci a Majalisar Tarayya, wannan da kuma wasu dalilai na Daya daga cikin abin da ya zaburar da ni na yanke shawarar fitowa takarar Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar wannan yankin, domin bayar da tawa gudummuwar wajen ceto rayuwar Jama’ar Kananan Hukumomin Malumfashi da Kafur daga halin tsaka mai wuya da suka tsinci kansu “.

Dakta Mukhtar Malumfashi, ya ci gaba da cewar, “Kananan hukumomin Malumfashi da Kafur suna fama da rashin ingantaccen wakili a Majalisar Kasa dake Abuja, lamarin da ya sanya, duk da irin arzikin Kasa da Matasa da Allah ya yi wa yankin, sai ya zamana hakan na neman tashi a banza, domin an bar Matasan yankin a baya ta bangarori da dama, wannan shi ne babban abin da ke ci mani tuwo a Kwarya kenan wanda ya sanya na yanke shawarar tsayawa takara domin ceto rayuwar matasa da sauran Jama’ar yankinmu.”

Da ya dawo batun inganta rayuwar Mata da Matasa kuwa, Dakta Mukhtar Malumfashi, ya bayyana cewa, tuni ya samar da wuraren koyar da sana’o’i ga Matan yankin baki Daya, yadda za su zamanto masu dogaro da kansu da kuma taimakawa Mazajensu, kuma ya Kara da bayyana cewa, da yardar Allah, zai Kara faDaDa wannan shiri yadda zai kasance kowace Mace dake Kananan Hukumomin Malumfashi da Kafur, ta tsayu da kafafuwanta har ta Dauki Dawainiyar wasu ta fuskar koya musu sana’o’i idan Allah ya cika masa burinsa na zama zabbaben Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kananan hukumomin Malumfashi da Kafur a majalisar dokoki ta Kasa dake Abuja.

Daga Karshe, ya Kara da janyo hankalin Daukacin Matasan Jihar katsina da kuma Nijeriya baki Daya, da cewa lokaci ya yi da zasu dawo daga rakiyar batagarin ‘yan siyasa masu fakewa suna basu Kwayoyi da makamai wajen yin bangar siyasa. A cewarsa, yanzu lokaci ne na sanin ciwon kai da kuma KoKarin yin gwaninta ta hanyar gasar karatu ko fannin KirKire KirKire sana’ar fasaha irin ta zamani wanda duk duniya da waDannan Matasa gwamnatin ke alfahari.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: