Sama Da Yara 20,000 Ba Su Zuwa Makaranta A Nasarawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Sama Da Yara 20,000 Ba Su Zuwa Makaranta A Nasarawa

Published

on


 

Sakamakon rikicin Kabilanci da ya mamaye kudancin Jihar Nasarawa Wanda ya shafe Kananan hukumomi guda biyar Lafia Doma Keana Obi Awe . yayi sanadiyar sanya dubban yara Kanan zaman dirshen a gidajensu.rikicin da ya sanya malaman Piramare gudu domin niman mafaka shine ya sanya iyayen yara janye ya’yansu domin gudun kada rikicin ya afkamasu .

Sauran yaran suna sansanin gudun hijira tare da iyayensu .mafiya yawan yaran dake sansanin gudun hijira suna zamane batare da samun ilimi a ko da makarantu na wucin gadi ba.

Hukumar bada ilimin baidaya ta Jihar Nasarawa SUBE tace duk da cewa akwai wanan matsalar na rashin karatun yara amma adadin da aka bada ba lallai ne yakai hakan ba saboda ba kididiga akayiba tana iya yuhuwa yawuce hakan ko kuma ya gaza hakan .

Da take jawabi ga manema labarai Hajiya Hadiza Alakayi Wanda ta wakilci Shugaban ilimin bai daya na Jihar Nasarawa Alhaji Musa Muhammad Dan Azumi, ta ce, sun samu wanan labari kuma dama suna da tabbacin hakan zai iya faruwa .

Sakamakon haka nema hukumar kula da Ilimin baiDaya na Jihar ta yi gaggawan samar da kwamitin da zasu binciko Susan adadin yaran sannan ta san matakin da ya kamata ta Dauka.

Ta Kara da cewa adadin yawan Daliban da ake fadi ba lallaine ya kai haka ba tana iya yuhuwa yakai ko ya wuce haka , shi ya sa suka gana da Shugabannin makarantun domin su san yadda za a yi Dalibai su dawo su ci gaba da karatunsu tunda Allah ya sa yanzu ansamu zaman Lafiya a wadanan yankunan da rikicin ya shafa.

 

Advertisement
Click to comment

labarai