Connect with us

LABARAI

Shugabancin APC: Kotu Ta Kori Karar Da Ke Kalubalantar Karin Wa’adi Ga Oyegun

Published

on

 

Kotun tarayya dake Abuja tayi fatali da Karar dake Kalubalantar KoKarin Karin wa’adin da aka nemi yi wa shugaban jam’iyyar APC Cif John Odigie-Oyegun da sauran muKarabansa na Kasa tare da sauran shugabannin jam’iyyar a matakin jihar da Kananan hukumomi da kuma shugabannin jam’iyar na unguwanni.

A hukunci biyu daya zartasa, mai shari’a Nnamdi Dimgba, ya ce, Karar bata da wani makama kuma kamar wasan yara ne, saboda jam’iyyar nada haKKi da ikon Kara wa shugabanninta wa’adi a duk lokacin data ga dama.

Mai shari’an ya Kara da cewa, kotu ta lura da cewa, jam’iyyar APC ta fara gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a matakin unguwanni da Kananan hukumomi a dukkan jihohin tarrayar Kasar nan, ya kuma ce, kotu ta lura da cewa, a halin yanzu jam’iyyar ya aiyyana ranar 19 ga watan Mayu domin gudanar da babban taronta na Kasa.

Ya ce, kotu bata bayar da hukunci a kan wani da bashi da mahimmanci, kotu na amfani ne da abin da yake a zahirance mai mahimmanci ne.

AlKalin ya kuma bayyana cewa, da KoKarin  Karin wa’adin da aka yi ya tabbata, da hakan kai tsaye ya sabawa tsarin mulkin Nijeriya dana jam’iyyar APC gaba Daya.

Shugabanin jam’iyyar sun Kara wa kansu wa’adi a wani taron shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu halarta a ranar 27 ga watan Fabrairu 2018, ana sa ran wa’adin nasu zai Kare ne a ranar 30 ga watan Yuni 2018 kuma an so a Kara musu shekara Daya ne.

Wani Dan jam’iyyar ne daga jihar Imo, Mista Okere Uzochukwu, ya shigar da Kara mai lamba FHC/ABJ/CS/219/2018 ranar 2 ga watan Maris 2018 yana Kalubalantar KoKarin Karin wa’adin. Kara na biyu kuwa, wasu ‘yan jam’iyyar 4 ne dake hanKoron neman shugabancin jam’iyyar suka shigar da ita ranar 8 ga watan Maris 2018, Karar mai lamba FHC/ABJ/CS/237/2018 na Kalubalantar KoKarin da shugabannin jam’iyyar ne keyi na Kara wa kansu wa’adin ci gaba da mulki.

A wani taro daban shugaba Buhari ya shawarci kwamitin zartaswa na jam’iyyar dasu kaucewa maganar Karin wa’adin saboda haka zai iya jefa jam’iyyar cikin matsaloli a gaba shari’a.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: