Connect with us

SIYASA

Siyasa A Yau

Published

on

 

Da farko me za ka ce dangane da Korafin da jama’a ke yi cewar har yanzu ba su gani a Kasa ba dangane da dalilan da ya sa suka zabi wannan gwamnatin?

Kowa ya san yadda gwamnatin nan tazo kan karagar mulki da irin matsalolin da ta gada, in ko haka ne ba ya yiwu wa ka ba ta maki a cikin shekaru biyu, domin idan ka yi la’akari da jihar ba mu da hanyoyi na Kwarai, ba mu da asibitoci na Kwarai, makarantun mu sun lalace, ba wani da za ka Dauka ka nuna wa duniya kuma an aza harsashin gyara tun lokacin mulkin marigayi Abdullahi Kure, waDanda suka gaji kuren ba su mayar da hankali akai ba, shi maigirma gwamna da yazo ya iske basussuka wanda dole cikin Dan abin da yake shigo wa ake zaftare wannan bashi.

Da Alhaji Abubakar Sani Bello ya zo ya sha alwashin duk wani abu mai anfanin al’umma da aka fara aka watsar sai ya kammala, kuma gaya Dan abin da ke shigo wa can ake narkar da su ka ga dole sai an bi a hankali wanda duk zai yiwa gwamnatin adalci zai yabawa gwamnatin nan akan waDannan abubuwan da na zayyano ma ka gane.

 

Ba ka ganin cewar wannan bai isa ya zama hujja ba, duba da cewar ita romon dimukuraDiyya waDanda ake muka ya kamata su bayyana shi ba ita gwamnatin ba?

Kasan ita siyasa dole ne a yi adawa, amma ya kamata ita adawar nan ta zama ta ilimi da fahimta ka gane, saboda haka idan kana sakamakon yadda abubuwan ke tafiya za ka iya tantance komai tunda kaima Dan jihar ne kuma komai a fili yake. Idan ka duba kusan duka manyan garuruwan jihar nan in ban da ayyukan da maigirma Kure ya yi na samar da hanyoyi da gyaran makarantu, asibitoci, ba wani abu da aka sake kafawa sai bayan zuwan Abubakar Sani Bello, ka duba wasu daga cikin makarantun mu musamman ma na kimiyya da fasaha da na koyon aikin jinya kai da kan ka za ka yabawa gwamnatin nan, dubi yadda bangaren ilimi ya lalace ba Kwararrun malamai balle kuma kayan aiki, kan haka mai makon a kori mutane aiki kamar yadda wasu jahohin suka yi, sai aka KirKiro makarantun horar da malamai ta yadda nan ‘yan shekaru kaDan sai malamai sun zama abin alfahari, sassa uku na jihar nan ko ina an kafa wannan cibiya ka ga ba aikin rana Daya ba ne ai.

Amma akwai Korafin rashin aiki ga matasa wanda wannan ba Karamin barazana ba ne ai.

Haka ne, to ai ganin gwamnati ba ta iya baiwa kowa aiki yasa maigirma gwamna ya fifita harkar noma wanda an gayyato kamfanoni wanda suka yi haDin guiwa da ita gwamnatin kuma kashi saba’in na waDannan kamfanoni matasan mu ne ke tafiyar da su, nan cikin azumin nan mai kamawa farashin abinci zai sauKi saboda samuwar shinkafar da aka noma a jihar kuma za ta shiga kasuwa. Na biyu muna da cibiyoyin kowon sana’o’in hannu wanda a baya sun durKushe kuma maigirma gwamna bayan zuwansa sun farfaDo yanzu dubban matasa ne ke cin moriyar shirin, abin bai ma tsaya akan gwamnati ba hatta makusantan gwamna sun jajirce da abin hannun su suna bunKasa shirin.

Akwai masu ganin cewar bai kamata a yabawa ita gwamnatin ba domin ko wasu muhimman abubuwa da suke mallakin gwamnati ba su da nagartar yabo.

Ai ya sa makarantar horar da ma’aikata jinya ta Bida aka tabbatar hukumar lafiya ta gwamnatin tarayya ta amince da ita wanda duk shekarun da aka baro baya tamkar gata nan ne, sai ga ta Kontagora da aka samar yanzu, ko waDanda ke minna ta kimiyyar lafiya da ta horar ungwazoma aka tabbatar an Daga darajarsu. To ire-iren ayyukan da aka mayar da hankali ke nan martaba abin da yake haKKin gwamnati da inganta tsarin aikin gwamnatin.

Rashin aiki na daga cikin abin da yasa matasa faDawa bangar siyasa da shaye-shay, kuma ana zargin cewar ku ‘yan siyasa laifin ku ne.

 

Ina jaddawa matasa ‘yan uwana cewar APC tazo da nufin canji ne daga turbar da muka fito zuwa nagartacciyar turba, dan haka duk Dan siyasar da yace maku ku fito dan yin bangar siyasa to ya turo maku Dansa ya zama jagora, bai yiwuwa ‘ya’yansu na Ketare suna karatu mu kuma a gurbata mana rayuwa.

Ya zama wajibi mu natsu mu faDi wa junanmu gaskiya, mutum bai samun kamala ya yi kyakkyawan nazarin abin da zai taimaki rayuwar su sai ya inganta tunanin sa, da farko dai mu koma makaranta sannan mu nemi sana’a domin ita siyasa hanya ce ta haDuwar jama’a da tunanin yadda za a gina Kasa, ban ko tunanin mai shaye-shaye zai iya natsuwar da zai inganta rayuwarsa balle ya inganta na wani.

Gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello tazo da shirin da zai inganta rayuwar matasan, shi yasa aka KirKiro cibiyoyin koyon Sana’ar hannu ga wanda ya yi karatun da ma wanda bai yi ba, sai in ce a Neja ba a taba samun gwamnatin da ta sanya tubalin inganta rayuwar al’umma ba kamar wannan gwamnatin.

Wanne Karin haske za ka yi ma waDanda ke ganin kamar ba a yi komai ba.

Kamar yadda na fadi ne a baya, tun lokacin siyasa muke wajibi ne ayi adawa amma adawar nan ta zama ta gaskiya, domin gwamna a koda yaushe yana jin Korafe-Korafen jama’ a kuma akansu ake aiki. Dan haka duk wanda zai faDi wata magana indai gaskiya ce ai kamar tunatarwa ce ya yi.

Ba a hana adawa ba, kuma ai ita adawa ba Kiyayya ba ce, tuni ga mai mulki ina jaddada ma cewar na gamsu da muradun gwamnatin nan domin ta daKile kafafofin da ke yoyo ta yadda nan gaba al’umma zasu ga anfanin hakan, domin muradu ne da manufofi masu kyau.

 

 

 

 

Da farko me za ka ce dangane da Korafin da jama’a ke yi cewar har yanzu ba su gani a Kasa ba dangane da dalilan da ya sa suka zabi wannan gwamnatin?

Kowa ya san yadda gwamnatin nan tazo kan karagar mulki da irin matsalolin da ta gada, in ko haka ne ba ya yiwu wa ka ba ta maki a cikin shekaru biyu, domin idan ka yi la’akari da jihar ba mu da hanyoyi na Kwarai, ba mu da asibitoci na Kwarai, makarantun mu sun lalace, ba wani da za ka Dauka ka nuna wa duniya kuma an aza harsashin gyara tun lokacin mulkin marigayi Abdullahi Kure, waDanda suka gaji kuren ba su mayar da hankali akai ba, shi maigirma gwamna da yazo ya iske basussuka wanda dole cikin Dan abin da yake shigo wa ake zaftare wannan bashi.

Da Alhaji Abubakar Sani Bello ya zo ya sha alwashin duk wani abu mai anfanin al’umma da aka fara aka watsar sai ya kammala, kuma gaya Dan abin da ke shigo wa can ake

 

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

A jiya ne tsohon Ministan ayyukan na musamman ‘Special Duties’ a zamanin Jonathan, Alhaji Kabiru Tanimu a ya kira wani taron ganawa na shuwagabannin Kananan hukumomi 21 da ke Jihar Kebbi, da kuma shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Kebbi da kuma ke da mazabu 225 a jihar domin ya nemi goyon bayansu kan kiraye -kirayen da ake yi masa na tsayawa takarar kujerar shugabancin Kasa a zaben 2019 mai zuwa, inji shi.

Ministan ya bayyana aniyar tasa ta tsayawa takarar kujerar shugabancin Kasar nan a zaben 2019 mai zuwa ga manema labarin ne a jiya a Birnin-kebbi yayi gudanar da taron ganawa ta musamman da shugabannin jam’iyyarsa ta PDP kama tun daga shugabannin Kananan hukumomi har zuwa matakin na jihar domin neman goyun bayansu kan kudurin nasa na neman a tsayar dashi Dan takarar kujerar shugabancin Kasar nan a KarKashin jam’iyyar PDP wanda a nan take shuwagabannin suka amince da buKatar shi da ya gabatar a gare su.

Taron ganawar na musamman ya gudana ne a sakatariyar ofishin na jam’iyyar PDP ta jihar Kebbi da ke a Birnin-kebbi kusa da tsohuwar tashar mota a cikin babban Birnin jihar.

Alhaji Kabiru Tanimu ya ce; “Na nemi shawarwari daga mutane da dama kafin na gudanar da wannan taron na musamman da shugabannina na jam’iyyar PDP a wannan jihar da kuma wasu shugabannin kama tun daga na addinai, Kungiyoyi na gwamnatin da kuma masu zaman kansu da kuma sauran irin-irinsu wanda kuma dukkanninsu sun bani Kwarin gwiwa da kuma goyon baya ga tsayawa takarar kujerar shugabancin Kasar nan, saboda haka shi ne na ga ya dace na bayyanawa abokai kuma ‘yan uwa na siyasa.”

Haka kuma tsohon Ministan Kabiru Tanimu ya ce, “dalilansa na ganin cewa ya dace ya tsaya takarar kujerar shugabancin Kasar nan shi ne cewa, jam’iyyarsa ta PDP ta yi mulki shekaru goma shashida a Kasar nan inda ta samar da tsaro ga ‘yan Kasa ta kuma samar da ayyukkan yi ga jama’ar Kasar nan da kuma tabbatar da cewa arzikin Kasar nan ya samu ta hanyar bada dama ga masu saka jari na Kasashen waje sun saka jari a cikin Kasar Nijeriya da kuma samar da walwala ga mutanen Kasar ta Nijeriya “ .

“Amma yau an wayi gari gwamnatin APC ta lalata duk abin da jam’iyyar PDP ta gyara ta kuma barma ‘yan Kasa domin amfana dashi”.

Har wala yau ya ce; “A Kasar nan yau babu tsaro domin gwamnatin APC takasa magance matsalar rikicin fulani makiyayay da manoma da kuma yawan kashe-kashe da ke adabar mutanen Nijeriya a wasu jahohin Kasar nan irin jihar Zamfara, Taraba, Benuwai da kuma kaduna a birnin gwari da kuma sauransu.

“Haka kuma gwamnatin APC na ikirarin yaki da cin hanci da kuma rashawa amma kuma cikin gwamnatin ta shuwagabannin APC Din zakaga cin hanci da kuma rashawa a tsakaninsu fiye da duk wata gwamnatin da ta gabata a Kasar nan wanda abin kunyane da kuma banmamaki ga ‘yan Kasar nan”.

Buga da Kari ya ce; “jam’iyyar da ta kasa gudanar da zaben wakilan mazabun unguwanni da kuma na Kananan hukumomi a duk faDin Kasar Nijeriya wannan abin kunya ne, balle su ce suna iya fuskanta sauran wasu jam’iyoyin Kasar nan a zaben 2019 mai zuwa”.

Saboda haka ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar PDP a duk faDin Kasar nan da su jajirce wurin ganin cewa sun kada jam’iyyar APC a duk jihohin Kasar nan”.

“Daya daga cikin dalilan da ya sa na tsaya takarar kujerar shugabancin Kasar nan domin na kawo gyara ga abubuwan da na faDa tun farko cewa, gwamnatin APC ta lalata da kuma tabbatar da na lashe kujerar Buhari a zaben 2019 mai zuwa” inji shi.

Hakazalika ya ci ga da bayyana cewa; “Jam’iyyar APC a Kasar nan ba ta samar da komi ba bayan cin hanci da rashawa da kuma rikice-rikicen Kabilanci a Kasa da kuma salwantar rayukan jama’ar Kasa da ba su ji ba su gani ba”.

Daga Karshe ya yi kira ga ‘yan Kasar nan da su kara bai wa jam’iyyar PDP dama ga shugabancin Kasar nan duk da yake munsan akwai wasu ‘yan kurakurai da suka auku amma ya zama wajibi mu gyara domin mutanen Nijeriya sun san irin ayyukan da gwamnatin PDP ta yi a Kasar nan da kuma jin daDi da walwala da aka samar ga jama’ar Nijeriya saboda haka a zabi jam’iyyar PDP a zaben 2019.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: