Tawagar Jam’iyyar GPN Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Gidan Khalifa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Tawagar Jam’iyyar GPN Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Gidan Khalifa

Published

on


 

A yammacin ranar lahadi ne tawagar jam’iyyar ‘Green Party of Nigeria’ GPN Karkashin me neman takarar Gwamnan jahar Kano. Alhaji Abdulkarim Abdulsalam Zaura suka kai ta’aziyyar rasuwar Sheik Khalifa Isyaka Rabiu ga iyalansa.

A.A Zaura wanda ya ce sun je ta’aziyyar ne a madadinsa da uwar jam’iyyar ta Kasa akan wannan babban rashi da akayi wanda cike gurbinsa abune mai wahala.

Zaura ya ce tunda suka taso har suka girma su ka ga a na hidimar Kur’ani a gidan Khalifa don haka nema ake kiran gidan da suna gidan Kur’ani, suna kuma fatan albarkar Kur’ani da ya tafi ya bari ya ci gaba da yaDo a tsatson wannan gida da jihar kano, Kasa da Afirka gaba Daya.

Alhaji A.A. Zaura ya yi nuni da cewa lallai an yi babban rashi wanda ya kamata ya zama mutuwarsa ta yi babban darasi. Mutane su tsaya su rungumi gaskiya da bin Ka’idoji da Allah ya shimfiDa a duk abin da Dan adam zai yi.

Ya ce, shi Khalifa ta sa ta yi kyau yayi aikin alkhairi, ya bar baya me kyau duk rayuwar khalifa hanya ce ta gaskiya ya bi ta riKo da Kur’ani. Duk abin da mutum zai yi a rayuwa siyasa, kasuwanci, mulki da zamantakewa a tsakanin al’umma idan Allah ya bai wa mutum ya riKe gaskiya. Da fatan dukkan al’umma za su ci gaba da koyi da abin da ya bari.

 

 

Hisba Ta Kai Samame Unguwar

Advertisement
Click to comment

labarai