Connect with us

LABARAI

Za Mu YI KoKarin Ganin Umar Datti Ya Amsa Kiran Al’ummar Dala

Published

on

 

 

An bayana matashin Dan jaridar nan Umar AbdulKadir Datti a matsayin Dan kishin Kasa wanda ya fito daga Karamar hukumar Dala a Jihar Kano, wannan wajabi ya fito daga bakin Hajiya Salamatu Sabo Bakin Zuwo, a lokacin da take Karin haske kan gogewar matsahin Dan jaridar.

Hakazalika al’ummar Karamar hukumar Dala a Jihar Kano sun sha alwashin cewa sai sun matsa lamba ga Malam Umar AbdulKadir Datti wajen ganin wannan matashin Dan jaridar domin wakiltarsu a majalisar dokokin Jihar Kano. Wata Kididdiga da aka gudanar wanda aka gano cewa shi ne matashin Dan jarida mai hazaKa kuma mafi Karancin shekaru a fadin Najeriya dama Afirica baki Daya, da ke gabatar da shiryi shiryen siyasa a gidan Radion EDpress.

Saboda waccan gogewa da kuma Kaunar ci gaban al’umma yasa jama’ar Dala ke ganin cewa ba wanda ya fi da cewa da wakiltarsu a Majalisar dokokin Jihar Kano sai Malam Umar AbdulKadir Datti wanda Gogaggen matashin Dan jarid ne dake aiki da gidan Radio eDpress da ke birnin kano.

 
Up Next

Hisba Ta Kai Samame Unguwar Danbare Da Dakatsalle A Kano Daga Na’ima Abubakar, Kan Rundunar Hisba ta Jihar Kano a KoKarin da ta ke na umarni da aikin alhairi da hani da mummuna aiki, ta kai wani samame unguwar Danbare dake Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, Jami’in da ya jagoranci tawagar da takai samamen Malam Sani Zailani ya bayyana cewa an samu nasarar damKe samari da ‘yan mata waDanda ke gudanar da harkokin baDala, Shaye Shaye da kuma masu yawon ta zubar a Unguwar Danbare. Alokacin Samamen rundunar ta Hisba tayi nasarar cika hannu da waDanca matasan da aka yi ittifaKin cewa suna wannan baKar ta’ada ne ba tare da sahalewar iyayensu ba, Hukumar wadda kullum aikinta shi ne ganin al’umma ta tsarkaka daga munanan ayyukan da ake fatan ganin an samu ingantacciyar al’umma. Haka zalika Rununduna ta Hisba ta sake kai irin wannan samame garin Dakatsalle dake Karamar Hukumar Bebeji inda anan ma hukumar tayi sa’ar damKe wasu masu yawon tazubar wandaacikinsu har akwai waDan ke Dauke da ciki, da aka tambayi mai Dauke da cikin ko ina waDanda yayi mata cikin sai tace ya gudu ya barta, amma dai da yawa na nuna cewa suna sana’ar sayar da abinci ne. Darakta Hukumar Hisbarna Jihar Kano Malam Abba Sa’idi Sufi da yake Karin haske kan wannan samame da hukumar takai y atabbatarwa da wakiliyarmu cewa wannan na cikin ayyukan Hukumar Hisba, saboda haka ya bayyana cewa za’a tantance waDanda wannan shi ne kamun farko da aka yi masu, inda za’a yi masu wa’azi tare da yin nasiha garesu, sauran kuma masu kunnen Kashi bayan kammala bincike za’a gurfanar dasu gaban kulliya domin girbar abinda suka shuka. A tattaunawar da aka gudanar da wasu waDanda aka kama sun bayyana nadamar su tare da roKon yi masu afuwa bisa alKawarin cewa ba zasu sake aikata irin wannan laifi ba

Don't Miss

Gwamna Bagudu Ya Yi Kira Ga Gaggauta Kammala Hanyar Kontagora Zuwa Yauri

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: