Connect with us

KASASHEN WAJE

Zanga-Zangar Falasdinawa Ya Kazance A Yayin Da Amurka Ta Bude Ofishin Jakadancinta A Birnin Kudus

Published

on

 

Ma’aikatar lafiyar Gaza ta bayyana cewa dakarun Israila sun harbe akalla Falasdinawa 16 har lahira a kan iyakar Gaza inda dubban mutane suka hadu domin yin zanga-zanga kan shirye shiryen da Amurka ke yin na dauke ofishin jakadancin ta daga Tel Abib da maida shi Kudus.

Ma’aikatan lafiyar ta ce akalla mutane 500 ne suka raunana daga harbin bindiga. Mace-macen ya kara yawan Falasdinawan da sojojin Isra’ila suka kashe a cikin makonni shida da suke ta zanga zanga zuwa fiye da mutane 50.

Masu sharhi sun zargi Israila da bude wutar da suka yi, inda su kuma sojojin Yahudawan suka ce hakan ya zama tilas saboda tsaro, domin mutanen na kawo barazana ga shingen kan iyakar.

Masu zanga zangar sun jefa abubuwa da dama ta kan iyakar kuma sun kona tayoyi a gaban ofishin jkadancin da aka bude a yau din. An rufe Wuraren san’a da makarantu da dama a garin na Gaza.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: