Connect with us

LABARAI

An Gurfanar Da Shaikh Zakzaky Kotu A Kaduna

Published

on

An gabatar da Jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatu Ibraheem a gaban kotu yau a garin Kaduna.

Da sanyin safiyar ranar talatar ne aka dauko Malamin daga in da ake tsare da shi a Abuja zuwa garin Kaduna don gabatar da shi din a gaban kotu. An dai gabatar da shi ne a karkashin mai shari’a Kurada, a babbar kotun ta 4 ta jihar Kaduna da ke Titin Ibrahim Taiwo. A kwanan baya ne dai Shaikh din ya ki amincewa.

Lokacin da aka kira karar, Lauya mai gabatar da kara, Barista Bayero Dari ya nemi a daga shari’ar, saboda sun yi kokarin ganin sun kai takardar tuhuma ga sauran mutane biyu din da ake kara amma ba su sami nasara ba.
Sai dai Lauyan Malam Zakzaky, Barista Madwell Kyon, ya bayyana cewa Lauyoyin Gwamnati ba su yi niyyar kai sammacin ba domin sun san inda wadannan mutane suke kuma ba su nemesu ba.
An yi ta gardama tsakanin lauyoyin biyu har sai da alkali ya sanya baki sannan suka yi shiru. In da daga baya alkaali ya amince da dage karar zuwa mako daya don a kai musu takardar don ci gaba da yin shari’ar. Amma wanda ake kara Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa a dage shari’ar har sai bayan Sallah saboda azumi ya riga ya matso nan take alkali ya amince da hakan. In da aka dage shari’ar har zuwa 21 ga watan Yuni mai zuwa.
Tun kafin nan, Lauyoyin da ke gabatar da kara sun nemi da kotu ta basu dama a ci gaba da tsare Malamin a hannun jam’ian tsaro na DSS a Abuja. Don haka Lauyan Madwel Kyon, wanda ke rikewa Femi Falana (SAN) ya tambayi Malam ko ya amince da hakan? Malamin ya bayyana cewa ba matsala. Don haka alkali ya nemi da a mayar da Malamin wajen DSS a Abuja.
Sai dai kuma Lauyoyin Malamin sun nemi da a basu damar ganin Malamin duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Don haka alkali ya nemi da DSS su tabbatar duk lokacin da Lauyoyin Malam ke son ganinsa sun sami ganinsa. Don haka Lauyan Gwamnati ya ce sun amince da hakan amma duk lokacin da Lauyoyin ke son ganin Malamin to su ba su kwanaki uku.
Jim kadan da kammala zaman yau, Shaikh Abdulhamid Bello, wani Malami daga cikin kungiyar ta ‘yan uwa musulmai ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin shaikh Ibraheem Zakzaky da ta ke tsare da shi tun shekaru sama da biyu da suka wuce. Ya ce sakin Malamin ne kadai mafita ga gwamnatin kasar nan da ta shiga cikin rudu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: