Buhari Ga Talakawa: Ba Zan Zalunce Ku Ba, Ba Kuma Zan Bari A Zalunce Ku Ba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Uncategorized

Buhari Ga Talakawa: Ba Zan Zalunce Ku Ba, Ba Kuma Zan Bari A Zalunce Ku Ba

Published

on


 

Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa, zai ci gaba da yin iya bakin kokarinsa domin hana kansa da duk wani mutum zaluntar talakawan wannan kasa.

Buhari ya yi wannan furuci ne a jiya bayan kaddamar da kudin akwati kimanin naira milyan 176.350 wadda aka gabatar jiya a filin taro na Malam Aminu Kano dake birnin Dutse.

Ya ce, kamar yadda gwamnatin APC ta kuduri aniyar tabbatar da adalci, gaskiya da rikon amanar al’ummar wannan kasa to babu ko shakka zan iya bakin kokarina wajen kare hakkinku a duk matakin da zan iya.

‘’Inaso in tabbatar muku cewa, da yardar Allah, ba zan zalunceku ba, ba kuma zan bari wani mutum ya zalunce ku ba, zan yi iya bakin kokarina wajen kare hakkinku gamida tabbadar da adalchi a tsakaninmu baki daya’’ inji shugaba Buhari.

‎Haka shugaba Buhari ya yabawa al’ummar wannan kasa bisa fuskanta da suke nunawa wannan gwamnati duk da irin halin kuncin da a cewarsa tsohuwar gwamnata ta jefa al’umma a ciki.

Sannan ya kuma gamsu da yadda al’ummar wannan kasa musamman ‘yan jihar ta Jigawa suka karbi noma hannu biyu gami da habaka‎ shi wadda a cewarsa wannan zai taimaka matuka gaya wajen farfado da tattalin arzikin wannan kasa tamu baki daya.

Shi kuwa da yake nasa jawabin a lokacin taron, gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ya ce wadannan kudade za’a dunga turasu kowacce akwatu a kowanne wata wadanda yawansu ya kai naira dubu 50 zuwa 100 domin gudanar da kananan ayyuka.

Gwamnan ya ce, yin hakan zai taimaka matuka gaya wajen magance kananan matsaloli kamar gyaran rijiyoyin bada ruwan sha, masallatai, motocin lafiya da dai sauransu.

Haka kuma gwamnan ya yabawa shugaba ‎Buhari bisa ceto wannan kasa da yayi daka tabarbarewar tattallin arziki gamida dorata kan tirba ta gaskiya mai dorar da ci gaba.

Daga karshe ya yaba wa dubban al’ummar da suka tarbi shugaba Buhari‎ gamida rokonsu bisa bashi dama a karo na biyu domin dorewar ci gaba da bunkasar tattalim arziki.

Advertisement
Click to comment

labarai