Fashola Ya Kaddamar Da Tashar Wuta Mai Karfin MVA Dubu 40 A Adamawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Fashola Ya Kaddamar Da Tashar Wuta Mai Karfin MVA Dubu 40 A Adamawa

Published

on


Ministan ma’aikatun wuta, ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola, ya kaddamar da aiki da tashar wutar lantarki mai karfin MVA dubu arba’in a garin Mayo-Belwa, cikin karamar hukumar ta  Mayo-Belwa a jihar Adamawa.

Da yake jawabi a bukin Fashola wanda babban sakataren ma’aikatar wuta ta tarayya Mista Louis Edozei, ya wakilta ya ce aikin da gwamnatin tarayya ta himmatu dashi shine  kokarin samar da ingantacciyar wuta a kasar.

Ya ce “wannan kaddamar da tashar wutar lantarki yana cikin aikin da gwamnatin tarayya ta sa a gaba, duk wata muna kaddamar da tashar wutar lantarki a wannan bangare na wuta domin amfanin jama’a.

” muna zama da kwararru kuma suna aiki dare da rana na ganin sun kawo karshen matsalar wuta a gurare daban daban, domin maisheda wannan kasa cikin wadataccen wutar lantarki” inji Louis.

Ya ce babban kalubalen da suke fuskanta itace yadda zasu cimma wannan manufa ta shugaba Muhammadu Buhari, don haka ya ce kamfanin samar da wutar shiyar jihar na kokarin kaiwa ga cimma wannan manufar.

Ministan ya kuma yaba da kokarin shugaban kamfanin samar da wutar lantarki ta kasa shiyar yankin (YEDC), da cewa ya’yi amfani da kwarewarsa wajan daukaka matsayin kudaden shigan da kamfanin ke samu duk wata.

Shima da yake jawabi shugaban kamfanin samarwa da raba wutar lantarki ta kasa shiyar jihar, Injiniya Baba Umara Mustafa, ya ce yayi matukar farin ciki da bude tashar wutar.

Ya ce “lamarin zai taimaka mana wajan samar da wuta mai inganci ga jama’ar yankin kananan hukumomin Jada, Ganye, Mayo-Belwa da Numan, saboda haka ba zamu Iy nuna farin cikinmu ba” inji shi.

Da yake jawabi tunda farko shugaban sashen Transmission Company of Nigeria (TCN) a jihar Usman Gur Mohammed, ya ce wannan shine matakin farko a jihar, zasu ci gaba da kafa tashushin wutar ingata wuta ga mutanen karkara.

Advertisement
Click to comment

labarai