Connect with us

LABARAI

Gwamna Da Wasu ’Yan APC Sun Share Hanyar Kassara Jam’iyyar A Bauchi –Ali Dogare

Published

on

Wani magoyin bayan jam’iyyar APC a Jihar Bauchi Alhaji Ali Ibrahim dogare Ningi kuma tsohon shugaban karamar hukumar Ningi ya zargi gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar da wasu magoya bayan jam’iyyar APC masu  nuna halin son zuciya da yin zagon kasa don ganin APC ba ta sake samun nasara a yayin zabuka masu zuwa na shekarar 2019 ba.

Ali Dogare Ningi ya bayyana haka ne cikin taron manema labarai da ya qira a Bauchi inda ya ce dukkan ginin da suka jima suna yi don ciyar da jam’iyyar APC gaba wadannan mutane suna yunkurin rusa shi tare kuma da birne hanyar da suka share don ganin shugaban kasa Buhari ya kai ga sake samun nasarar zama shugaban qasa a yayin zabukan gama gari masu zuwa.

Don haka ya ja hankalin masu zagon kasa da cewa sun tona ramin birne jam’iyyar  APC ce saboda kasa gudanar da zaben shugabannin da suka yi don haka ya kamata a gaggauta samar da gyara don tabbatar da ci gaba da riqe matsayin da jam’iyyar APC ke da shi a kasar nan.

Alhaji Aili Ibrahim Dogare Ningi ya bayyana cewa a zaman su na ‘yan APC na gaskiya suna nuna rashin jin dadi game da yadda aka ce an yi zabe a Jihar Bauchi alhali ba haka ba ne ba a yi zabe ba nadi aka yi, an yi rubutune kurum. Ya ce saboda tun farko da suka fahimci za a yi hakan sun kai kuka ga uwar jam’iyya amma suka bijire. Saboda haka ya bayyana cewa sun lura ana son a kashe jam’iyyar ce alhali su ba za su amin ce ba. Saboda kuwa idan aka wayi gari an bayyana tsoffin shugabannin da ba a so a matsayin sabbin shugabanannin jam’iyya haqiqa APC za ta samu matsala yadda mutanen da aka fusata za su koma su zabi wasu shugabanni a wasu jam’iyyun.

Alhaji Ali Ibrahim dogare ya bayyana cewa wadanda ke yin irin wannan kama karya ba masu kaunar shugaban kasa Buhari ba ne mutane ne masu son zuciya don haka idan lamarin ya dore da haka za a wayi gari shi kansa shugaba Buhari ba shi da tabbas na cin zabe saboda ganin irin halin da ake ciki. Don haka ya bayyana cewa alamu na nuna akwai ‘yan PDP da suka shigo suke son yakar jam’iyyar APC ta hanyar nuna irin halayen magudi da a baya suka bi suka kashe jam’iyyar ta PDP har ta kai ga faduwa zabe na shekarar 2015.

Don haka ya ja hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi la’akari da gwamnonin da suke nuna  irin wannan hali suna yi ne don zagon kasa ga Buharin da jam’iyyar don ganin bata sake cin zabe ba.

Saboda haka ya bayyana cewa su ne suka wahala a cikin jam’iyuyar APC kuma suna da yawa wadanda ko da rana guda basu taba fita zuwa cikin wata jam’iyya ba amma yanzu an ci yaki an bar su da kuturun bawa.

Bayan haka kuma ana so tagomashin da jam’iyyar keda shi a lalata shi bayan tsawon lokacin da suka dauka suna gina jam’iyyar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: