Connect with us

KASASHEN WAJE

Mutane Da Yawa Sun Mutu Sakamakon Fadan Gaza

Published

on

 

Jami’an Palasdinu sun ce an jikkata masu zanga-zanga fiye da 2,700 a dauki ba dadin da aka yi bakin iyakar Gaza a rana mafi muni da aka yi tashin hankalin bakin iyaka tun shekarar 2014 da aka yi yadi da Isra’ila.

Dakarun Isra’ila sun sha suka gamedda yin amfani da darfi a kan Palasdinawa a bakin iyakar a lokacin zanga-zangar da aka yi makonni 7 da suka wuce, amma jami’an Isra’ila sun ce matakan da aka dauka suna da muhimmanci wajen kare iyakarsu kuma sun zargi ‘yan bindigar Hamas da fakewa bayan zanga-zanga don tada zaune tsaye.

Wannan fadan ya faru ne a lokacin da jami’an Amurka da Isra’ila suka yi bukin bude sabon ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus. Dakarun Isra’ila kuma sun ce mutane fiye da 40,000 ne suka yi zanga-zangar. Ana sa ran ganin ci gaban wannan tashin hankalin a yau Talata a kan iyakar ta Gaza da Isra’ila.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: