Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

NDLEA TA Tarwatsa Hekta 11,000 Na Gonar Wiwi A Ondo

Published

on

 

 

Kwamandan Hukumar hana amfani da muggan qwayoyi wato sayensu da kuma amfani dasu Mr Monammed Sokoto ya bayyana cewar ta lalata, gonar da aka shuka Tabar Wiwi mai faxin hekta 11,000 a jihar Ondo.

Kwamandan ya bayyana haka ne lokacin da yake yinma ‘yan jarida jawabi a Akure babban birnin jihar, ita rundunar ta jihar, ta yi hakan ne tsakanin shekarun 2015 da kuma 2018.

Ya ci gaba da bayyana cewar idan da ba alalata gonar ba, zata samar da kilo milyan xaya na ita Tabar Wiwi, wanda hakan babban haxari ne ga zaman lafiya na jihar.

Sokoto ya qara da jaddada cewar an kama mutane waxanda basu wuce 80  ba, saboda aikata laifukan da suka shafi ita Hukumar NDLEA, a wannan shekara.

A vhalin da ake ciki yanzu har an kai su kotu suna kuma fuskantar hukunci. Waxanda aka kama mutane 80 suna kotu za kuma a iya xauresu a kurkuku.

‘’A kwai kuma wau gandun daji guda 10  a jihar Ondo in aka shukja ita tabar Wiwi, za kuma  a xauki mataki nan bada daxewa ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: