Connect with us

LABARAI

Tsohon Darakta Da Ma’aji Na Wata Cibiyar Ilimi Sun Gurfana Kan Zargin Cuwa-cuwan Naira Miliyan 208

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rasahawa gami da dukkanin abubuwan da kan karya tattalin arziki, EFCC, ta gurfanar da, Peter Ojedele da Ali Ahmadu, tsohon babban darakta da kuma Ma’aji na cibiyar, ‘National Institute for Educational Planning and Administration (NIEPA),’ a gaban Mai Shari’a Abdul Dogo, na babban Kotun tarayya da ke zama a Akure, ta Jihar Ondo kan tuhumomi tara da suka shafi satar sa hannu da kuma karban kudi ta hanyar karya.

Laifin na su ya saba da sashe na 16 (1) (b) wanda yake da hukunci a sashe na 58 (5) (a) na dokokin Nijeriya.

Su biyun a matsayin  su na Babban darakta da kuma ma’aji na cibiyar ta, ‘National Institute for Educational Planning and Administration (NIEPA),’ ana zargin su da karban kudi sama da Naira milyan 208, daga gwamnatin tarayya a matsayin gudummawa a shekarar 2011 da kuma 2012 wanda kuma ba su shigar da su  cikin asusun gwamnati ba. Ana kuma zargin su da karyan mallakan ofisoshi a kusan dukkanin Jihohin kasarnan, alhalin ba su da ko da guda bayan an bi diddigin adireshin da suka bayar.

Bincike ya tabbatar da takardun da aka rubuta ga cibiyar a shekarar 2011 da 2012 su na kunshe ne da wasu sunaye na ma’aikatan cibiyar na bogi da cibiyar ke biyan su albashi. Hakanan wadanda ake tuhuman sun zurara kudi kan na’urar DBD da suka sayo wa cibiyar.

Bayan an karanta masu tuhumomin na su, sun musanta aikata laifin.

Bayan sun musantan, Lauyan EFCC, Cosmas Igwu, sai ya bukaci da a sanya masu ranar fara shari’ar, ya kuma bukaci kotun da ta ajiye wadanda ake tuhuman a gidan yari. Sai dai, Lauyan wanda ake tuhuman na farko, Abel Kosoko, da kuma Lauyan wanda ake tuhuma na biyu, Olushola Oke, duk sun bukaci kotun da ta amince da su nemi belin wadanda suke karewar da baki. Amma sai Mai Shari’a Dogo, ya ki amincewa da bukatar na su na neman belin da baki, ya kuma yi umurni da a mayar da wadanda ake tuhumar ma’ajiyar ta EFCC, har zuwa lokacin da za a saurari neman belin na su.

An daga sauraran karar zuwa ranar 18 ga watan Mayu 2018, domin ci gaba da sauraron neman belin a ranar 25 da 26 don ci gaban shari’ar.

Daya daga cikin tuhumar da ake masu na cewa, “Kai, Dakta Peter Kolawole Ojedele da Ali Ahmadu, kun yi amfani da matsayin ku na, Babban darakta da kuma Ma’aji, bi-da-bi, na cibiyar, ‘National Institute for Educational Planning and Administration, Ondo, ta Jihar Ondo,’ wani lokaci a shekarar 2012 a Ondo, inda wannan kotun ke iya yin hukunci, da nufin yin yaudara, inda ku ka amshi tsabar Naira milyan 115,380,488,24, daga gwamnatin tarayya bisa karyan za ku biya hakkokin ma’aikata ne na shekarar 2012 tare da kun san karya ku ke yi, da hakan kun aikata laifi da za a iya hukunta ku da sashi na 1 (3) na yaudara da cuwa-cuwa, na dokokin shekarar 2006.”

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: