Wata Coci Ta Raba Kayan Abinci Ga Musulmi Yan Gudun Hijira A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Wata Coci Ta Raba Kayan Abinci Ga Musulmi Yan Gudun Hijira A Kaduna

Published

on


A daida lokacin da ake shirye shiryen fara azumin watan Ramadan wata coci mai suna “Church of Christ Ebangelical and Life Interbention Ministry” dake Sabon Tasha, a jihar Kaduna ta rarraba wa daruruwan musulmi da ‘yan gudun hijira dake garin Kaduna.

Da yake jawabi ga ‘yan jarida bayan rarraba kayan abincin, shugaban cocin, Mista Yohanna Buru, sun rarraba kayan abincin ne ga masu karamin karfi da ‘yan gudun hijira domin su samu issashen abincin da za su yi amfani dasu a lokacin wannan wata na azumi.

Ya kara da cewa, kayan abincin zai yi matukar taimamak musu jin dadin azumi da fuskantar addu’oi a cikin kwanaki 30 na watan Ramadan din.

Mista Buru, ya ce, cocinsa na kan gaba wajen karfafa dangantaka da son juna tsakanin Musulmai da Kiristoci a jihar Kaduna.

“Cocinmu ta samar da buhunhunan kayan abinci domin rarraba wag a musulmi da kuma karfafa musu wajen fuskantar addu’o’i na kwanaki 30, da fatan Allah ya kawo mana karshen kasha kashen da ake yi a fadin arewacin kasar nan”.

“Zubar da jinni da kashea-kashen da ake yi a kullum ya zama babbar barazana ga tsaron kasa da sauran kasashen duniya” inji Faston Mista Buru, ya kuma kara da cewa, cocin ta ceto matasan musulmi da dama daga gidajen yari Kaduna, ya kuma bayyana cewa, raba kayan abincin nada nufin taimaka wa iyalai su fuskanci kwanaki 30 na azumin watan Ramadan cikin jin dadi da walwala.

“Ya kamata mu fahinci cewa, dukkanmu daga iyalai daya muke, Damu da Hauwa’u, muna kuma bauta wa Allah daya ne, dukkanmu mun yi imani da aljanna da wuta mun kuma yi imani da tashi bayan mutuwa ranar tashin kiyama.

“Muna da littafan dake shiryar damu yadda zamu yi kyakyawan dangantaka da junanmu.

“Dole mu taumaka wa ‘yan uwanmu maza da mata da abin da zasu ci a kwanaki 30 din na musamman ganin yadda kayan abinci ke tsada a kasuwannin mu” inji Buru.

Shugaban cocin ya kuma bukaci musulmi dasu lizimc karatun Alku’ani mai tsarki da zuwa wuraren tafsir saboda samun lada da kuma addu’ar Allah Ya kawo mana karshen matsalolin da ake fuskanta a Afrika dama fadin duniya baki daya.

Da yake jawabi, daya daga cikin wadanda suka amfana da kayan abincin, Malam Rilwani Abdullahi, ya bayyana farin cikinsa da kaytan abincin da aka basu, ya kara da cewa, “Kayan abincin zai yi matukar taimaka mana da abin da zamu ciyar da iyalanmu, zamu kuma samu karfin gwiwar tuna wad a Allah madaukakakin Sarki”

Malam Rilwanu, ya kuma bukaci masu hannu da shuni daga cikin musulmi da su tuna masu karamin karfi da marayu da ‘yan gudun hijira a cikin al’umma.

A nasa jawabin a madadin ‘yan gudun hijirar da suka amfana, Maman Aisha Gamboru Ngala, wadda tana cikin ‘yan gudun hijira daga jihar Borno, ta ce, Allah ne kadai zai iya biyan wannan cocin saboda tunawa da ‘yan gudun hijiran da suka yi, ta kuma bukaci malamai suyi amfani

da watan Ramadan wajen yi wa kasar nan addu’a mudamman bangaren arewa maso gabas.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai