Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Yadda Na Biya Fansar Yuro 232,000 Don Evans Ya Sako Ogana’

Published

on

Wani ma’aikacin kamfaninn harhaxa magunguna na Maydom Pharmaceuticals Limited Mr Uchenna Okagwu, ranar Juma’a ne ya shaidawa babbar kotun Ikeja cewar, ya bada kuxin euros 232,000, abinda ya kai Naira milyan 99.76, kuxaxen da yaba babban mai garkuwa da jama’a Chukwudememe Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, domin tabbatar da an sako  ogan shi.

Okagwu ya bayyana cewar ya biya kuxaxen ne gas hi shugaban garkuwa da jama’a, saboda a samu sakin oganshi Mr Donatus  Dunu, wanda shine shugaban kamfanin.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya bayyana rahoton cewar shio dai Evans yana fuskantar, shari’a  ne, tare da Uche Amadi, Ogechi Uchechukwu, Okwuchukwu Nwachukwu, Chilaka Ifeanyi,, da Victor Aduba, ana zarginsu da aikata laifuka.

Okagwu ya shaidawa kotu cewar Evans shi da ‘yan tawagarsa, sun yi barazanar zasu kashe shi, idan yayi wani kuskure lokacin da ya kai kuxaxen.

Ya bayyana cewar ‘’Watannu biyu da suka wuce bayan an kama ogana na samu kira daga xan’uwanshi, cewar Anselem ya kai ma masu kafguwa da jama’a euros 232,000.

‘’Ya bani wayarshi wadda su masu garkuwan zu yi amfani da ita yawar su bayyana mani inda zan je in kai masu kuxi’.

‘’Daga nan kuma sai na yi ta fara samun kira da ita wayar daga wurin su waxanda suka yi garkuwa da mutanen, cewar kada in yarda in yi wani kuskure, saboda idan nayi zasu iya kashe ni.’’

‘’An tambaye ni ida na san hanya zuwa Mile 2 sai nace masu i, na tafi da kuxaxen, cikin mota. Daga can sai aka ce mani na tafi FESTAC daga can kuma na tafi wani wuri da ake kira Okota.’’

‘’An faxa mani in bita wata hanya inda nasamu masu haya da mashin wato Okada, aka ce maiu kuma nayi bayanin duk abinda na gani,, na kuma ce masu naga wata wutar mai qyalli akan pole’’.

‘’Ana cikin hka ne sai aka   mani na tsaya, na fito daga mota da kuxaxen.

‘’Da na fito daga cikin mota, sai aka faxa mani cewar na ajiye kuxin, na yi yadda suka ce, sai aka ce mani nayi sauri na bar wurin bayan da na aje kuxin.

‘’Na duba domin inga ko minene sai na lura ashe mota ce wadda aka ajiye, a farkon hanyar ga kuma hasken wuta.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: