Connect with us

WASANNI

’Yan Wasan Afrika Sun Bani Babban Gudunmawa A Lokacin Da Nake Arsenal

Published

on

 

Mai koyar da yan wasan  Arsenal mai barin gado, Arsene Wenger, ya bayyana yadda yake matukar kaunar ‘yan wasan kwallon kafa da suka fito daga nahiyar Afirka a wani taron manema labarai na karshe da ya yi a matsayinsa na manajan kungiyar.

A kalaman Mr Wenger ya ce ‘yan wasan Afirka sun yi matukar ba shi gudunmawa a yayin da yake jagorantar kungiyar Arsenal kuma bazai taba mantawa dasu ba a rayuwarsa.

“Na yi mu’amala da ‘yan wasan Afirka duk tsawon rayuwata. Na bude makaranta a Afirka da daya daga cikin abokaina. Mutane kamar su Yaya Toure da Kolo Toure da Eboue da Gerbinho, duk daga wajena suka fito daga wannan makarantar,” a cewar Wenger.

Ya kara da cewa: “Ina tare da George Weah tun yana karami da kuma Fofana da Ibory Coast. Ina da Lauren daga Kamaru. A koyaushe a tawagata akwai ‘yan wasan Afirka. Sun bayar da gudunmawarsu matuka.”

A wajen ‘yan wasan Afirka da dama dai musamman wadanda suka yi aiki karkashinsa, matsayin Wenger ya wuce mai koyarwa  kawai.

Dakarunsa daga cikin ‘yan wasan Afirka sun hada da Emmanuel Adebayor na Togo da Emmanuel Eboue daga Ibory Coast, da Gerbinho daga Ibory Coast, da Aled Song daga Kamaru da Lauren Etame Mayer daga Kamaru da sauran su.

Wenger ya jagoranci wasansa na karshe a Arsenal inda suka kara da Huddersfield inda Tawagar tasa ta samu nasara ci 1-0 a wannan wasan kwallon da sabon dan wasan kungiyar Aubameyang ya ciwa kungiyar.

An yi ta nuna masa kauna ta hanyar aika masa da sakonnin taya murna a lokacin da kuma bayan kammala wasan Dukkan magoya bayan Huddersfield da na Arsenal sun yi ta shewa a yayin da ya isa filin wasan.

Kafin a fara wasan, ‘yan wasan kungiyoyin biyu sun yi masa wata tsayuwa ta ban girma a filin wasan.

Ya dauki dan lokaci kadan kafin ya yi jawabin ban kwanansa na karshe ga ‘yan wasan Arsenal din da za su koma gida.

A yayin da ake wasan, dukkan magoya bayan kungiyoyin biyu sun mike tsaye suna shewa don girmama shi a yayin da aka yi minti 22 da fara wasan, wato daidai tsawon shekarun da ya shafe yana jan ragamar kungiyar.

Haka kuma wani karamin jirgi dauke da sakon taya murna ga kocin, ya yi ta shawagi a saman filin wasan kafin a tafi hutun rabin lokaci sannan Wenger ya bayyana wasan a matsayin wani “biki” da kuma “rana ta musamman” a gare shi.

Wenger ya bar Arsenal bayan da ya ja ragamar wasanni 1,235, inda ya samu nasara sau 717 da kuma cin kwallaye 2,298.

Har yanzu dai kungiyar Arsenal ba ta bayyana wanda zai gaje shi ba tukuna sai dai Wenger ya ce zai ci gaba da harkar koyar da kwallo, amma har yanzu bai bayyana inda zai koma ba
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: