2019: Yanda Za Mu Yi Aiki Da Jam’iyyu 68 Wajen Tsara Takardun Zabe – INEC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

2019: Yanda Za Mu Yi Aiki Da Jam’iyyu 68 Wajen Tsara Takardun Zabe – INEC

Published

on


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ce sam yawaitan Jam’iyyun siyasa masu rajista ba wata matsala ce a gare ta ba, ko ga yadda za ta gudanar da zaben a kasarnan.

Daraktan zabe da kula da Jam’iyyu na hukumar, Aminu Idris, ne ya bayar da wannan tabbacin yayin tattaunawa kan “ Karuwar Yawan Jam’iyyu A Nijeriya Da Yadda za a tsara takardun zaben a shekarar 2019” wanda aka yi ranar Talata a Abuja.

Tattaunawar wanda wasu kungiyoyi biyu masu zaman kansu suka shirya, – Centre for Democracy and Debelopment (CDD) da, ‘Open Society Initiatibe for West Africa (OSIWA).

A yanzun haka dai Nijeriya ta na da Jam’iyyun siyasa masu rajista 68 ne.

Mista Idris ya ce, zabukan da hukumar ta shirya a kwanan nan, sun nu na a zahiri cewa hukumar ba ta da wata matsala wajen gudanar da babban zaben.

“Batun yanda za a tsara Jam’iyyun siyasan kan takardun zaben shi ne babban matsalar da hukumar INEC za ta fuskanta.

“A wasu lokutan mukan yi maganin hakan ne ta hanyar saka alamomin Jam’iyyun da suka shiga zaben ne kadai, ta yadda ba za a ruda mai yin zaben ba.

Babban sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi, wanda yana daya daga cikin shugabannin taron, cewa ya yi, a maimakon yawaitan Jam’iyyun ya zama matsala, hakan zai ma sanya ne masu jefa kuri’ar su yi yawa.

Abdullahi ya ce, matsalar ita ne inda hatta jam’iyyun da ba su da karfi za su so shiga kowane zabe har ma da na shugaban kasa.

“A gaskiya, ni ban ga matsalan yawaitan Jam’iyyun ba. kamata dai ya yi Jam’iyyun su yi ma kansu adalci, ta hanyar shiga zaben kawai da suka cancanta.”

A na shi bangaren, mataimakin sakataren Jam’iyyar PDP na kasa, Emmanuel Agbo, ya alakanta yawaitan Jam’iyyun ne da burin da wasu ke da shi na zamowa Shugabannin Jam’iyyu na kasa.

Emmanuel Agbo ya ce, akwai bukatar wayar wa da ‘yan siyasa kai, su san cewa, ba duk sabani ne a tsakanin su zai sanya a kai ga kafa sabuwar Jam’iyya ba.

“Ya kamata mu iya hankurewa juna, mu san cewa mun fito ne daga matakai, fahimta da al’adu daban-daban amma muka narke a cikin kungiya guda.

“Matukar kuwa hakan ne, to zai yi wahala kowa ya sami biyan bukatan sa.”

Shi ma, Shugaban Jam’iyyar PPA, Peter Ameh, cewa ya yi, ba wata matsala da kasantuwar mu da Jam’iyyu masu rajista guda 68, domin ai ko kananan kasashe kamar Senegal, Jam’iyyun ta masu rajista guda 300 ne, hakanan kasar Benin ta na da Jam’iyyu sama da 150.

Mista Ameh ya ce, ya na da mahimmanci a yi maganin matsalolin Jam’iyyun na kasarnan, a maimakon a rika duba alamomin matsalolin kadai.

Matsalolin na su kuwa a cewar shi, sun hada da yawan ficewan da jami’an Jam’iyyun ke yi daga kananan Jam’iyyu zuwa manyan Jam’iyyu, da kuma ayar tambaya kan sahihancin zabukan da hukumomin zabe na Jihohi ke shirya wa a kananan hukumomi.

“Zaben kananan hukumomi da aka taba shiryawa na gaskiya kwara daya ne rak a kasarnan, shi ne kuwa wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta shirya a babban birnin tarayya Abuja. Amma sauran kuwa, sai dai ka ji an ce APC ta cinye kujeru duka a Jihar Kano, ko kuma ka ji an ce Jam’iyyar PDP ta cinye kujeru duk a Jihar Delta.”

Mista Ameh ya ce, matukar kasarnan za ta ci gaba da inganta tsarin zaben ta, shakka babu hakan zai fiye wa al’umman kasar kyawu.

Tun da farko a na ta jawabin, shugabar cibiyar ta, Democracy and Accountability, OSIWA, Catherine Angai, cewa ta yi ana yin rajistan Jam’iyyun siyasa ne bisa dalilai daban-daban, da suka hada da janyo hankulan masu jefa kuri’a da kuma bin diddigin ayyukan gwamnati.

Ta ce, an shirya tattaunawar ce saboda a amsa wasu zaunannun tambayoyi,kamar na, “Shin Jam’iyyun siyasar su na yin abin da aka kafa su domin shi kuwa? Akwai dimokuradiyya a cikin Jam’iyyun kuwa? Ko akwai wata matsala da Jam’iyyun? Ta ce, wadannan da ma wasun su, su na daga cikin abin da ya kamata tattaunawar ta amsa su.

Shugaban cibiyar ta, Partner for Electoral Reform, Mista Ezenwa Nwagwu, ya yaba wa wadanda suka shirya tattaunawar.

Sai dai ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a rika duba rawar da Jam’iyyun ke takawa a wajen zabe, musamman a mataki na tarayya.

“Ga misali, a sanya dokar matukar ba ka iya cin akalla kujeru hudu ba a zaben kananan hukumomi, to kuwa ba ka da ‘yancin shiga zaben matakin tarayya.”

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!