Boko Haram: EFCC Ta Shaida Wa Kotu Yadda Manyan Sojin Sama Suka Karkatar Da Naira Biliyan 22.8 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Boko Haram: EFCC Ta Shaida Wa Kotu Yadda Manyan Sojin Sama Suka Karkatar Da Naira Biliyan 22.8

Published

on


Mai Shari’a Mohammed Idris,na babbar kotun tarayya da ke Legas, a jiya ya jiye ma kunninsa zargin da ake wa wasu manyan jami’an rundunar Sojin sama na karkatar da wasu kudade da aka kebe su domin sayen man jiragen sama da kuma wasu ayyukan na yakar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Wani Jami’in hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Tosin Owobo, ne ya bayyanawa kotun hakan yayin ci gaba da tuhumar da ake yi wa tsohon Kwamandan rundunar ta sama, Adesola Amosu, da wasu mutane biyu, da a yanzun haka suke fuskantar tuhumar yin sama da fadi da Naira bilyan 22.8.

Owobo, wanda shi ma shaida ne a tuhumar da ake yi wa jami’an, ya yi zargin cewa, sun karkatar da kudaden ne daga asusun Ma’aikatar tsaro zuwa asusun rundunar sojin saman, ta hanyoyi da dama da suka hada da ta, “Operation Lafia Dole.”

A ranar 29 ga watan Yuni ne hukumar ta EFCC ta gurfanar da Amosun tare da wasu manyan jami’an rundunar ta Sojin sama, Aeya Bays Mashal Jacob Bola Adigun, da Aeya Kwamando Gbadebo Owodunni Olugbenga, da kuma wasu kamfanoni bakwai a gaban Mai Shari’a Mohammed Idris.

Kamfanukan da aka ambata a cikin tuhuman sun hada da, Delfina Oil and Gas Ltd, Mcallan Oil And Gas Ltd, Hebron Housing and Properties Company Ltd, Trapezites BDC, Fonds and Pricey Ltd, Deegee Oil and Gas Ltd, Timsegg Inbestment Ltd da Solomon Health Care Ltd.

Hukumar ta EFCC, tana zargin su ne da hada baki, sata, cuwa-cuwan kudi, boye laifi da kuma karkatar da dukiyar da take mallakin rundunar Sojin sama na kasa ne zuwa amfanin kansu a tsakanin watan ranar 5 ga Maris 2014, a Legas.

Sai dai duk sun musanta aikata laifin.

Owobo, da yake amsa tambayar Lauyan na Amosun, Cif Bolaji Ayorinde (SAN), ya bayyana cewa, dukkanin jami’an hukumar ta rundunar Sojin saman da suka bincika kan lamarin sun tabbatar da cewa an kawo kudaden ne domin gudanar da ayyukan rundunar, amma kuma sai aka raba su kamar yadda Amosun  ya yi umurni.

Shaidar ya rantse da cewa, jami’an hukumar masu bincike guda takwas ne suka gabatar da binciken, sannan kuma hukumar ta EFCC ba ta kai samame ba, ta dai je bincike ne kadai.

Ya kuma ce, an kawo Naira bilyan guda a ranar 17 ga watan Janairu 2013, Naira milyan 100 a ranar 15 ga watan Mayu 2013, Naira milyan 18.6 a ranar 12 ga watan Yuni duk daga shalkwatar ma’aikatar tsaro.

Da lauyan na Amosun ya tambaye shi, “A lokacin da kake gabatar da binciken na ka, ko ka gano dalilin da ya sanya aka karbo wadannan kudaden?”

Sai ya bayar da amsa da cewa, “Bayan mun fara binciken namu, jami’an na rundunar Sojin ta sama da muka tattauna da su sun shaida mana kudaden duk na gudanar da ayyuka ne.”

Lauyan na Amosun ya sake tambayar jami’in na EFCC, “Ko ka tambayi ma’aikatar tsaron ko dalilin me ya sanya aka biya ma’aikatar Naira bilyan guda?” Jami’in ya amsa da cewa, “Ba zan iya tunawa ba.”

To ko ka san Naira milyan 18.6 na mene ne, Owobo ya ce, “Ban tambaya ba.”

Owobo ya ce, tsohon Kwamandan na rundunar Sojin ta sama,Aled Badeh, yana daga cikin wadanda suka bincika lokacin binciken na su, ya kuma bayar da wasu bayanai.

Ayorinde sai ya bukaci da a ba shi bayanin na Aled Badeh yana bukatar sa domin kare wanda ake tuhuman.

Amma sai Lauyan da ke gabatar da karan, Rotimi Oyedepo, ya bukaci da a dakatar da shari’ar na tsawon mintuna 20 domin ya binciko bayanan Aled Badeh din. Ya soki bukatar da Ayorinde ya gabatar na neman a dage sauraron shari’ar, yana mai cewa hakan zai kara tsawaita shari’ar ne kawai.

Amma sai dukkanin Lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuman suka ki bukatar ta a dan dakatar zaman, suka ce ya fi kamata a dage zaman ne kawai.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Idris, cewa ya yi, sashe na 36 na tsarin mulki ya bayar da daman sauraron kowa, wanda hakan ke nu ni da cewa, tilas ne amutunta bukatan masu zargin juna a kotu.

“A duk lokacin da wanda ke kare mai laifi ya bukaci da a ba shi wasu takardu da suka shafi wanda yake karewa domin ya duba da kyau ya san yadda zai kare wanda ake tuhuma, ya zama tilas da a ba shi, bayan ya biya dukkanin kudaden da aka bukace shi kan hakan.

“Domin kwatanta gaskiya, ina ganin ya fi kyau ne a dage zaman bisa yadda doka ta tanada. Na san cewa a duk lokacin da aka jinkirta shari’a ana kokarin kaucewa gaskiya ne, amma gaggawan yanke hukunci kuma rushe gaskiya ne. Don haka za mu dage saboda neman gaskiya.”

Daga nan sai Mai Shari’a Idris ya dage zaman har zuwa ranar 15 ga watan Mayu don ci gaba da sauraron shari’ar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai