Connect with us

KIWON LAFIYA

Dalilan Dake Janyo Wa Maza Su Gaza Yi Wa Matansu Juna Biyu

Published

on

Sabon binciken da aka gudanar akan daukar ciki a tsakanin ma’aura ta, ga dukkan alamu, ya kawo masu sauki.

A baya, ana dora laifin daukar ciki akan matan aure da kuma chamfi kashe ‘yan biyu a cikin wasu alumomin.

A bincikin da masana harkar kiwon lafiya suka gudanar ya nuna cewar, bayanan da suka samo akan maza ma’aurata da aka yi masu gwajin akan rashin yiwa matan su ciki a shekaru goma yawan mazan ya karu.

Wata barazana da masanan suka gano itace, karanci da kyaun maniyin da maza ma’aurata suke fitar wa a yayin saduwa da iyalan su ya ragu.

Binciken ya kuma gano cewar, a bisa kididdiga kashi hamsin bisa dari na kalubalen rashin haihuwa da ma’aurata ke fuskanta ana danganta hakan akan rashin samun juna biyu kuma ya fi karuwa akan maza saboda manyantar da suka yi.

Da yake yin bayani akan dalilan, Dakta Ada Okoro, na asibitin kwararru dake jihar Legas ya ce,“gaskiya ne matasa a yanzu basa iya fitar da lafiyayyen maniyi da zai iya sanyawa matan su su zauki juna biyu saboda yawan kwankwadar barasa da kwaya da kuma shan sigari.”

Da take magana akan nata darasin akan wani majinya ci, Dakta Okoro ta ce, “akwai wani majinya ci na da aka gaya masa cewar yana fuskantar matsalar rashin haihuwa, yaki yarda da hakan.”

Ta ce, “mun baiwa sakamakon wani majinya ci, kuma mun dauki dogon lokaci muna yi masa bayani, amma yaki yarda.”

Daktan ta kara da cewa,” majinya cin ya ce ya fi son yaje wani wurin don a sake yi masa gwaji, amma daga baya ya sake shawara ya dawo gun mu don a yi masa magani.”

Har ila yau, wani jami’in kiwon lafiya dake jihar Legas Dakta Uche Okenyi ya jadda da maganar Dakta Okoro, inda ya danganta hakan akan sabon canjin rayuwa da wasu mazan suka runguma, inda hakan ya sanya basa iya fitar da maniyi mai kyau.

Ya ce,“koda yake bamu san abinda ke janyo karuwar rashin daukar juna biyun a tsakanin maza ba, amma ina ganin saboda rungumar sabuwar rayuwa ne da suka yi.”

Ya sanar da cewar, idan muna hudda da maza masu fuskantar matsalar kasa yiwa matan su ciki, mukan basu kwarin gwaiwa akan yi masu gwaji da yi masu magani.”

Okenyi ya yi nuni da cewa, ga maza da dama ana auna maniyin su yadda yake fita.

Shima wani kwararren likita dake asibitin kwararru na jihar Legas Dakta Emeka Amadi ya yi nuni da cewar, matsalar tafi kamari a tsakanin  mutane masu shekaru sama da arba’in.

Amadi ya tabbatar da cewar, adadin yawan maniyin dake fita ya ragu, inda hakan yake nuna kasa da kashi 1.4 dake raguwa a duk shekara.

Bugu da kari, a wani bincike na hadaka da sashen kiwon lafiya da gidauniyar yawan al’umma na majalisar dinkin duniya (UNPF) suka dauki nauyi, sun gano cewar, rungumar sabuwar rayuwa yana janyo wa miji ragewar fitar maniyi saboda karanci yadda ya kamata ya fita.

Binciken ya kuma nuna cewar, a Afrika, matsalar ta kai kashi hamsin da bakwai cikin dari a sama da shekaru talatin da biyar da suka shige.

Dakta Amadi a ra’ayin sa ya ce, wasu mazan auren basa son su nemi magani amma suna ci gaba da boye kansu, wasu kuma a shirye suke suje a gwada su wasu kuma ba sa son zuwa saboda suna ganin abin kunya ne ko kuma wasu dalilan na kashin kansu.”

A wani sharhi da aka wallafa a wata mujjalar kasar nan ta kiwon lafiya a bisa wani bincike da aka gudanar akan kawun da miniyin ma’ura yake dashi, garin Ile-Ife, maza masu shekaru talatin da daya zuwa arba’in an gano sunfi fama da matsalar.

Makamancin wannan rahoton, an walla wani sharhin a cikin wata mujallar yanar gizo mai duba larurar mata mai take “yawan karuwar matsalar a tsakinin maza ma’aurata a yankin kudu maso Yamma”,inda a bisa wannan binciken, an anyi gwaji akan ma’aura ta 314 dake fuskantar matsalar a wani asibiti dake Nnewi a cikin jihar Awka, inda binciken ya nuna cewar, ma’aura ta 204 suna fuskantar karamar matsala 110 kuma, suna fuskantar babbar matsalar.

Mutane da dama da wuya suka damu da wannan matsalar saboda suna ganin tunda su maza ne sam basu da wannan matsalar.

Karamin dalili shi ne chamfi cewar mazan aure basu ne keda matsalar ba.

Acewar wani Williams da taba fuskantar matsalar aka kuma yi masa aiki a asibiti ya ce,” mun shafe shekaru biyar bamu samu karuwa ba amma ina yiwa Allah godiya da a yanzu ya arzurta ni da da namiji.”

Williams ya ci gaba da cewa,” a bisa magana ta gaskiya, na danyi jinkiri inje asibiti saboda ina ganin bani da wata matsala, daga baya na yanke shawarar inje asibitin, inda na gano cewar nine keda matsalar bayan da likita ya sheda mini ina da karancin maniyi sai naji kamar

rayuwa ta shi kenen kuma.”

Sai dai, silar dake kawo maza matsalar, ba’a iya tabbatar da ita ba saboda kimanin maza kashi hamsin cikin dari da aka yi masu gwajin matsalar, ba’a iya tabbatar da hakikanin abinda ke haddasa ta ba.

Mafi yawancin matsalar a tsakanin maza itace yawan maniyin ko kuma kyawun sa.

Wasu daga cikin abinda ke janyo matsalar da akafi sani sun hadada jin ciwo maraina da mutumum wanda aka taba yi masa wani aiki na da ban da kamuwa da kwayoyin cuta yin aiki a kusa da sanadaran guba ko dumamar yanayin sandar (mast) ta kamfanonin sadarwa, wanda akafi sani yana janyo cutar Kansa ga wadanda suka tsallake.

Akwai kuma rungumar sabuwar rayuwa, wadda zata iya haifarwa da maza matsalar kamar sanya dan kamfai matsatse da shan sigari da barasa da sauran kayan maye.

Duk da cewar, a wannan sashen kasar matar aure ita aka fi dorawa laifi akan matsalar ya kamata a sabon binciken da za’a gudanar, a wayarwa da al’umma kai akan wannan imanin.

Masana sun bayar da shawarar cewar, afi mayar da hankali akan maza ma’aura ta in har ana fuskantar matsalar.

Akwai kuma bukatar a wayar wa da maza ma’aura ta kai dasu amince sune ke da matsalar, musamman don a rage kyamar da ake nunawa mata.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: