Farashin Mai Da Disil Ya Sauka A Watan Afirilun 2018 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Farashin Mai Da Disil Ya Sauka A Watan Afirilun 2018

Published

on


Hukumar kididdiga ta kasa, (NBS) ta sanar da cewar, dan karamin farashin mai a lita daya da masu saye suke biya ya ragu da kashi 7.3 bisa ddari zuwa naira 151.4 a cikin watan Afirilun  2018 daga naira 163.4 da aka samu a cikin watan Maris 2018.

Dan karamin farashin mai ya karu da kashi daya idan aka kwatan ta da dan karamin farashi na naira 149.9 da aka samu a cikin watan Afirilun 2017.

Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin wannan rahoton da aka yi masa lakabi da farashin mai na (PMS) da aka kungiyar dake sanya ido akan farashin ta wallafa shi a kafar ta ta yanar gizo ranar Litinin data gabata.

Bugu da kari, rahoton mai taken  Gas da mai wanda kungiyar ta sanya ido akan farashin mai ta wallafa a kafar yanar gizon ta an buga shi ne a ranar Litinin data wuce, inda hukumar ta kididdiga ta kasa ta ce, dan farashin na lita daya da masu amfani da disil suke saye, ya ragu da kashi 10.86 bisa dari akan naira 204.35 a cikin watan Afirilun 2018 daga dan farashi na naira 229.25 da aka samu a cikin watan Afirilun 2017.

Farashin disil ya sauka da kashi daya bisa dari, idan aka kwatan ta da farashin naira 206.41 da aka samu a cikin watan Maris din 2018.

Ba kamar farashin mai da disil ba wadanda suka ragu idan aka kwatanta da a cikin watan Maris din 2018, inda dan farashin kalanzir ya karu da kashi  3.53 bisa dari a cikin watan Afirilun 2018 akan naira 278.49.

Idan aka kwatan ta da dan farashin naira 280.8 da aka samu a watan Afirilun 2017, farashin da aka biya na kalanzir, ya ragu da kashi 0.83 bisa dari.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!