Ganduje Ya Sasanta Rikicin Majalisar Dokokin Jihar Kano — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ganduje Ya Sasanta Rikicin Majalisar Dokokin Jihar Kano

Published

on


Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu nasarar sassanta bangarorin dake rikici da juna a majalisar dokokin jihar.

A Sanarwa da kwamishinan watsa labarai, Mohammed Garba, ya raba wa manema labarai a Kano, ya ce, an samu wannan nasarar ne a wani taro da aka gudanar da wakilan bangarorin biyu da basa ga maciji da juna a gidan gwamnati cikin daren Talata.

Ya ce, Gwamna Ganduje ya shiga tsananin ne saboda a samar da zaman lafiya da ci gaban jihar, saboda haka za a bude zauren majalisar ranar Alhamis inda za a ci gaba da tattaunawa domin kara fahintar juna.

Sanarwar ta ce, ‘Mai girma gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta rikicin dake tsakanin bangare biyu na majalisar dokokin jihar.

“Wannan sasantawar ya kawo karshen rikincin da aka yi fama dashi, saboda a na saran bude zuren majalisar ranar Alhamis in za a ci gaba da tataunawa domin samar da fahintar juna.

“Taron samar da sulhun ya kankama ne da tsakar daren jiya a gidan gwamnati tare da wakilan bangarorin da basa ga maciji da juna da gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda ya shiga tsakani domin samar da zaman lafiya da ci gaban harkar dimokradiyya a jihar”.

“An gudanar da taron cikin mutunci da sanin ya kamata” inji Garba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!