Matsalar Da Ta Dakile Kubutar Leah Sharibu –Gwamnatin Tarayya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Matsalar Da Ta Dakile Kubutar Leah Sharibu –Gwamnatin Tarayya

Published

on


Gwamnatin tarayya ta bayana cewa, ana fuskantar matsala a kokarin kubutar da Leah Sharibu ‘yar makarantar Dapchi da ‘yan Boko haram suka sace kwanakin baya ne, saboda sarkakiyar dake tattare da tattaunawar da ake yi da kungiyar ‘yan ta’addan.

Ministan watsa labarai da al’adu, Mista Lai Mohammed, ya tabbatar wa da ‘yan jarida haka bayan kammala taron majalisar kasa a fadar shugaban kasa Abuja.

Idan za a iya tunawa, Leah Sharibu, na daya daga ciki ‘yan makarantar “Gobernment Girls Science Secondary School” dake garin Dapchi ta jihar Yobe da aka sace a ranar 19 ga watan Fabrairu 2018.

Yayin da aka samu kubutar da ‘yan mata 105 a watan Maris, yanzu gashi ana wata na daya amma bata samu ‘yancinta ba, tana nan a hannu ‘yan ta’ddan saboda taki barin addininta na Kirista zuwa addinin Musulumci. A ranar Litinin ne ta cika shekara 15 da haihuwa.

Ministan ya kuma kara da cewa, duk da sarkakiyar da ake fuskanta muna da yakinin ceto ta. Ya kara da cewa, “Ina tsammanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya warware maganan a jawabin da ya yi a kasar Amurka, nima matsaya ta daya take dana shugaban kasa, har yanzu bamu warware maganan daya shafi ‘yan mata 6 ba, an sace ‘yan mata 111 mun kubutar da 105 kuma har yanzu muna bibiyar abin daya faru 5 daga cikinsu kuma a kullum muna ta tatauna da ‘yan ta’addan a kan yadda za a kubutar da daya yarinyar mai suna Leah Sharibu.

“A na nan ana tattaunawa da ‘yan ta’addan, lamarin yana da tsananin sarkakiya amma ina mai tabbatar muku da cewa, ba zamu cire rai ba muna aiki dare da rana na ganin an kubutar da ita”.

“Duk wani daya taba tataunawa da ‘yan ta’adda a duniya, dole ya san cewa, ba kai tsaye ake tattaunawar da ‘yan ta’addan  ba” inji shi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai