Mu Muke Nishadantar Da Taron PDP Amma An Bar Mu A Baya -NTA Talba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Mu Muke Nishadantar Da Taron PDP Amma An Bar Mu A Baya -NTA Talba

Published

on


Wasu masu shigar barkwanci na kayan PDP suna rike Kamar talabijin na kwali suna nishadantar da jama’a a tarurruan jam’iyyar PDP a jihar Gombe da ake kiransu NTA Talba, sun koka kan yadda aka bar su a baya.

Sani Sule dan unguwar hayin kwarin Misau din BCJ a fadar jihar Gombe da ya yi magana a madadin su ya ce gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo sun sani tana ayyukan ci gaba na raya kasa da ciyar da matasa gaba amma duk da haka wadanda suka sha wahala ya kamata gwamnati ta duba su tana kula da su domin su suka fi sha mata wahala.

Sani Sule,ya ce su da suke nishadantar da tarurrukan PDP basu gane bakin zaren gwamnatin ba har yanzu kuma kayayyakin aikin su ma da wanda suke sawa sun lalace suna neman a tallafa musu domin su nemi wasu dan su san cewa ba’a manta da su ba.

Ya ce rashin kulawa da ake yiwa wadanda suka wahala a jam’iyyar ta PDP yasa yanzu haka jam’iyyar APC ta fara kwashe musu matasa ganin siyasa ta fara karatowa dan haka suke kiran gwamna Dankwambo da kar ya yi sake a kashe jam’iyyar a jihar idan ya tafi a rasa mai rike ta.

Sani Sule, ya kuma ce tunda yanzu ta ko’ina an fara buga gangar siyasa ya kamata irin tallafin nan da uwargidan gwamna Hajiya Adama Ummu uwar marayu take yi na koyawa mata sana’oi a basu jari ta dawo da shi dan yana taimakawa al’umma matuka musamman ma a irin wannan lokacin zai fi taimakawa saboda halin da ake ciki na rayuwa.

Ya kuma ce kula da jama’a da talalfin da ake samu shi ne yake ciyar da jam’iyya gaba amma fa gwamna ya sani a kewaye dashi akwai marasa tausayi da basa son suga yana taimakawa jama’a su ne suke jawo masa bakin jini a gari domin ba masu kaunar sa bane.

Har ila yau ya kara da cewa tunda shi gwamna ya gama wa’adin sa a karo na biyu a shekarar 2019 ya daure ya dauko wanda zai karbu a wajen jama’a ya tsayar da shi dan idan yaci zabe ya dora daga inda ya bari kar ya kawo wanda jama’a basa so.

Daga nan sai Sani ya ce yana mai kira da babbar murya ga gwamna Dankwambo da yaji kukan su ya taimaka musu saboda rashin wannan taimako yana mayar musu da ayyukan da suke yi baya dama kuma gashi ba biyan su ake yi ba kuma idan har ba’a taimake su yanzu ba har gwamnati ta kare jama’a za su yi musu dariya ya kamata kafin ya sauka suma su gane cewa sun yiwa PDP wahala amma wahalar tasu ya zama basu yi ta a banza ba.

Sannan sai ya sake yin rook da cewa an sha musu alkawarin kujerar Makka amma ba ta iso su dan haka gwamna ya sani, haka suma yan takarkarun nan ya yi kira garesu da cewa duk wanda yaci zabe ya rike su da amana saboda da su aka fara jam’iyyar PDP sune kuma NTA Talba amma har yanzu ba su gani a kasa ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!