Osinbajo Ya Ziyarci ’Yan Gudun Hijira A Binuwai — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Osinbajo Ya Ziyarci ’Yan Gudun Hijira A Binuwai

Published

on


Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya karyata zargin da ake yin a cewa, kashe-kashen dake gudana a jihar wani shiryayyen lamari ne na kawar da mutane.

Farfesa Osinbajo, wanda ke ziyarar aiki da kwanaki biyu a jihar, ya yi wannan bayanin ne a taron masu ruwa da tsaki da aka yi a fadar gwamnatin jihar dake Makurdi.

Ya ce. Gwamnatin tarayya a shirye take ta sake gina dukkan barnar da aka yi a sassan jihar dama sauran jihohi don ta karyata wannan rade radin da ake yi.

Ya kara da cewa, fushi da damuwar da aka nuna a taron abu ne mai mahimmanci, amma ya kuma tabbatar da cewa, a shirye gwamnati take ta samar da cikakken tsaro ga dukkan ‘yan kaasa, an kuma samar da shirye shirye da dama domin saukaka wa jama’a fuskantar rayuwa.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma tabbata da cewa, gwamnati zata nemo musabbabin rikicin domin samar da hanyoyin magance faruwarsa nan gaba.

Ya kuma karyata kokarin dangata kashe-kashen da akeyi da addini, yana mai cewa, an san Kiristoci da kokarin wanzan da zaman lafiya a ko wanne hali, saboda haka ya kamata Kiristoci su yi tattalin zaman lafiya a kowanne lokaci.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma ce, daukar jami’ai da ake yi a hukumomin tsaro na kasar nada nufin samar da isassasun dakarun da zasu fuskanci aikin tsaron kasa da mutanendake cikinta gaba daya, musamman bangaren da aka fi samun tashe tashen hankulla.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga cocin Katolika na Saint Ignatius Parish Mbalom inda aka kai musu mummunan hari, harin da ya yi sadaniyar mutuwar mutum fiye 18 ciki har da limaman cocin guda 2, ana kuma zargin Fukani makiyaya ne suka kai harin.

A nasa jawabin tun da farko, gwamnan jihar Biniwai Mista Samuel Ortom, ya bukaci gwamnatin tarayya ta gagauta zakulo wadanda suka kashe limaman cocin nan guda 2 da sauran jama’ar da aka kashe ba tare da wani dalili ba.

Ya kuma memi taimakon gwamnatin tarayya don fuskantar dimbin ‘yan gudun hijira dake zaune a sansanonin dake bukatar gyara sosai.

A nashi jawabin a taron, Lawrence Onoja, ya bukaci a gaggauta kafa ma’aikatar  kula da yankin mai suna “Middle Belt Reconstruction Commission” domin fuskantar matsalolin da ake fuskanta a yankin musamman a bangaren aiki gona.

Mista Onoja, wanda tsohon hafsan soja ne, ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta cafke Fulani makiyayan da suka aiwatar da kashe kashen dake gudana a yankin Biniwai a kuma samar da karin matakan tsaro da kariya ga manoma domin su samu komawa gonakinsu.

Shi kuwa shugaban cocin Katolika na yankin Gboko, Mista Williams Abenya, ya yi takaicin harin da aka kawo kwana kwanan nan, ya kuma bukaci a samar da labi da burtaloin kiwo a yankin gangaren Biniwai domin kaucewa asarar rayukan jama’a.

A nasa jawabin, shugaban majalisar dokokin jihar Binuwai Mista Terkimbi Ikyange, ya bukaci gwamnati ta kafa dokar haramta kiwo a sarari, don ta haka ne za a kawo karshen rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma a dukkan fadin kasar nan.

Wani tsohon shugaban jami’ar ABU, Farfesa Daniel Saror, ya roki gwamnatin tarayya ne data haramta kiwo gaba daya, domin kuwa ya zuwa yanzu makiyaya sun kwace musu filayen gonad a gidajensu..

Shi kuwa Mista Magdalyne Dura, wani malamin  jami’a, ya yi bayanin cewa, Naira Biliyan 10 da aka ware domin sake gida garuruwan da suka lallace sun yi matukar kadan musamman in aka lura da girman barnar da Fulani makiyaya suka yi a yankin na Binuwai.

Saura wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da tsohon Ministan shari’a Mike Aondoakaa da Janar Atom Kpera da Farfesa Tony Ijohor da kuma Farfesa Jerry Agada, dukkansu kuma sun nemi a haranta kiwo a cikin al’umma.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!