Sai Gwamnati Ta Mutunta Dokokin Hanya Kafin A Samu Saukin Lalacewar Hanyoyi –Taufik — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sai Gwamnati Ta Mutunta Dokokin Hanya Kafin A Samu Saukin Lalacewar Hanyoyi –Taufik

Published

on


An yi kira ga gwamnatin jihar Neja da sake duba akan kwangilolin aikin hanyoyi da aka bayar kafin zuwanta, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lapai, Alhaji Ibrahim Taufik ne ya yi kiran ganin yadda aikin hanyoyin da aka bada kwangilolinsu tun kafin hawar wannan gwamnati ke gudana. Shugaban ya ce kusan duk hanyoyin da suka lalace an bada ayyukan su wanda ko dai an kammala sun sake komawa ‘’yar gidan jiya tun ba a dauki lokaci ba ko kuma ma har yanzu ba a kammala aikinsu ba kuma sun zamowa mutane damuwa.
Ibrahim ya ce misali aikin hanyar Dangana da ya kusa durkusar da harkokin matafiya da masu fatanci tun kafin gwamnatin Abubakar Sani Bello ta zo kan karagar mulki aka bada ta amma har yanzu an kasa kammala ta, mafi yawan ayyukan sun tsaya ne akan gadoji saboda yawaitan fadamu a yankin wanda kusan su ne jigon lalacewar hanyoyin.
Ya ce duk da cewar manyan motocin dakon kaya sun taimaka wajen lalacewar hanyoyin kasar nan saboda irin kayan da suke daukowa ya wuce lissafi, hakan kuma na da nasaba da rashin bin dokokin hanya na daukar kaya wanda duk nahiyyar Afrika suna da irin wadannan dokokin, ya zama wajibi a dawo a mutunta wadannan dokokin duk motar da aka samu da ta ka dokar a tabbatar an hukunta ta, ta hanyar rage adadin kayan da aka amince a dauka, in ba haka babu ranar da hanyoyin kasar nan zasu samu ingancin da zai sa su yi karko.
Ibrahim ya ce hanyar Dangana a duk shekara sai ta fuskaci irin wannan kalubalen, domin tun farko ba a yi ta dan motocin dakon kaya ba, amma kasancewar ta zama hanya mafi sauki ga wanda ya fito shiyyar Bida in yana bukatar zuwa kudancin kasar nan yasa har wadanda ke tasowa daga yankin Sokoto da Kebbi in suna bukatar zuwa kudu musamman idan ta Lokoja zasu bi tafi sauki gare su domin ba ta da kwaramniya kuma tafi kusa. Kan haka manyan motocin dakon kaya sun zama barazana gare ta.
Mu al’ummar wannan yankin muna naman gwamnatin jiha da ta samu mana maslaha domin ita kadai muke da ita wadda ke Sanda mu da kauyukan mu, kasancewar mafi rinjayen jama’armu manoma ne matsalolin da hanyar nan ke samu yakan shafi harkokin mu na yau da kullun.
Yanzu haka a duk lokacin da damana ta kan kama mun shiga fargaba musamman na tsoron samun matsalar hanya tunda ita kadai muka dogara akan ta na tafiya gonakin mu. Ya kamata gwamnati ta samar da dokokin da zai hanawa manyan motocin kaya daukar kayan da suka wuce kima, domin dune barazana ga hanyoyin kasar nan, motocin nan ba wasu kudaden shiga suke samar wa kasar nan ba illa hasarar da suke jawo kasar ta fuskar lalata hanyoyin kasar wanda a wani lokaci kan zamo barazana da rasa rayukan jama’a.
Muna kira ga maigirma gwamna da ya dube mu ya taimaka a sake duba aikin hanyar nan, duk shekara da zaran ruwan sama ya sauka sai ta samu matsala, shekara bara inda ta karye daban ne, shekaru kusan uku ke nan muke fuskantar wannan matsalar idon haka ya cigaba jama’ar mu ba zasu samu damar mai da hankali akan aikin gona yadda ya kamata ba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!