Connect with us

ADABI

Shata Ya Tafi, Shata Ya Dawo

Published

on

07030797630 imel: ibrahim@fudutsima.edu.ng

Bayan shekaru kusan 18 da doriya da gushewar Dr. Mamman Shata (rasuwar sa ranar 18/6/1999) kusan a yau mutum 2 daga cikin ‘ya’yansa ke yin waka. Alhaji Lawal Mamman Shata da aka fi sani da Magaji ya fara waka tun cikin shekarun 1970 lokacin ya na firamare. Ya fara wakar da shi da Umbaje dan Yalwa kanwar Shata da ya ke shi ma lokacin Shatan na rikon sa. Da farko dai Shatan ba ya son wakar ko alama, don haka idan ya na a gida aka zo a aka ce masa ‘ga Magaji can ya na waka a bakin kantuna’ sai ya ruga y koro su gida ya na ma mai dukan su. Amma dai fara waka sosai-sosai Magaji ya soma waka cikin 1983 lokacin ya shekara 2 da kammala karatun Sakandare. Ya kuma shiga kusan ko’ina a cikin kasar nan da sunan waka. Ya yi tafiye-tafiye, ya sadu da mutanen Shata iri-iri.

Da farko, an haifi Magaji Lawal Shata a ran 23/9/1960. Sunan mahaifiyar sa Hajiya Zuwaira ko Asabe. Ita, asalin ta mutumniyar Nahuce ce ta kasar Kano. Ta biyo kanwar mahaifiyar ta Funtuwa ne da ta ke aure, mafarin zaman ta a nan kenan. To rannan da safe ta na tallar goro sai ta biyo layin Ta-Korau mai tuwo inda Shata ke da gida. Ta tarar da shi a kofar gida zaune ya na yin karta shi da wani marokin sa da ake ce ma Tankon Usaina. Sai ya kira ta ya sayi goro, daga nan ya fara nuna ya na son ta, har maganar aure ta kullu a tsakanin su. Ya aure ta cikin Disambar 1959, jim kadan ma bayan barowar sa Musawa da kuma tarewar sa Funtuwar.

Ban da Lawal Magaji, a dakin Hajiya Zuwaira akwai sauran ‘ya’ya kamar Ibrahim (Babangida, ya rasu cikin 1994) sai kuma Rahmatu (Uwaliya) da A’isha (Hajjajo, ita kuma ta auri Shehu Ajilo Danguzuri, kuma ta rasu kwanaki 19 kafin rasuwar Shatan)

Magaji ya halarci makarantar Firamare ta Aya da ke Funtua daga 1967 zuwa 1974. Kusan ma salar sa ne Shata ya san, kuma ya yi tarayya da Alhaji Ado Kankiya, lokacin ya na koyarwa a makarantar.  Daga nan ya wuce Sakandaren gwamnati ta Kafanchan, inda ya shekara 2. Sai aka yi masa canji zuwa Sakadaren gwamnati ta Malumfashi inda ya kammala cikin 1981.

Lawal fasihi ne kwarai da gaske. Babu irin wakar da za ta gagari Magaji ko wacce iri ce, duk da cewa baban sa Shata ya na yi masa tarnaki a lokuta daban daban. Akwai ma lokacin da Shatan na kwance a gida wajen karfe 12 na dare ya ji kalangunan san a tashi a Bikitiri otel a nan Funtuwa. Daga nan dakin sa ya tabbatar kalangunan sa ne. Ya kasa daurewa har ya zabura ya dauko mota ya nufo otel din. Ya tsaya a waje ya na daga cikin mota ya na jin wakar, sai ya gane ashe Magaji ne ke wasa kuma tare da wasu makadan Shata, su Bala Dan Sani. Sai, don ya nuna masu ya gan su ya shiga da kan sa har ya yi ma Magaji din likon kudi. Ya na fitowa taron wakar ya watse. Wakar Shata da Magaji ba za ya iya kwaikwayo ba sai dai wadda bai taba ji ba.

Hatta irin tsoffin wakokin nan na Hakananne Mamman Kanen Idi Wan Yalwa masu nauyi da wuyar kwaikwayo Magaji na iya juye su

Akwai kuma daruruwan wakokin sa na kashin kan sa kusan a gidajen rediyoyi na Kasar nan. Ya kan kuma tafi Sakkwato da Yola don yin wasanni. Amma inda ya fi bada karfi shi ne Kano, inda ma ya ke da zama. Magaji ya cinye taron fadar Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo na 2003 lokacin da Najeriya ta amshi bakuncin dan Sarauniyar Ingila wanda ya kawo ziyara.

Yanzu kuma daga bayan nan sai ga dan autan Shata da ake kira Sanusi Shata shima ya yunkuro don kada gadon gidan su ya bace a cikin tarihi.   Shi dai Sanusi an haife shi a cikin 1984. Sunan mahaifiyar sa Hajiya Dije, kuma ita jikar Sarkin Fulanin Falgore Bello ce wanda amini ne ga Shata don tun cikin 1944 zuwa 1954 Shatan ke ta karakainar zuwa Falgoren wajen sa lokacin ya na zaune a Bakori. Idan ya je, ya gama zaman sa na kwanakin da za ya yi sai Dagaci Bello ya bada aron doki Shata ya hau a tsallakar da shi bakin iyakar kasar sa zuwa Sundu ko Dutsen Kura sannan ya ba da dokin a maido masa. Lokacin da ake tafiya a kasa kena kenan. Da Malam Bello ya rasu sai tarayyar sa da Shata ta koma bias kan dan sa kuma sabon Dagacin Falgore watau Alhaji Sani Bello. To shi Sani shi ne mahaifin ita Hajiya Dije. An bada ta aure ga Shata ran 24/5/1975 a lokacin da aka kira shi daurin auren. Bai ma san cewa da shi aka daura ba.  Alhaji Sani ya yanke wannan shawara ne don ba ya son zumuncin gidan su da Shata ya yanke. Don a Duniya ya dauki Shata muhimmin mutum kuma karimi, wanda duk wata sabga ta arziki a yi ta da shi. Ya nuna cewa Shat aba ya da raina mutane kuma mutum ne amintacce, nagartacce. Shata ya nuna masu shi da ne kuma ya maida ragon suna. Ban da Sanusi, akwai Muntari a dakin Hajiya Dije, shi ne ma yayan Sanusi din, don shi an haife shi cikin 1982. Muntari da Sanusi sun halarci Firamare ta cikin Kwalejin Tarayya ta ‘Yammata ta Bakori, sannan su ka wuce Kwalejin Tarayya ta Daura inda su ka yi karatun sakandare.

Sanusi ya yanke shawarar fara waka ta dailin wani mafalki da ya taba yi na mahaifin nasa. Inda Shata, a cikin mafalki ya ke tambayon sa ‘shin mi ya ke yi yanzu?’ Sai ya ce mas aba ya yin aikin komi yanzu. Sai Shatan ya ce masa ‘to tunda ga kalanguna nan an bari ya dauka mana ya nemi abinci da su’. Don haka sai ya fara gabatar da kan sa a gidan Tarihi na Katsina lokacin wani buki. Ya kuma iya wakokin Shata ya na kuma kwaikwayon irin muryar sa da salon sa. Bayan wannan shi ma Sanusi ya na da tarin wakokin sa da ya rera ma masoyan Shata da kuma masoyan sa.

Mu kwana nan.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: