Shugabancin APC A Kano: Al’umma Sun Nemi Murtala Zainawa Ya Fito Takara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Shugabancin APC A Kano: Al’umma Sun Nemi Murtala Zainawa Ya Fito Takara

Published

on


‘Yan jam’iyyar APC da dama a jihar Kano na ci gaba da matsin lamba da kira ga daya daga cikin jigo a jam’iyyar, Alhaji Murtala Alhasan Zainawa a kan ya fito domin a fafata da shi a takarar neman shugabancin jam’iyyar na jihar Kano.

Masu wannan kiraye-kiraye daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun yi la’akari ne da cacantarsa da kuma yadda Alhaji Murtala Alhasan Zainawa yake kula da ‘yan jam’iyya da kula da ci gabanta, saboda haka suke ganin shi ne kadai zai iya kawo hadin kan ‘yan jam’iyya, wannan kuma shi ne  abin da ake bukata domin samun nasara a zabubbukan dake tafe.

Sun yi nuni da cewa, Murtala Alhasan Zainawa nada matukar burin ganin ci gaban jam’iyyar APC a dukkan matakai ta yadda zata sake samun nasara a zabukan dake tafe, sau da dama da kudin aljihunsa yake mata hidima koda yaushe idan bukatar hakan ta taso kuma dan siyasa ne mai kwarewa a harkokin siyasa duba da irin rawar daya taka tun a siyasun baya har zuwa na yanzu, don haka ba wanda ya kamata asa a gaba don a sami ci gaban jam’iyyar daya wuce shi.

Masu wannan bukata ta neman Zainawa ya tsaya  neman takarar shugabancin jam’iyyar APC na Kano sun ce duk abin da zai kare kima da darajar Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zaka sami Zainawa a kan gaba saboda soyayyarsa da kishinsa garesu.

Daya daga wadannan masu  kiraye-kiraye  ya ce, ya kamata duk mai ruwa da tsaki a harkar zaben jam’iyyar a jihar Kano  da za a yi kuma yake son ci gabanta da suyi karatun ta natsu, su dauko mutum mai kima irin Murtala Alhasan Zainawa ya shugabanci jam’iyyar, wannan zata bada dama a rungumi kowa da kowa kuma a kauda duk ‘yan matsaloli dake tasowa..

Advertisement
Click to comment

labarai