Za Mu Kafa Kungiya Domin Fidda Shugabanni Na Kwarai (II) -Rimin Zayam — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Za Mu Kafa Kungiya Domin Fidda Shugabanni Na Kwarai (II) -Rimin Zayam

Published

on


Ci gaba daga jiya…

Mene ne ya sanya kake damuwa sosai kan hakan ne kam?

Yanzu kamar abin da ke faruwa a nan jihar Bauchi sai ka ga mutum ya sayi amsakuwa (lasifika) na massalaci sai ya je ya ce maka ya kawo ci gaba wa jama’a, har ma ka ji ya ce maka Sadakatujjariya ne, ko ka ga wani ya kawo kafet din massalaci sai ya ce maka ya kawo ci gaba, ko kuma sai wani dan siyasa ya je asibiti ya dauki dubu 2 biyu yana raba wa marasa lafiya sai a ce ya kawo ci gaba, ta ina ne ci gaba a nan? ci gaba a siyasance ka kawo hanya a garinku, ka hada kan kasarka ka kuma yi kokari ka taimaki jama’an da suka kawo ka ba, ka dauki dubu 50 ko 30 ka ce ka taimakesa ba, a’a ka yi masa hanya shi ma ya tsaya da kafafunsa.

Yanzu abin da ke neman ya samemu, tun lokacin da aka kafa majalisu akwai maganar kan iyaka, idan kuka dauki wani shashasha kuka tura majalisa wanda bai san mene ne matsalar kasar nan ba, bai san kuma ina ne ma kasar nan ta sanya a gaba ba, mene ne matsalar Arewa, mene ne matsalar da ke gaban Arewa, dukkani wani dan siyasar bai ma san wadannan matsalolin ba, amma jama’a za su turasa majalisa, dole jama’a su tsaya su duba wannan lamarin.

Idan talakawa ba su tsayu suka zabi wadanda suka dace ba, to tabbas akwai matsala, talakawa su tsaya su yi zabi na gari, su duba mutum ba wai wace jam’iyya ya fito ba, a kowace jam’iyya mutum ya fito su zabe shi matukar sun san mutumin zan yi musu aikin da ya dace, zai mutunta sarakuna, zai taimaki talakawansa. Saboda haka muna rokon mutane su tsaya su bi shugabanin da suke kan mulki yanzu.

Yaushe ne kuke sa ran kaddamar da wannan sabowar kungiyar taku, kuma wasu irin mutane ne za su kasance a cikin kungiyar?

Kowani dan kasar Nijeriya zai iya shigowa cikin wannan kungiyar, dan jarida ne, dan kasuwa ne, dan siyasa ne, mai jam’iyya, marar jam’iyya, mace, na miji, baligine kowa da kowa muna son kowa ya shigo kuma kowa zai iya mallakar katin shaidar kasancewa mamba. Idan lokaci zabe ya yi jama’a sai su tsaya su duba wanda ya dace sai su zabe shi. Kowace jam’iyya kake ciki ba hidimar addini bane, dukkanin jam’iyyar da mutum ya fito a duba waye shi, kuma wace irin gudunmawa zai iya bayarwa. Za mu fitar da wannan kungiyar tsare-tsari wanda zai taimaka wa jama’a sosai.

Jama’an jihar Bauchi za su so ganin wannan kungiyar ta fara aikinta, ya za ku yi wajen fadakar da jama’an jihar da sanar da su?

Eh za mu yi kokarinmu ta jaridu ne, rediyo ne ta Magana da kuma tuntubar jama’a dukka za mu yi wajen sanar da jama’a manufarmu. Kungiyar za ta tashi ne tun daga karamar hukuma, ta yi jaha, za mu yi a Arewa Maso Gabas, za mu yi a Arewa za kuma mu yi wannan kungiyar a fadin kasar nan ta Nijeriya domin fidda jagorori na kwarai masu kishin jama’ansu.

Amma fa lokacin gudanar da zaben 2019 ya karato kuna da lokacin yin wannan gagarumar aikin da ke gabanku kuwa?

Waye ya san gobe ban da Allah? Da ni din da kai din waye ya san zai kai gobe? Shi ma mai neman kujerar yana da tabbacin zai kai gobe ne? to sai me?

Da kake maganar jam’iyya, akwai batun da aka kawo na cewar dan takara ya tsaya neman kujera a kashin kai ba tare da wata jam’iyya ba ya kake kallon wannan batun?

Ai maganar tsayawa takara a kashin kai, idan mutum ya ga shi hakan zai yi kuma hukuma ta amince da wannan, ‘Independent Candidate’, idan aka samu wanda ya fi wanda jam’iyya suka tsaida sai a yi shi, mu fa muna maganar mutum ne, kuma mun san kowa, wasu abokanmu ne wasu ma kannenmu, a yanzu dai yayunmu basu da yawa, don haka za mu kafa kungiya kuma za mu gaya wa jama’a su zo su shiga, amma fa shiga kungiyarmu ba zai hanaka yin jam’iyarka ba. Idan jam’iyyarka ta tsaida nagartacce sai ka yi wanda jam’iyyarka ta tsaida, idan kuma ba haka ba sai ka nemi wanda zai taimakeka.

Ranka dade baka fargabar kar wannan kungiyar taka ta yi irin na Obasanjo yanzu ga shi kungiyarsa dai ta lume a cikin wata kungiya?    

Ai Obasanjo mayaudari ne, Obasanjo bai son Arewa, Obasanjo kule a cikinmu. Don haka ‘yan siyasar yanzu zai yi wuya su gane hakan, mutum ne ya ce bu-yace-me, amma tabbatacce Obasanjo baya son Arewa, amma lokaci zai zo da jama’a za su gane komai, Obasanjo ya yi mana auren dole, ya san ba’a so ya yi mana, ya kuma yi mana abubuwa da yawan gaske. Amma Allah ba zai barshi ba.

Daga karshe mene ne za ka shaida?

Muna godiya wa Allah madaukakin sarki, sannan muna sake kira ga jama’an kasa da su nutsu, su sake jaddada zaman lafiya, sannan kuma kowani dan kasa ya nemi katin kada kuri’arsa ya tanadar waje guda ya adana sosai, sannan kuma ina kira ga jama’a da suke sanya ido sosai kan masu neman takara, kama daga sanata, kansila, gwamna shugaban kasa da dai sauran kujeru kowa ya tsaya ya duba sosai ya ga waye ya dace da ci gaban yankinsa gabanin zabensa ba wai jam’iyya ba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!