Connect with us

KASASHEN WAJE

Gwamnatin Nijar Ta Bude Dakunan Kwanan Jami’ar Abdumumuni Da Ta Rufe

Published

on

Gamsuwa da yadda kungiyar dalibai ta kasa ta soma biyayya da wasu sharuda da gwamnatin Nijar ta gindaya a matsayin na share fagen shiga tattaunawa a tsakanin ta da dalibai ya sa hukumomin ilimi yanke shawarar sake bude wuraren kwanan dalibai inji ministan Ilimi Yahuza Salisu, inda ya ce wajibi ne gwamnati ta bude wuraren kwana da wuraren abinci domin su ci gaba da karatun su tunda sun janye yajin da sukeyi.

 

Shugabannin kungiyar dalibai sun yaba da wannan yunkuri da suke kallo a matsayin matakin kubutar da sha’anin ilimi daga dabaibayin da yake fama dashi.

Tsalha Kaila wani kusa a kungiyar dalibai ya ce za ayi amfani da wannan yajin aiki domin a duba wadansu abubuwa wadanda dalibai ke bukata lallai, gwamnatin kuma tayi alkawarin daukar matakai domin kawo karshen matsalolin da ke hana ruwa gudu a jami’oin kasar ta yadda baza a sake samun tarnaki ba a fannin ilimi.

aba kuke yi ko kuma baya?
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: