Connect with us

NAZARI

Illar ‘Yan Mulkin Mallaka Ga Al’adun Afrika

Published

on

Mulkin mallaka,kalma ce da malaman tarihi kan yi amfani da ita a mafiya yawan lokuta wajen kwatanta zamanin da ke tsakanin shekarun 1800 zuwa 1960 na tarihinAfrika.

Mulkin mallaka ya faro ne sakamakon fara samun canja-canje a kasashenTurai,  bayan yakin duniya na II, wanda ake jin shi ne ya kawo sauyi a tarihin duniya.

Mulkin mallaka,shi ne inda wata kasa daga waje ta zo cikin wata kasar ta daban ta kuma salladu a kanta, ya kasance kasar ta wajen ne ke gudanar da dukan al’amurran da suka shafi iko da mulki na wannan kasar. Ta kawo mata irin ci gaban ta, iliminta, addinin ta (AddininKirista) al’adu da makamantan hakan, da sukarika aukuwa a zamanin na ‘yan mulkinmallaka.

Zama nin na ‘yan mulkin mallakan, ya kawo wa Afrika sabon babi, daga babin mulkin danniya da fin karfi, rashinwayewa da jahilci, zuwa yanayi na bin tsari da kuma sabbin dabaru ga mutanen na Afrika wadanda a baya an san su ne kawai da dogaro da sana’o’in Noma da kamun kifi.

Al’adun na Afrika suna kunshe ne da siyasa, al’amurran rayuwa, tattalin arziki, Addini da dai sauransu wadanda mutanen na Afrika kan yi amfani da su a tsakaninsu kafin zuwan na ‘yan mulkin mallakar. Ana kuma iya ganin wadannan din ne a cikin al’adunna Afrika wajen auratayyarsu, zamnatakewar iyali, kabilu, kyaututtukansu da kuma sunayensu, hadi da kwarewa, bukukuwan al’adu, tufafinsu, kade-kade da raye-rayensu da dai sauransu.

Sakamakon mulkin mallakan ne kan ‘yanAfrikan, ya kawo rugujewar al’adun na Afrika ta wadannan hanyoyin.

Sadaukarwar da suke yi a makabartu, bakin rafuka, saman tsaunuka dominsu nuna godiyarsu da bukatunsu ga ababen bautarsu na Afrika, wadanda duk a yanzun ba saika ta shigen wadannan abubuwan, suna ma ganinsu a matsayin abin dariya ne kadai.

Al’adar suna sanya tufafi misali daura, Ankara, Bagdad, Isiagogamata, yanzun duk sun zama kauyanci.

Yanzun mutan nan na Afrika suna sanya tufafi ne irin na Turai mazansu da matansu da sunan wayewa, sun bar tufafin su masu tsada da nagarta wadanda kan rufe masu jikinsu bakidaya.

A fili yake, rungumar da muka yi na yin amfani da harshen su naTuranci a matsayin harshen mu na kasa, hakan yana matukar kashe namu al’adun. Misali a nan shi ne inda za ka iya samun, cikakken yaro dan asalin Afrika, amma kuma ya ce maka shi ba ya iya ji ko magana da harshen sa na asali, saboda na taso ne a Lagas ko kuma Abuja, tamkar wadannan wuraren ba a cikinAfrika ne sukeba?

Bukukuwan da suka saba yi a duk shekara da wasu lokuta na musamman, kamar na bukin zuwan sabuwar doya, kamunkifi, bukukuwan Aure, da sauransu, yanzun duk sun shude saboda yanzun ‘yan Afrikan suna can manyan shagunan cin abinci ne na zamani suna sheke ayarsu.

A fannin tsarinmu na ilimi kuwa, duk an fi mayar da hankali ne a kan harshen Turanci a maimakon harshen mu na asali kamar su, Swahili, Asante, Yarbanci, Inyamuranci, Hausa da sauransu, an manta da cewa, ba wani harshen da za a ce ya fi wani. Sai kuwa ana karantar da wadannan harsunan a kanana da manyan makarantunmu ne kadai za mu iya gadarwa da zuriyar namu da harshen namu na asali.

Don haka ya kamata duk dan Afrika ya sanya hannu wajen ‘yanto al’adun namu, da farko dai, duk dan Afrika ya ji, ya kuma yi tinkaho da cewa shi dan Afrika ne, yarika yin magana da harshensa na asali a duk inda ya tsinci kansa cikin wannan duni yar, sannan kuma ya tabbatar ya sami lokacin da zai rika koyawa ‘ya’yansa harshen nasa na asali domin a farfado da al’adun namu na Afrika.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: