Connect with us

LABARAI

Mu Kara Kaimi Wajen Aikata Ayyukan Alheri A Watan Azumi

Published

on

An yi kira ga al’umar musulmin kasar nan da su kara kaimi wajen aikata ayyukan alheri  acikin watan azumi wanda ya yi wannan kira shi ne shugaban manoman jihar Katsina Alhaji Tukur Kankara. Shugaban ya yi wannan kirane a lokacin da yake zakkar kayan amfanin gona wanda ake amfani da su a wajen abincin azumi kamar gero , masara, dawa, shinkafa, farin wake, da sauran makamnatasu Alhaji tukur ya cigaba da cewar  wajibi ne musulmi ya kara kaimi wajen aikata ayyukan alheri acikin watan azumi a cewarsa musulmi musamman masu hanu da shuni da sauran al’ummar musulmi a cikin wannan wata na azumi mai zuwa surinka nuna halin tausayawa wadanda basu dashi kokuma mabukata wajen ciyar dasu da sauran tallafi da aka bukaci musulmi ya yi cikin watan azumin wanda hakan ke kare dan’adam akan wadansu bala’oi nayau da kullum  da kuma samun wani kaso a cikin ladarda ubangaji kera ba ma musulmai sannan ya ci gaba da cewar suma yansiyasa musamman shuwagabanni a cikin hidimar su ta siyasa su ware wani kaso na musamman domin tallafama mabukata ba wai sai lokacin siyasa ba ko lokacin da suke neman kuri’a sannan zasu taimaka injishi taimako anason a rika yin shi a kowane lokaci

Da ya maida jawabinsa a kan yan’kasuwa kuwa musamman masu sayarda kayan masarufi a cikin azumi cewayayi suma yan kasuwar suna da muhimmiyar rawar da yakamata sutaka a cikin azumi na sayarda kaya kan farashi mai kyau domin tausayawa talakawa da sauran mabukata ya ci gaba da cewar kamata ya yi yan kasuwar su rage kudaden kayan abincin a cikin wannan watan mai makon kari da suke domin samun ladar wannan wata mai alfarma kuma yaci gaba da cewar yana taya yan uwa musulmai murnar zagayowar wannan wata na azumin bana

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: