Connect with us

WASANNI

An Kulla Brazil Da Faransa Su Hadu A Wasan Karshen Kofin Duniya 1998 –Platini

Published

on

 

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, wato Eufa, Macahel Platini, ya bayyana cewa daman da gangan aka hada rukuni rukunin da aka hada a gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Faransa a shekarar 1998 domin Brazil ta hadu da Faransa a wasan karshe.

Ya cigaba da cewa, an saka Faransa a rukuni na A yayinda aka saka Brazil a rukuni na C domin kada kasashen biyu su hadu sai a wasan karshe kuma hakan akayi domin sun hadu.

Ya kara da cewa hakan yana nufin kowacce shekara ma ana tsara irin abinda akeson tsarawa domin a bawa wata kasar dama wajen samun damar lashe kofin.

Ya cigaba da cewa idan anason irin wannan tsari damar tun a rabon rukuni rukuni ake tsarawa kuma idan anyi abin cikin nasara sai kaga abinda akeso ya kasance kamar yadda akayi nasara a shekara ta 1998 din.

Ya ce kowacce shekara akwai kasar da ake tsarawa zata samu nasarar lashe kofin sai dai ana samun cikas saboda kwallo komai yana iya kasancewa kamar yadda kowa yasani a kowanne lokaci.

Platini dai a yanzu haka yana zaman dakatarwar da kotun kula da wasanni tayi masa sakamakon kamashi da akayi da laifin cin hanci da rashawa a hukumar kwallon ta turai kuma tuni yafara zaman dakatarAwar tasa na tsawon shekara hudu.

Faransa ce dai ta lashe gasar cin kofin duniya da aka fafata a kasar a shekarara ta 1998 bayan ta lallasa Brazil daci 3-0 inda Zidane ya zura kwallaye biyu sai kuma dan wasa Petit yaci kwallo ta uku kuma ta karshe a wasan.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: