Connect with us

RAHOTANNI

Dan Nijeriya Na Fatan Gwamnati Ta Sassauta Manufofinta

Published

on

 

Game da matsalar tsaro da Nijeriya ta fada musamman rikicin Boko Haram, wanda ya fi tayar da hankalin kowa kusan shekara goma, tun rayuka ba su salwanta sosai ba idan ba a mance ba akwai wani lokaci da wani mai suna Mohammed Marwan kakakin Boko Haram ya taba fitowa kafafen watsa labarai ya bayyana aniyar su na neman sulhu duk da cewa an kira su kashi da dama don su zo a yi sulhu, amma sai an fara magana sai azo a tattara su aje a harbe. Marwan ya ce akwai shirin sulhun da suka je inda manyan shugabannin a lokacin Goodluck suka tura sama da mutum 30 su uku kacal suka kai labari, sun je Kaduna taron sulhu su11 shi kadai ya je shan mai a mota ya tsira bayan ya dawo ya taras an harbe sauran.

Sun nemi sulhu a Kano Marigayi Sarki Ado Bayero ya ce duk inda aka gan su a kashe ana zaton shi ne yasa suka kai masa hari a wancan lokacin. Sarkin musulmi da manyan arewa sun nemi gwamnati ta martaba shirin sulhun a kira su a zauna tun ba a samu asarar dukiya da rayuka kamar wanda aka samu yanzu ba wato shekaru biyar baya amma lamarin ya faskara a wancan lokaci kuma ana gani kamar laifin waccan gwamnati ce ta Goodluck.

Akwai shirin sulhun da aka shirya a baya karkashin Sheikh Ahmed Lemu da Dokta Datti Ahmed da Sheikh Dahiru Bauchi amma kowa  idan ya lura gwamnatin Jonathan ba da gaske take yi ba bata da bukata sai ya janye jikinsa daga kwamitin, don bai san me zai  biyo baya a kan sa ko iyalen sa ba. Zan tuna lokacin da Sheikh Dahiru Bauchi ya kira taron manema labarai a gidan sa da ke Bauchi ya nuna mana takardar shirin shiga tsakani da za su yi tare da wani babban malami a jihar Yobe wanda yawanci su Mohammed Yusuf sun yi karatu a wajen sa. Amma an fara shirin ba a jima ba ya sake kiran mu ya ce daga yanzu ya janye wannan magana ya fitar da hannun sa don ya ga gwamnati ba da gaske ta ke yi ba,  yau kusan shekaru hudu kenan babu abin da ya canza game da wannan yaki illa abin da ba za a rasa ba na tsaida watsuwar lamarin zuwa wasu jihohin kasar nan.

Sakamakon wadannan rigingi mu an nakasa kasuwancin arewa, an kona wasu an rusa gidaje masu yawa an kona wuraren sana’a masu yawa gonaki da garuruwa sun zama kufayi,  har yanzu akwai kananan hukumomin da an kasa zama cikin su duk da himmar jami’an tsaro a karkashin wannan gwamnati,  ya kamata idan an kashe maciji a sare kai ta hanyar binciko masu ci da ceto da sunan tashin hankali a Nijeriya. Gwamnati ta binciki asalin yadda ta ke kashe kudi da masu cin moriyar lamarin da kuma abubuwan da suka faru a baya na zargi kala kala, kama daga tashin jirage da ake cewa suna kai kayan aiki tungar Boko Haram a wancan lokacin a bi a gano gaskiyar lamarin da sauran zarge zarge na badakala mai yawa da ke faruwa.

Haka kuma sana’ar da matasa suka dogara da ita musamman tuka babur na acaba yanzu an wayi gari a yawancin Jihohin arewa an hana, lamarin da ya kara yawan matasa marasa aikin yi yadda masu son zuciya suka fada cikin aikata miyagun ayyuka alhali babu wani dalili da zai sa a hana yin acaban don rage zama kashe wando tsakanin matasa. Abin da ke faruwa a Kano na hana dubban daruruwan mutane sana’ar acaba, wanda idan aka kiyasta mutanen da aka haramta musu wannan sana’a a arewa sun kai kusan mutane milyan takwas. Wannan mataki ya haifar da karin zauna gari banza suna karuwa inda suke sa bayin Allah barci da ido guda ido daya na bude.

Wadanda ke son karatu kuma kudin makaranta ya fi karfin su wadanda suka yi karatu kuma sun zamo zauna gari banza babu aikin yi, kuma duk da cewa an fara samun zaman lafiya gwamnatoci sun ki daga dokar sai dan abin da ba za a rasa ba, to ina muka dosa? Mutane sun yi  ta korafi kan hana acaba, ‘yan kasuwa kuma an wayi gari wanda ke cinikin dubu dari da kyar ya yi dubu ashirin, saboda manufofin tattalin arziki masu tsauri, ya sa kamfanoni da dama sun rufe ‘yan kasuwa masu yawa sun tsiyace yawanci sun cinye jarin wasu kuma har sun dangana da gidajen yari saboda sun taba dukiyar abokan hulda.

Haka kuma idan matsayi za a raba yawanci inda aka cire dan arewa sai a maye da dan kudu, a wancan lokacin. Idan kuma an nada dan arewa zaka taras ba mai kishin arewa ko mai taimako ake ba matsayin ba, zuwan wannan gwamnati ta fara gyara yadda aka yi wa ‘yan sanda da wasu kalilan. Da farko an fara kamar za a yi gyara sosai amma yanzu an kusan komawa gidan jiya saboda duk wani gurbi da ya fito idan dan Arewa bai san wani ba, ba ya samun karbuwa sai ya bayar da cin hanci na makudan kudi.

An hana daukar ko da yara zuwa makaranta ko mutum ya goyi matarsa a mashin, ko neman abinci alhali gwamnati ba ta kawo wata hanyar da za ta maye wannan da aka hanaba, kuma ko ta yi alkawari baya cika alhali akwai dukiyar da za a iya komai na ciyar da mutane da arzikin su gaba.

Wannan gwamnati ta fito da karin nata manufofin da suka shafi rufe kan iyaka da makamantan su yadda mutane ke ta rasa ayyukan yi, kuma matukar matashi ba abin yi to abokin shawarar sa shaidan ne. Wannan yasa ko masu garkuwa ko ‘yan fashi aka kama da manyan barayi yawanci matasa ne. Don haka samar da aikin yi ko karatu kyauta hakki ne ga gwamnati don a samu ci gaba a raba matasa da zaman banza. Idan kuma an ji hassadar kudin da za a kashe a dauki matasa aiki na gaskiya to za a kashe kudin wajen daukar jami’an tsaro da sauran ma’aikata don daidaita halayen mutane ko magance ayyukan ta’addancin da marasa hakuri da talauci ke aikatawa na cutar da kasa da mutanen ta.

Hatta masana’antu da ake da su yawanci sun wargaje basa aiki an rufe an kori mutane saboda tsadar gudanarwa ko neman kudin haraji da sauran kudin shiga daga gwamnati, lamarin da ke kara yawan lalatattun mutane maza da mata, batun da ke haifar da tsoro da rashin alkibla a zuciyar maza da mata babba da yaro.  Lalata tattalin arzikin arewa na cikin ajandar ‘yan kudu, balle yanzu da ya hada har da da karyewar tattalin arzikin mutane masu yawa da karuwar rashin aikin yi. Idan haka kuma ya ci gaba ba makawa sai ‘yan kudu su fara maganar a raba kasa saboda kullum kiran ‘yan arewa suke yi kaska mai shan jini ba mu da komai sai tarin almajirai da marasa aikin yi.

Kafin mu farfado daga barnar da aka yi wa arewa sai an sha wahalar gyara tarbiyyar  mutune da dama saboda yadda wahala da yaki suka lalata tarbiyyar mutane da arzikin su da mutuncin su musamman matasa maza da mata. Mutanen mu kar su zaci za su dawwama a mulki kuma kar su zaci idan ‘yan kudu suka ga fitintinu da rashin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a arewa ba  abin da za su nema nan gaba sai kowa ya ci gashin kansa  kamar yadda wasu daga cikin su ke ta wannan gwagwarmawa a karkashin Biafra da neman yankin Niger Delta. Don haka a gyara kasa kowa ya ci moriya a samu zama lafiya matasa su samu abin yi hakan shi zai sa gwamnati ta zauna lafiya mutanen kasa su zauna lafiya.

Amma idan aka ce jiki magayi gyara ake yi kowa ya ji a jikinsa ba tare da la’akari da irin barakar da ake samu na lalacewar halayen mutane ba za a wayi gari matsaloli sun taru a cikin kasa ko wannan gwamnati ta tafi za ta bar baya da kura, don  za a wayi gari matasan sun hana kowa rawar gaban hantsi musamman wannan lokaci da ake fiskantar siyasa mai zafi a Nijeriya kowa zai iya tara dukiya su hana shi natsuwa waje guda don ya ci shi da iyalensa sai ko idan zai gudu ya bar kasar.

Dabara ta ragewa mai shiga rijiya musamman ‘yan siyasa da masu mulki da jami’an tsaro da ‘yan bokon arewa su yi karatun ta natsu don nemawa ‘ya’yan su da jikanun su makoma ta gari, saboda idan har Allah ya kawo wannan lokaci da za a yi fama da matasan fiye da yadda ake a halin yanzu matasan za su kasance masu cin zarafin mutane a siyasance da zamantakewa da kuma neman hanyar da za su rayu su ci su sha ta ko halin kaka, don haka ya kamata tun yanzu kowa ya yi tunani da addu’ar neman hanyar gyara kasa a dauki ayyuka a ma’aikatun da suka durkushe don su farfado,  a taimaki manoma su yi noma ta gaskiya ba yaudara ba, kuma a temaki kamfanoni da jari a daina damun su da yawan kawo kudin shiga wa gwamnati alhali suna yin kayan ba ciniki wasu faduwa suke yi kullum da fata Allah ya sa mahukunta su duba halin da ake ciki su sassauta ra’ayin su rayuwa ta daidaita kowa ya samu shan iska a cikin kasar sa ta aihuwa.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: