Connect with us

SIYASA

Ina Taimakon Jama’a Domin Allah Ne Ba Don Na Tsaya Takara Ba –Dr. Ukashatu

Published

on

 

  1. HAMZA UKASHATU MUSA MATAZU, wanda ma’aikaci ne a Jami’ar ABU da ke Zariya, wani matashi ne dan kishin kasa, wanda ya kafa gidauniyar Ukashatu Foundation, domin tallafa wa al’ummarsa. Wakiliyar LEARDERSHIP A YAU LAHADI, FADILA H. ALIYU KURFI, ta samu zantawa da shi a wata ziyara da ta kai garin Matazu da ke jihar Katsina. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Me ya ja hankalinka har ka buɗe wannan cibiya ta tallafin al’umma, wato Foundation dinka?

To wannan Foundation ina ganin kusa da sama da shekara tara ko goma bayan rasuwar mahaifinmu, muka yi tunanin cewa bari mu dauka a matsayinshi na malamin addini bari mu ci gaba daga abin da ya ke yi, domin duk wanda san shi anan karamar hukumar matazu yasan mutum ne wanda yake kokarin sadaukarwa ta bangaren addini da kuma ɗan abinda ya samu da kuma Albashin shi domin kyautatawa ‘yan uwanshi da sauran abinda ya samu.

 

Me ye asalin buɗe cibiyar tallafin da ka bude da manufofinta?

Maganar Foundation mu mu ka ƙirƙireta, Ina ganin a karkashin Foundation na taɓa kawo Sheikh Muhammad Bin Usman  ya zo ya ba da lakca akan hakkin iyaye akan yayansu, ya bada lakca akan muhimmancin ilimi wanda Foundation ta ɗauki nauyi, sannan kuma karkashin foundation din mun kawo makaranta ta haddar alkurani misali wadda muka ce daga Zariya wadda na yi, akwai makarantar da ba ƙirƙira, tawace a Zariya Madarasatul Sabilul Rashallittahfizul  kur’an, Na ga cewa bai yiyuwa na je garin wasu na yi makaranta, me zai hana na kawo karamar hukumata wadda muka kawo karkashin wannan foundation ɗin ‘yan uwa suka kakkama, muka dauko malamai da ga Malumfashi, Funtua, Zariya, duk ranar asabar da Lahadi suna zuwa nan Matazu dan koyar da yaran, kuma wasu yaran na ma koya ma ɗalibai, sannan wasu daga cikin yaran suna zuwa Gasar Al’kurani su wakilci karamar hukumar Matazu.

 

Wane irin tallafi ku ke bayarwa?

Idan akan aka lura akwai kusan tallafi daban-daban wanda tunda na fara aiki a jami’a Malaman islamiya tun kafin ni inbada foundation a gina wannan makaranta saboda ni na bada bulo wajan dubu biyu kusan shekaru bakwai da suka wuce, na yanka masu wani percentage daga cikin albashina domin a dinga tafiyarwa, idan kuka lura da yanayin garin maganar gaskiya talauci yayi ma mutane katutu, to ni daga cikin albashina nake dauka ina ba su domin tafiyar da ita makarantar islamiyar, So bayan nan har suka samu mazauni nasu karkashin foundation din nayi tunanin bari mu zo mu saka gasar karatun al’kur’ani duk yaron da yafi kowane yaro hazaƙa ta al’kurani ni a karkashin Foundation na bashi kyautar Keken hawa, Haka kuma duk yarinyar da tafi kowace yarinya yawan hadda al’kurani ni a karkashin Foundation na basu kyaututtukan Keken ɗinki, sauran yaran su duka na basu Kwamfutoci tare da shaddodi da sauransu.

 

Shin ko akwai hannun gwamnati a cikin aikin nan?

Wannan babu wani hannun gwamnati, Gwamnati bata cikin wannan hidimar, sannan baccin nan akwai abubuwa, wanda in ka zo karamar hukumar Matazu tun kafin ma na fara tunanin zan fara takara wannan duk kusan abubuwa ne daban-daban,  A wannan lokacin tsohon Kakaki ya zo yayi launching din wannan zan tabbatar da cewa da zuwanshi da komai da aljihuna na dauki nauyi da kuma hadin abinda muke hadawa tsakanimu danginmu. Bayan nan munyi tunanin akwai mata da suke zuwa in na zo Matazu, irin wadanda aka mutu aka barsu da marayu, so a karkashin wannan na gaji da complain in na zo wannan dubu daya, wannan dubu biyu wannan dari biyu na gaji da wannan sai nace da irin wannan kwanda na zo na yi Empowering dn mutane, yanzu idan kana son kayi empowering din mutane ba wai ka koya masu yoghurt ko magi da sauransu ba, ni a nawa tunanin duk sana’ar da za ka koyar a karamar hukumar Matazu ya zaman to sun iya ta kuma anan in anyi ta nan garin  za’a saya, idan ka dauko mace ka koya mata yogut, yogut ba shine matsalar  ‘yan ƙaramar hukumar Matazu ba, wani ba shi da kudin sayenta, wani ko fura ya siya haka nan zai dama ta, akwai local business wanda su matan sun iya amma ba su da halin sana’ar sai nayi designing din form musamman su wadanda mijinsu ya rasu, in sana’ar kosai za ki yi dama wake za a baki, In sana’ar Awarace ke ma ga abin da kike bukata, in Kunu ne ga abin da za a baki, in Kuli-kuli ne wannan ma gyada kike bukata, na yi shawara da ‘yan uwana nace su bani list na mace dari hudu, lokacin amfanin gona ya fito, na samu mai girma gwamnan jihar Katsina nace ma shi ga program din zanyi a Matazu  ya gani yace ai yana son ya zo yayi launching din wannan program din, kinga babu gudummuwar gwamnati, babu hannun gwamnati a ciki, idan kika ga na yi program anan ni nake fita na nemo kudina na yi, akwai ‘yan aikace-aikace da gwamnati take bani ko na je na yi Superbising akwai dan abin da nake samu na allowance, da aljihuna nake cewa ya cancanta in taimaka sannan ina consultancy a unibersity daban-daban sai naga ya cancanta in dawo in dubi mutane na, da wannann mai girma gwamna ya zo yayi launching din kayan sana’ar nan nan mace dari hudu ya ba da, ganin abinda aka yi ya burge shi shi kuma ya basu naira dubu goma-goma.

Kafin wannan na zauna da kungiyoyin marayu shin menene matsalar marayu? In ka dubi hadisin nan na Manzon Allah da yake cewa, “Ranar tashin alkiyama idan kana son Allah ya saukaka ma to ka dafa maraya, dafawar ba wai haka nan ba, A’a ka sanyaya mashi” Sai na duba na ga akwai marayu har abokanmu wadanda suka rasu suka bar ‘ya’ya to kungiyoyin marayun Matazu a karkashin Malam Aminu Musa kafin in tafi indiya yake ce man babbar matsala marayun nan abinda za su ci shine, shima ina Indiya na turo kudi aka shinkafa masara, gero, sugar, da sauransu aka kirawo su suka zo suka karba aka ba marayun, na zagaya islamiya irinta ‘yan darika na ga akwai matan da Uniform ya gagaresu suma na ce a bani mata guda Ashirin a cikin gari, da wajan gari ko ina dai mace Ashirin wajan mace dari gaba daya, muka yi masu uniform muka saya masu litattafai a matsayin gudummuwa ta bangaren ilmi, sannan su ma marayun a cikin wannan abin da aka yi nace a bani marayu dari aka sai masu jikkuna, Litattafai da uniform kowanne aka sanya mai da sauransu.

 

Shi kuma wannan taron da aka yi na tallafi kan me ye?

Shi kuma na lafiya na ziyarci asibiti na ga wata mata ta zo dan ba lafiya uban kuma yana Lagos, wasu maganin naira ɗari ya gagara, tunda likitocin wasu duk abokaina ne da mu ka yi ABU Zariya da su, sai nace masu wace gudummuwa za su bani a ƙaramar hukumata, suka ce wane local ciwo ne ke damun mutane shi babban wanmu Adamu yace, Akwai Ulcer, diabetes, Hypertension, ba mu saka ciwon ido ba nace su yi man kiyashin kamar na mutum dari hudu na je na raba form mutane suka zo suka cika, sai na ga ya kamata a dar da masu ciwon ido, dan kana iya ganin mutum za ku gaisa ma kaga baya gani.

Wannan kuma abu ne da ba zai gagara ba, Milyan biyu kawai ta isa ayi aikin, amma sai ka ga abun na neman ya gagara, wannan ni na yi planning akwai wani abokina da yake Kano Alhaji Adamu, muka amso magani  shima ya ba da tashi gudummuwar, muka amso wajan na mutum dari takwas, cikin ikon Allah Her Edcellency matar Maigirma Gwamnan jihar Katsina Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari ta sa mana rana dalilin wannan ma ta kara itama da katifofi, akwai wani abinci  da ake ba masu tamowa dankwamuso, duk gudummuwarta ne dalilin wannan aikin. Ba zamu iya cewa ba wai gwamnati take da hannu a wannan aikin sai dai ni kamar yadda nake ta fada kowa akwai irin gudummuwar da zai bada kar mu dogara kawai mu ce sai gwamnati, akwai nurses da suka bada gudummuwa da irinsu Maigirma Fagaci da kudinsu da komai kuma sun nemawa garin albarka, kar mu ce komai ya taso sai gwamnati ita kadai mu a yanzu in kana da wani abu kaine ma ya kamata ka taimakawa gwamnatin, wannan shine kadan daga cikin abinda zan iya fada.

 

Wane kira za ka yi ga masu hannu da shuni kan tallafawa al’umma?

To, kiran da zanyi kamar waccan kiran ne da na yi a taron mutum dari hudu, duk wanda Allah ya ba dukiya nan ake barinta, kamar yadda hadisin Manzon Allah yake cewa, “Abubuwa uku za su raka mutu idan ya rasu, amma daya zai tsaya biyun su dawo. Masu hannu da shuni su tuna cewa, dukiyarsu da ‘ya’yansu duk nan za su barsu abin alkhairin da zaka yi shi zaya zauna dakai, saboda haka ya zama wajibi garesu dasu taimaka sai an jajirce dan shaidan baya barin aikin Alkhairi, kiran da zanyi gare su da wadanda ke nan Matazu, dama wadanda ba nan suke ba duk wanda Allah yaba dama ko hamsin ce ya taimaka, wannan shine kiran koda gidanku ne ka taimaka dan ba a rasa mabukata kannanka ko ‘yan uwanka daga karshe zaka ga nasara a rayuwarka, kira ke nan

 

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: