Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Ma’anar Azumi A Musulunci

Published

on

07066366586 ibrahimba182@gmail.com

Azumi a Shari’a shi ne kamewa daga barin ci da sha da jima’i da abin da zai dauki hukuncinsu; tun daga fitowar Alfijir har zuwa faduwar rana ga kebantattun mutane da niyyar bautawa Allah.

 

Dalilan Wajabcin Azumin Ramadan

Allah Madaukakin Sarki, ya wajabta Azumin Ramadana; a inda ya ce, “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku, wala-alla kwa sami takawa”.

Sanannen hadisin nan wanda Imam Muslim ya fitar cikin littafinsa, daga Umar Bin Khaddab RA, da kuma hadisin da aka yi tarayya wajen fitarwa tsakanin Imamul Bukhari da Muslim daga Abu Abdulrahman Abdullahi Bn Umar Bn Khaddab RA, duk sun bayyana wajibcin yin azumin watan Ramadana.

 

Sharudan Wajabcin Azumin Watan Ramadan

Azumin watan Ramadan yana sauka a kan wasu, sakamakon wadansu dalilai da Shari’a ta aminta da su, shi ya sa wajen ci gaba da ayar da ta gabata, malamai suka bayyana ire-iren wadannan mutane, tare da dalilan. Ci gaba da bayani, sai Allah ya ce; “Wadansu kwanaki ne abaiban kidayawa. To wanda ya kasance mara lafiya a cikinku, ko a kan wata tafiya, to (idan ya sha ruwa) sai ya rama a wadansu kwanakin na daban, har ma wadanda za su iya yin azumin, su ba da fansa ta ciyar da abinci ga miskini guda daya, to dukkan wanda ya kara (a kan abincin miskini), to wannan ya karawa kansa alheri. Amma ku rika yin azumin shi ne ya fi alheri a gare ku, in har kun kasance kuna sani. Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, kuma ayoyi bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa tsakanin karya da gaskiya. Don haka dukkan wanda ya halarci watan cikinku, to ya azumce shi. Kuma wanda ya kasance marar lafiya, ko akan tafiya, (to idan ya sha ruwa) sai ya rama a wadansu kwanaki na daban. Allah yana nufin sauki a gare ku, kuma ba ya nufin tsanani a gare ku. Don haka ku cika adadin (kwanakin Ramadan), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da ya yi, kuma ku zamo masu godiya gare Shi. Kuma idan bayi Na suka tambaye Ka game da ni, to Ni kusa nake (da su), ina amsa kiran mai kira, da zarar ya kiraye Ni. To su nemi amsawa ta, kuma su yi imani da Ni, domin su shiryu. An halatta muku saduwa da matayenku a daren watan Azumi, su sutura ne gare ku, ku ma suturu ne gare su. Allah ya san ku kun kasance kuna ha’intar kawunanku, sai ya dawo da ku, kuma ya yi muku afuwa. To a yanzu din ku sadu da su (da daddare), kuma ku nemi abin da Allah ya rubuta muku, kuma ku ci, kuma ku sha har farin zare ya bayyana daga bakin zare na alfijir, sannan ku cika azumi zuwa dare, kuma kar ku sadu da su alhali kuna i’itikafi a masallaci. Wadannan iyakoki ne na Allah, kada ku kusance su! Kamar haka ne Allah yake bayyana ayoyinSa ga mutane, don su zamo masu takawa” (Bakara: 184 – 187).

Wadannan ayoyi a dunkule sun yi bayanin wadanda shari’a ta dauke musu azumin watan Ramadan; sakamakon wasu dalilai da karbabbu ne a Shari’a da sharadin bayan waraka daga wadannan al’amura, sawa’un rashin lafiyar da za ta hana yin azumin ne, ko mace mai shayarwa ko juna (kamar yadda wasu malamai irin su Ibn Taimiyya da almajiransa, Auza’i, Hasanul Basri da Ibrahimul Nakha’i suka tafi a kan su ma marasa lafiya ne), ko matafiya ne, to za su rama wadannan azumi da suka sha bayan kwanakin azumin, ma’ana bayan Ramadan.

Sannan a cikinsu akwai bayanin wadanda za su ciyar da miskinai abinci sakamakon rashin lafiya, ko tsufa da mai ciki ko shayarwa bisa fatawar Abdullahi Ibn Umar, Abdullahi Ibn Abbas da Ishak Ibn Rahawaihi, kamar yadda Sheikh Nasiruddeen Albani ya fitar a cikin littafinsa Irwa’ Alghalil 4/18 – 24).

Shahid dai, wadannan ayoyi kunshe suke da cikakkun bayanai game da wajabcin azumin Ramadana, da kuma nuni a kan wadanda azumin ya wajaba a kansu, misali dukkanin musulmi, baligi, mai hankali, kuma wanda yake da ikon yi, mazaunin gida. Sannan an bayyana matakan da aka bi wajen shar’anta shi, da kuma wadanda azumin ya zama wajibi a kansu. Domin neman cikakken bayani, sai a tuntubi malamai a majalisunsu domin jin yadda abin yake.

A gefe guda kuma, akwai wadanda azumin Ramadana ya sauka a kan su, ma’ana su azumin Ramadana bai wajaba a kan su ba. Cikin irin wadannan akwai:

  1. Kafiri.
  2. Yaro, amma za a iya umartarsa da yin azumin domin ya saba.

iii. Mahaukaci, wannan kuwa koda balagagge ne, domin ba ya cikin hankalinsa. Kuma Manzon Allah S.A.W ya ce “An dauke alkalami a kan mutum uku: mai barci har sai ya farka, yaro har sai ya balaga, da mahaukaci har sai ya warke”. (Sahihul Jami’ al-Saghir (3513).

  1. Tsoho, amma zai bayar da Mudun-Nabi guda biyu ko ya ciyar da miskini dafaffen abinci a madadin kowacce rana.
  2. Mara lafiya, sai dai akwai ramuwa a kansa bayan ya warke, wannan kuwa ko da bayan shekara nawa ne. Amma cutar da kwararrun likitoci suka tabbatar ba za a warke ba, sai dai kawai a ciyar a madadin kowacce rana.
  3. Matafiyi, zai yi ramako bayan Ramadana.

bii. Mai jini haila ko jinin biki, amma ita ma akwai ramuwa a kanta.

biii. Mace mai ciki ko shayarwa, ita ma za ta iya ajiye azumi idan tana tsoron cutuwarta ko cutuwar abin da ke cikinta, ko abin da take shayarwa idan ta ci gaba da azumin. An rawaito hadisi daga Anas Ibn Malik Al-Ka’abi R.A cewa, Manzon Allah S.A.W ya ce, “Hakika Allah ya dauke wa matafiyi rabin sallah, kuma ya dauke azumi ga matafiyi da mai ciki da mai shayarwa”. (Sunan Ibn Majah, (1667).

A nan malamai suka yi bayanin cewa, idan matukar dai matafiyi da mara lafiya za su rama azumi, to babu abin da zai sa a ce mai ciki ba za ta rama ba.

 

Tsayuwar Watan Ramadan

Azumin Ramadana yana tsayuwa ne da ganin jinjirin watan Ramadana, wato ba a amfani da kirge na kalanda ko lissafin taurari, a’a Manzon Allah S.A.W ya alakanta yin azumin ne da ganin watan na Ramadana.

Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairata R.A cewa, Manzon Allah S.A.W ya ce, “Ku yi azumi domin ganinsa (wato Ramadan), kuma ku sha ruwa domin ganinsa (wato Shawwal). Idan watan ya faku a gare ku (ba ku gan shi ba), to ku cika Sha’aban kwana talatin”. (Sahihul Bukhari (1909), Sahihuul Muslim (1081).

Wani abu muhimmi shi ne, ba sai kowa ya ga watan Ramadan ba sannan ya dauki azumi ba, ana iyar daukar azumi ko da mutum daya ne ya ga watan. Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar R.A cewa, Mutane sun yi kokarin ganin jinjirin wata, sai na gaya wa Manzon Allah S.A.W cewar ni na ga wata, sai Manzon Allah S.A.W ya dauki azumi, kuma ya umarci al’umma da su dauka”. (Sunan Abu Dawud, 2342. Hakim, 423, da Ibn Hibban ³438).

Fadakarwa: Son zuciya da jahilci kan hana wasu tashi da Azumi da hujjar cewa shugabanni ba adalai ba ne, alhali Manzon Allah S.A.W ya ba da dama a bi su hattasallah, ballantana azumi. Bisa haka, idan adali ya shaida ya ga wata, kuma shuagaba ya aminta da ganinsa, to wajibi ne a tashi da azumi. Dangane da sauke azumin kuwa, sai mutane biyu sun shaida cewar sun gani, sannan a ajiye kamar yadda aka rawaito daga Abdulrahman Ibn Zaid Ibn Khaddab yayin da ya yiwa mutane huduba a ranar shakku (wato ranar da ake kokwanton ko Ramadan ne ko ba Ramadan ba).

 

Falalar Watan Ramadan

Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah S.A.W cewa “Wanda ya azumci watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa da suka shude”. Haka nan, a wani hadisi, Manzon Allah S.A.W ya ce, “Idan watan Ramadan ya shigo, ana bude kofofin rahama da kofofin Aljanna, kuma ana rufe kofofin Jahannama, kuma ana daure shaidanu”. Haka kuma an rawaito daga Anas Ibn Malik R.A cewa, Manzon Allah S.A.W ya ce, “Lalle wannan wata na Ramadana, hakika ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin dake cikinsa), hakika an haramta masa alheri dukansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa sai wanda ba shi da rabo”. (Sunan Ibn Majah 1644).

 

Zan ci gaba a sati mai zuwa insha Allah

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: