Connect with us

LABARAI

Mata Na Neman Zarta Maza Wajen Zuwa Makaranta A Sokoto –Farfesa Madawaki

Published

on

A yanzu haka mata, musamman ’yanmata na neman haura maza matasa samari zuwa makarantar boko a jihar Sokoto sakamakon daukar mata kai da gwamnan jihar ta Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, ya yi na bunkasa ilimin mata a jihar da sauran jama’ar Sokoto.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Kwamishiniyar Ilimi ta Jahar Sokoto Farfesa Hajiya Aisha Madawaki a lokacin da ta ke yiwa manema labarai karin haske a Kano bayan kammala wani taro na kwana biyu da a ka yi a birnin na Kano, wanda hukumar USID ta shiryawa jihohin Sokoto da Bauchi don gano matsayin wani shiri da ta ke aiwatarwa na bunkasa ilimin zamani na wadanda su ka shiga makaranta da wuri da wadanda ba su shi ga makaranta da wuri ba a wadannan jahohi biyu.

Farfesa Madawaki kuma ta bayyana wannan shiri na USID na kula da Ilimin karatu da rubutu a wadannan Jahohi yasami Nasara bisa irin matakai da ake dauka na bin diddigi ga ma’aikatan wannan shiri na bikasa ilimi A Sokoto da Bauchi.

Farfesa Aisha Madawaki kwamishiyar ilimi ta Jahar Sokoto ta ce su yanzu sakamakon dokar ta baci na tallafin gaggawa dan bukasa Ilimi cikin sauri da Gwamna Alhaji Aminu Waziri Tambuwal yayi yasa yanzu an samu cigaba sosai ta fuskar ilimi A Jahar Sokoto kuma ga shirin ba da tallafin Naira 5,000 ga iyaye dan tallafar ya’yansu Mata da suka yarda da su tura ya’yansu Mata makaranta domin rage Nauyi ga kowacce Diya makaranta ta yadda kowacce Diya 5,000 ta yadda insunkai 10 ya’a ba da Dubu 50, haka biyu haka uku haka shida da dai sauransu wannan tsari na Gwamnan Sokoto Tambuwal ya sa an sami cigaban Ilimin Mata da ma sauran al’ummar Jahar Sokoto kamar yadda aka sami cigaba a kowanne fanni na rayuwar Sokotawa a Yau ciwar Farfesa Aisha Madawaki. A Kano.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: