Connect with us

KASASHEN WAJE

Moktada Sadr: Hadakar Jam’iyyun ‘Yan Shi’a Sun Lashe Zaben Iraki

Published

on

 

Hadakar Jam’iyyun siyasa a karkashin jagorancin tsohon shugaban kungiyar ‘yan Shi’a Moktada Sadr ta lashe zaben Majalisar Iraki.

Sakamakon karshe da hukumar zaben kasar ta fitar ya nuna cewa hadakar mai suna Saeroun ta lashe kujera 54, inda jam’iyyar Firaiminista mai ci Haider Abadi ta zo ta uku da kujeru 42.

Mista Sadr ba zai iya zama shugaban gwamnati ba da kansa saboda bai tsaya takara ba.

Amma ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa a kan yadda za a kafa sabuwar gwamnatin.

Wannan zaben shi ne na farko tun bayan da Irakin ta fatattaki Kungiyar ‘yan ta’adda ta IS a watan Disamba.

Jam’iyyun da suka goyi bayan Mista Sadr sun gudanar da yakin neman zabe ne bisa turbar yaki da cin hanci da rashawa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: