Connect with us

SHARHI

Sharhin Fim Din ‘Rai…

Published

on

 

Suna: Rai…

Tsara labari: Yusuf M. Ustaz da Yusuf Kalid

Furodusa: Tanimu Akawu

Bada Umarni: Yusuf Khalid

Kamfani: Muzafa Film Production

Jarumai: Sadik Sani Sadik, Zainab Abdullahi (Indomie), Tanimu Akawu, Sadik Ahmad, Abdu Kano (Karkuzu), Maryam Isah Adam da Hon Isa Umar.

Sharhi: Hamza Gambo Umar (Autan Hajiya): 07082268920, hamza71570@gmail.com

 

A farkon fim din an nuna Muhsin (Sadik Ahmad) a zaune a ofishinsa su na tattaunawa da abokin kasuwancinsa (Hon Isa Umar) yayin da aka kira wayar Muhsin aka sanar da shi cewa mahaifin sa yana kwance a asibiti ba lafiya. Muhsin ya tafi asibitin a rikice, likitoci sun bashi shawara akan ya fitar da mahaifin sa kasar waje don a nema masa magani. Muhsin ya amince da hakan amma sai mahaifin sa Baba Alhaji (Tanimu Akawu) ya fada masa cewa yana so yaga Muhsin ya fidda mace yayi aure kafin a bar kasar dashi. Muhsin ya amince kuma yayi masa alkawari duk da a sannan bashi da ko budurwa. Wata rana Muhsin yana tafe a mota shi da abokin sa sai ya kade wata budurwa da ta dauko talla Hanifa (maryam Isah) Muhsin ya bukaci suje asibiti a tabbatar da lafiyar ta amma sai ta nuna masa cewa tafi damuwa da kayan tallan ta da suka zube, saboda idan taje gida za’a daketa, nan take Muhsin ya bata kudi masu yawa suka rabu. Bayan Hanifa ta koma gida ta kaiwa kishiyar mahaifiyar ta kudin talla sai taji dadin ganin kudi masu yawa kuma bata tambayi yadda aka yi ta same su ba. Mahaifin Hanifa (Abdu Kano) ya nuna wa matar sa rashin jin dadin tallan da ake dorawa Hanifa, saboda kasan cewar ita marainiya ce, mahaifiyar ta ta rasu, amma sai matar tasa Baba Asiya ta balbale shi da masifa tana fadin cewa idan Hanifa batayi talla ba mai zasu dinga ci a gidan tunda shi baida karfin da zai fita ya nemo musu, haka ya hakura ya zubawa matar sa idanu ta dinga gallazawa Hanifa gami da cigaba da dora mata talla. A yawancin lokuta idan Hanifa ta fita wajen talla sukan hadu da Muhsin, kuma yakan tausaya mata saboda ganin yadda da girman ta take daukar talla, har ma yakan fadawa abokin sa damuwar sa akan haka amma sai abokin ya bashi shawara akan auren Hanifa ne kadai zai sa ya fidda ta a halin da take ciki, Muhsin bai amince da hakan ba saboda yana ganin shi da ita ba soyayya suke yi ba. Wata rana Hanifa ta dawo daga wajen talla ta kawowa Asiya kishiyar mahaifiyar ta kudi kadan, amma sai Asiya ta watso mata kudin ta nuna masu yawa take so irin wanda ta taba kawo mata, Hanifa ta fada mata gaskiyar wanda ya bata wancan kudin amma sai Asiya ta nuna babu ruwan ta Hanifa taje ko jikinta zata siyar ita dai a kawo mata kudi masu yawa. Bayan Hanifa ta fita ne suka sake haduwa da Muhsin a kan hanya yana tsaye jikin mota da abokin sa, Hanifa ta tsaya suka yi hira, a lokacin da Muhsin zai tafi a bisa tsautsayi sai ya yarda jakar wallet din sa a kasa. Bayan sun tafi Hanifa ta gani ta dauka taje gida ta zauna ta bude tana dubawa. A sannan Asiya ta fito ta karbi jakar ta kwashe kudin ciki zata rike, amma sai Hanifa ta nuna rashin amincewar ta akan haka har ma tayi nasarar fizge jakar daga hannun Asiya ta fita da gudu taje gidan su Muhsin ta kai masa. Zuwan Hanifa gidan su Muhsin ne yasa Mahaifin sa wanda aka sallamo daga asibiti za’a wuce dashi kasar waje, bayan Mahaifin Muhsin baba alhaji yaga Hanifa sai ya bukaci sanin alakar ta da Muhsin, nan take abokin Muhsin dake tsaye a wajen yace ita ce wadda Muhsin zai aura. Hanifa tayi mamaki amma haka tayi musu sallama. Bayan ta koma gida Asiya ta rufe ta da duka, Baba Mahaifin Hanifa ya fito zai kwace ta amma sai Asiya ta tunkude shi ya fadi kasa take a wajen ya mutu. Ganin haka ne yasa Asiya ta dau mayafi ta fice a guje, tana cikin gudu a kan titi mota ta buge ta ita ma ta mutu. Bayan mutuwar su ne gidan da Hanifa take ciki mai gidan yazo ya kore ta saboda rashin biyan kudin haya. Muhsin yazo har gidan su Hanifa yana neman ta bai ganta ba yana cikin neman ta ne ya ganta a cikin juji a zaune. Nan ya dauke ta suka tafi gidan su daga nan ya auri Hanifa.

An daura auren Hanifa da Muhsin rana daya da na wani abokin sa. Hanifa tana zaune a gidan Muhsin cikin kwanciyar hankali har zuwa lokacin da ta samu ciki kuma suka haihu lokaci daya ita da matar abokin sa Husna (Zainab Indomie) bayan su Hanifa sun haihu ne sai Muhsin ya bukaci ta shirya zasuyi wata tafiya zuwa wani gari tare da abokin sa da kuma husna. A hanyar su ta tafiya ne motar su tayi hatsari ta kama da wuta. Sakamakon haka ne yasa abokin Muhsin ya rasu tare da jaririn husna (Zainab Indomie) ita kuma Hanifa aka neme ta sama ko kasa ba’a ganta ba. Kowa ya zaci ko ita ma ta mutu. Ganin halin da Husna ta shiga na rashin mijinta ne yasa Muhsin ya sadaukar mata da kyautar dan sa, ba tare da ita ta san cewa dan ta ya rasu ba, likitan da ya duba ta da Muhsin ne kadai suka san gaskiyar lamari. Muhsin ya cigaba da zama shi kadai babu mata amma yana kula da Husna da dan shi. Bayan wani dogon lokaci kannen mijin Husna suka dawo gidan ta da zama saboda suna so su kwashe dukiyar ta kasancewar mijinta kafin ya rasu yana da dukiya. Yayin da Muhsin yake tsananin kula da Husna da dan ta Salim. Alakar dake tsananin Muhsin da Husna ta janyo kannen mijin ta sun soma tunanin ko soyayya suke wanda hakan yasa Husna ta soma canjawa Muhsin fuska. Wata rana yana zaune a gidan sa cikin damuwa kwatsam sai ga Hanifa ta shigo ita da Hanif (Sadik Sani Sadik) nan take ta bawa Muhsin labarin cewa bayan ta bata ne ta kamu da ciwon mantau kuma ta zauna a hannun Hanif (Sadik Sani Sadik) har ma soyayya ta shiga tsakanin su, suna shirin yin aure Hanifa ta samu lafiya ta dawo hayyacin ta shine suka dawo gida. Muhsin ya yiwa Hanif godiya suka rabu yayin da Hanifa ta cigaba da zama a gidan sa amma likitoci sun fada musu cewa Hanifa ta samu matsala a mahaifar ta abu ne mai wahala ta sake haihuwa. Hakan yasa Hanifa ta tashi hankalin ta har ma ta soma kishi akan irin yadda Muhsin yake bawa Husna da Salim kulawa. ‘yar aikin Hanifa ta tsegunta mata cewa akwai soyayya a tsananin Husna da Muhsin, hakan yasa Hanifa ta rutsa shi da tambaya a sannan ne ya fada mata cewa Salim dan su ne, jin hakan yasa Hanifa ta tada hankalin ta akan sai an dawo mata da dan ta, yayin da Mahaifin Muhsin ya goya mata baya. Muhsin da Mahaifin sa suka je karbar Salim a hannun Husna amma sai taki amince wa da bukatar su har sai da likitan da aka shirya abin dashi yayi mata bayani. Bayan komawar Salim hannun su Hanifa sai yaki sakewa dasu har ya soma yunkurin guduwa, hakan yasa Hanifa ta bukaci Muhsin ya auri Husna don su zauna gaba daya su rike dan su. Husna bata yi musu da wannan bukatar ba ta amince Muhsin ya aure ta ya hada su gaba daya a matsayin iyalin sa.

Abubuwan Birgewa:

1- An yi kokari wajen samar da gidaje gami da sauran wuraren da suka dace da labarin.

2- Sauti ya fita radau, camera ma babu laifi.

Kurakurai:

1- Shin wace lalura ce take damun mahaifin Muhsin? Wadda har tasa likitoci suka dage akan sai an fita dashi kasar waje an yi masa magani, duk da an nuna wa mai kallo cewa ya samu lafiya har ma an sallame shi.

2- An nuna wa mai kallo lokacin da Muhsin yake tsaye a jikin mota suna hira da Hanifa har zuwa lokacin da ya ciro wallet a cikin aljihun sa ya sake ta a kasa kamar bai sani ba. Hakan ya saba da irin yadda mutum yake yadda abin sa, ya dace a nuna ya ciro makullin mota ko waya daga aljihun sa wanda dalilin hakan yasa wallet din sa ta fadi, amma ba wai a nuna ya yadda ita da gangan ba saboda wani sako da ake son nuna wa mai kallo.

3- Bayan rasuwar iyayen Hanifa an ga mai gidan yazo ya kori Hanifa saboda rashin biyan kudin haya, Hanifa ta fita daga gidan ba tare da ta dauki komai ba, shin Hanifa ta mance da kayan sawar su gami da tarkacen su dake cikin gidan ne? Ko kuma shi mai gidan bai san cewa da kayan su a ciki ba ya rufe dakin da kwado? Ya dace aga ko watso musu kayan su ne yayi ba wai ya rufe dakin da kayan a ciki ba.

4- An nuna wa mai kallo cewa Hanifa sun saba haduwa da Muhsin a hanya kafin su yi aure, amma ba’a ga lokacin da ta kwatanta masa inda gidan su yake ba, sai gashi kuma Muhsin yaje gidan su Hanifa yana cigiyar ta bayan mai gidan ya kore ta. Shin dama Muhsin yasan gidan ne?

5- Muhsin da iyalan sa tare da abokin sa sun yi hatsari har motar ta kama da wuta, amma sai mai kallo yaga Muhsin da plasta a goshin sa haka ita ma Husna da plasta a goshi, shin dama idan an yi hatsari an kone a cikin mota haka yanayin kuna yake? Sannan kuma ya dace ace raunin da sukayi ya bambanta bawai su duka a goshi za’a nuna sun ji rauni ba.

6- Bayan su Hanifa sun yi hatsari har ma an zata ta mutu sai kuma aka ga Muhsin ya ajiye mace baliga matsayin ‘yar aiki a gidan sa, a matsayin Muhsin na baligi mara aure bai dace ya ajiye wata ‘yar aiki a cikin gidan sa ba, domin hakan ya sabawa shari’a gami da koyarwa irin ta addinin musulunci.

7- An nuno wasu samari sun zo gidan Husna sun sace mata dan ta Salim, Bayan sun gudu ne Muhsin ya hadu dasu har ma ya bi su ya rutsa su da bindiga, ya harbi daya a cikin barayin yaran, a matsayin Muhsin na wanda ba jami’in tsaro ko dan ta’adda ba shin a ina ya samu bindiga? Ko dama ya san za’a sace dan sa ne shi yasa yayi guzurin bindiga?

Karkarewa:

Shin wani darasi fim din ya ke son isar wa ne? An nuna muhimmancin sadaukarwa, amma zaren labarin sam bai tafi kai tsaye ba kuma babu cikakken jigo a labarin.

 

 

 

 

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: