Connect with us

KIWON LAFIYA

Tsokar Zuciya (2)

Published

on

Yau idan Sarki mafi gwanintar halitta yaso, zan ci gaba da bayani akan tssokar zuciya, da kuma abin da ke sawa ta takure ta harba jini, a inda a satin da ya wuce nake cewa : Wato idan zuciya ta samu matsala fa, to dukkan jikin yana cikin matsala.

Akwai matsalolin dake faruwa a zuciya inda ake samar da sakon lantarki domin yasa zuciya ta harba jini. To idan matsala ta afku a wannan sashe na tsokar zuciya, yanayin bugawar taata zai yi rauni, zagawayar jini a jiki shima zai yi rauni, daga nan kuma sai rashi lafiya.

A kaf jikin mutum, babu inda ake samun tsoka mai siffa biyu, masu aiki mabanbanta, kuma a waje daya sai a zuciya. Haka kuma babu wata tsoka da ta riga zuciya fara aiki. Ita tsoka ce amma ta musamman.

Na’ura mai kambama girman abubuwa wato microscope, ta nuna cewa tsokar zuciya tana da rassa kamar bishiya, sannan wadannan rassa, tsakanin silin tsoka daya da wani silin tsokar na reshe daya, akwai ‘yar tazara kadan; ta inda sakon lantarki daga sili ko zaren tsoka daya zai iya tafiya izuwa daya silin tsokar.

Duk wata tsoka ta jiki, tana zaman jiran sako ne da kuma umarni daga cibiyar gudanarwa, wato kwakwalwa kafin ta motsa, amma banda ta zuciya.

Shin ko kina so ki san yaya zuciya take harbawa ba tare da jiran sako daga kwakwalwa ba? Hakan ta kasance ne saboda wasu halittu masu kama da kulli da Sarkin halitta ya ajiye wurare na musamman a cikin zuciya.

Wadannan halittu masu kama da kulli ana ce musu “nodes”. Akwai na farko wanda yake a aljihun sama na dama na zuciya. Wannan shi ne madugu uban tafiya wato “pacemaker of the heart”. A turancin kimiyyar lafiya ana kiran sa da “sinoartrial node”.

A cikin sa akwai kwayoyin halitta masu kirkiro sakon lantarki da suke bawa zuciya damar bugawa da harba jini. Sai kuma kulli na biyu, ana ce masa “atriobentricular node”. Shima yana da wadancan kwaoyin halitta, kuma yana iya kirkirar sakon lantarki.

Shi wannan kulli na biyu, yana tsakiya ne, wato idan zaku iya tunawa, tsakanin aljifan sama na zuciya akwai shamaki, haka ma tsakanin aljifan kasa na zuciya, akwai wani shamakin a tsakiyar su. Kulli na biyu na a tsakanin shamakin sama da na kasa.

Bari in baku wani kyakkyawan misali. Ka kaddara kana tafiya akan shamakin da ya raba tituna biyu, dama da hagu. Idan ka kai wani gaci, Ai akwai fitilar wuta ko? Sannan daga kasan fitilar akwai wayoyin lantarki ko? To kaddara ka tsaya da tafiyar, a daidai inda fitilar wutar take. Gaba da fitilar kadan, Ai shamakin titin ya ci gaba ko? Madalla.

Ka kara kaddarawa cewa, a tsallaken titin, idan an dan zarta saitin fitilar, akawi transufoma wadda wayoyin ta suka taho ta karkashin kasa suka shiga karkashin fitilar da kake tsaye kusa da ita. Yanzu kuma bara kaji bayani.

Shamakin da ka fara tafiya akan sa, shine shamakin aljifan kasa na zuciya, dama da hagu. Fitilar wuta da ka tarar a akan shamakin, ita ce Kulli na biyu mai samar da sakon lantarki domin harbawar zuciya; kuma kasan wayarin din shi ne har zuwa shamakin da ka taaka, har bayan ka.

Waccan transufoma kuwa, ita ce a matsayin kulli na farko. Abinda yasa na kwatanta shi da transufoma shi ne: saboda aikin da yake yi a zuciya yayi kama da naata (transufoma). Shi ne mafi karfi da sauri wajen samar da sakon lantarki da ake bukata wanda zai bawa zuciya damar bugawa.

Kar ku manta, akwai wayoyin da suka taaso daga “transufoma” zuwa “fitilar wutar”. To hakanan akwai wayarin na lantarki da ya taaso daga kulli na farko zuwa kulli na biyu, zuwa sauran rassan da suke bagwayen zuciya.

Kulli na biyu ya harba wayoyin sa ne cikin shamakin zuciya na kasa. Daga nan wadannan wayoyin su kuma sukayi rassa suka yadu a ko ina a bangon zuciya. Mai zai faru kenan idan aka samar da sakon lantarki a kulli na farko? Kunga hakan zai sanar da tsokar zuciya cewa: ta shirya domin harba jini.

Tsokar zuciya tana bugawa kuma tana hutawa. Amma da za’a tambaye ka, tsakanin lokacin hutawar ta da kuma lokacin da take harba jini, wanne ne yafi yawa? Yaya zaka ce?

Amsar ita ce, lokacin hutawar yafi lokacin aikin tsaho. Amma kuma lokacin ta tsokar zuciya zata huta gaba daya, sai idan mutum ya rasu.

Idan ku na karanta kira, tsari, gini, da baiwar da Rabban yayi wa zuciya, baza ku so ku daina ba. Saboda abin yana da matukar ta’ajibi, sanya tunanin, la’akari, gamsarwa da kuma ilmintarwa har ma da kara ganin girman Sarki, Gwani, mai tsara halitta babu samfur.

 

 

 

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: