Yakamata Buhari Ya Yi Nazari Kan Zabukan APC –Bashar Adamu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Yakamata Buhari Ya Yi Nazari Kan Zabukan APC –Bashar Adamu

Published

on


 

An shawarci shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari da uwar jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya da su sanya ido game da yadda a ka gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar APC a jihohin Nijeriya, don ganin ba su zamanto sanadiyyar fashewar jam’iyyar ba, lamarin da zai iya haifar da faduwar shugaban kasa Buhari da sauran magoya bayan jam’iyyar a zabukan kasa masu zuwa.

Malam Bashir Adamu Azare wani dan siyasa mai talafawa dalibai wajen samun aiki ko karatu wanda da ke garin Azare shi ne ya bayyana haka cikin hirar sa da wakilin mu a Bauchi, inda ya kara da cewa ya kamata shugaba Buhari ya fahimci wadanda ke yin abin da suka dama wajen nada shugabnnin da suke so a APC suna yin hakan ne don son zuciya kuma zai iya haifar da tarwatsewar jam’iyyar nan gaba. Saboda an bata wa magoya baya rai a jihohi da dama, don haka ya bukaci ayi gyara don a jima ana cin nasara a hidimomin raya jam’iyyar.

Ya ce idan kuma ba a yi haka ba za a fiskanci matsala nan gaba saboda yadda ake yin magudi zai iya lalata jam’iyyar APC da tagomashin ta don haka ya bukaci shugabanni daga sama su sa ido don a kare aukuwar tarwatsewar jam’iyyar.

Bayan haka Bashir Adamu Azare ya roki shugabannin wannan lokaci a Nijeriya su kaunaci Allah su lura da mawuyacin halin da mutane ke ciki a kyautata musu a cikin wannan wata saboda mutane su na cikin wahala ba su da abin da za su ci wasu kuma tuni abin da suka dogara da shi suna yin kasuwanci babu ciniki sun cinye jarin, don haka matukar ba a yi sassauci game da yadda ake gudanar da rayuwa ba Allah zai tambayi wadannan shugabanni kuma suma za su shiga fushin Allah idan ba su samar da gyara ba.

Daga karshe ya shawarci mutanen Nijeriya su koma ga Allah su kai kukansu wajen Allah ta hanyar gyara ayyukan su don su samu ci gaba da ingancin rayuwa cikin wannan wata na Ramadan mai alfarma. Don haka ya ce komawa ga Allah cikin wannan wata shi ne zai kawo karshen ko saukin wahalhalun da jama’a ke sha a wannan lokaci.

 

Advertisement
Click to comment

labarai