Connect with us

ADON GARI

Yaren Bayar Da Hakuri (5)

Published

on

Amma siga ko yare na hudu da ake ba wa wanda aka yi wa laifi hakuri da shi, shi ne mutum ya bayyana wa wanda ya yi wa laifin cewa lallai zai yi kokarin ganin ya kiyaye kara faruwar irin laifin a gaba. Wato Ba Zan Kara Ba ko Ba Zan Kuma Ba. Wannan ishara ce da ke nuna tabbacin lallai ba ka ji dadin abin da ka aikata ba, tare kuma da yin alwashin ba za ka kara maimaita shi a gaba ba. Wannan wata siga ce wadda take da tasiri matuka wurin ratsa jikin mutumin da tsoronka ko kuma girman laifin da kake yi masa ya fara shiga tare da tasiri a cikin ransa.

Abubuwa da dama, ana samun samfurinsu mafi inganci ne yayin da aka koma can asalinsu. Don haka, idan mun koma can asali mu ka kalli yadda yara suke bayar da hakuri yayin da su ka yi wa babba laifi. Sawa’un a gida ne ko makaranta, za ka taras wannan yana daga cikin manyan kalamansu. Misali, yayin da yaro ya yi maka laifi, ka dauki bulala, ka nufe shi, ya tabbata dukansa kake shirin yi, kai tsaye zai yi wuya ka ji maganarsa ba “Don Allah ka yi hakuri! Wallahi ba zan kara ba,” ce. Hakan ma kuma abin yake in ma lamarin bai kai na a daga bulalar ba. Yana nan tsakanin ire-iren wadannan kalmomin.

Kamar da yawa daga cikin sigogin. Sau da dama ya fi kyau idan za a yi amfani da wannan sigar a yi mata sharer-fage da daya daga cikin sigogin da suka gabata. Musammam siga ta farko. Wato a fara cewa Ka yi hakuri. Sannan a ce Ba zan kara ba din. Misali: “Don Allah ka yi hakuri, ba zan kara ba.” Kamar dai yadda yaran suke yi.

Mutane da dama kuma abin da suke so su ji kenan. Domin idan mutum ya yi maka laifi, ya ba ka hakuri, ya yarda bai kyauta ba, kai kuma sau da yawa wani abu da zai rika yi maka kai-kawo a zuciya shi ne; “Anya kuwa zan ce na yafe masa? Kar fa kuma in ce na yafe masa gobe ma ya maimaita.” A lokuta da dama, irin wannan tunanin kuma shi ne zai sa wadanda mu ka yi wa laifi su dade suna shawarwari da zukatansu,shin su bayyana sun hakura din, ko kuwa su yi shiru kawai a tafi a hakan cikin duhu. Domin mutane da dama suna da tunanin yayain da mutum ya yi maka laifi, kai kuma ka ja ka yi gum, ba tare da magana ba zai fi kasancewa cikin dari-darin kar ya kara maimaita abin da ya aikata a baya. Saboda ya san har yanzu ba ka gama hakura da wanda ya yi a baya ba.

Irin wannan tunani yana daya daga cikin manyan dalilan kuma da suke sawa a dade a cikin gidajen ma’aurata ba tare da ana magana da juna ba. Suna faruwa ne sakamakon rashin amfani da wannan yare. Wato karkade dukkan wani kokonto daga zuciyar wanda aka yi wa laifin. Mukan ji Uwargida ta yi yaji, ta bar gida tsawon lokaci. Wani lokacin a yi ta faman kai kawo a kan ta dawo, abin ya gagara. Kai ba ma Uwargidan kadai ba, shi kansa Maigida yakan yi yaji. Shi ne irin tarihin da mukan ji na manyan mutane da malamai. Sai mutum ya bar shiga dakin matar ko kowacce daga matansa tsawon lokaci. Tunda shi namiji ba ya yin yaji ya bar gidansa. Kodayake ma akan bar gidan ta wata siga daban. Inda za ka taras magidanci in ya fita daga cikin gida ba zai dawo ba sai tsakar dare, in ya tabbbata matar gidan ta yi barci. Watakila yana can wurin hira da abokansa. Ko kuma wata majalisar, ko da kuwa ba jin dadin zaman wurin yake ba. Idan ma ba mai son zama a wajen ba ne, sai ka taras yana da wani wuri na musamman da zai makale, tamkar ba ya gidan. Misali, mutumin da yke dawowa gida tun karfe takwas, amma sai ya yi zamansa a cikin mota, a inda yake ajiye motarsa, a cikin gidan. Har sai bayan sha biyu, in ya tabbata matar gidan ta yi barci. Ya fito ya shiga dakin.

Alhali akwai abin day a kamata daya daga magidantan ya yi a sami salama a gidan. Wato ya yi kokarin goge duk wani kokonto daga zuciyar wanda ya bata wa ran. Ta hanyar ba shi tabbacin cewa ba zai kara ba. “Ki yi hakuri, in Allah Ya yarda ba zan kara yin hakan ba.” Ko “Ka yi hakuri, in sha Allahu hakan ba za ta kuma faruwa ba.” Wannan shi ne abin da yake gaggawar magance wancan dogon zaman kunci. Ya kuma dawo da sabuwar rayuwa mai cike da walwala irin ta baya, a gidan. Domin dama a mafi yawan lokuta ana yin irin wadannan kaura ne a matsayin horo, ko tabbatar wa mutum cewa ya aikata wani babban laifi da ba za a yafe masa ba har sai nadamarsa ta bayyana. Amma abin mamaki sau da byawa sai furta hakan ya zama wani aiki mai nauyi a bakunanmu.

Ya na da kyau dai mu sani cewa, dole ne idan mutum ya yi amfani da wannan kalmomi, ya kuma yi bakin kokarinsa na ganin ya cika maganar , kamar yadda ya yi alwashin. Wato kar ka ce “B azan kara ba.” Kuma a taras ka kara din. Wannan yana sawa nan gaba ko da ka yi wata maganar makamanciyar wannan a ki aminta da kai.

Sau da dama, mutumin da ka yi wa laifi, kuma ka yi amfani da irin wannan siga don ba shi hakuri, yakan yi maka tambaya , don tabbatar da abin da kake ikirari. Misali, idan ka ce: “Yi hakuri don Allah, in Allah Ya yarda ba zan kara ba.” Sai ya ce maka: “Ka tabbata?” Kar ka ji wata damuwa don wannan tambayar, kuma kar ka ki gaggawar amsa masa. Cene: “ In sha Allahu. “ Domin hakan da zai ji daga gare ka shi ne abin da zai kara kwantar masa da hankali. Ya sami nutsuwa a ransa cewa da gaske ne, abin ya wuce, kuma ba za ka kara maimaitawa ba.

Wannan ma kuma jigo ne mai matukar muhimmanci a yayin tuba. Domin idan muka dubi sharudan tuba ga Ubangiji (Subhanahu wa ta’ala) guda uku da malamai suka fitar, na karshe shi ne: “Wa yanwa an la ya’uda ila zambin.” Wato mutum ya kudiri niyayyar cewa ba zai kara maimaita wannan laifin ba. Wannan dayake Shi Ubangiji Yana ganin zuciyarka kenan. Don haka aka ce ka yi niyya. Amma mutum da ba ya ganin zuciyarka sai ka gaya masa da bakinka,. Cewa daga yau ka yi niyyar ba za ka maimaita wannan laifi ba. Da haka ne shi kuma zai sami nutsuwa ya kara yarda da kai. Maimakon ka bar shi da wasuwasin “Shin in na yafe wa wannan kuwa ba zai kara maimaita ba?”

Mutane da yawa wannan ita ce kalma mafi gamsarwa da suka fi son ji, yayin da ka zo ba su hakuri.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: