Connect with us

LABARAI

Zaben Shugabannin APC A Adamawa: Bangarori Biyu Sun Gudanar Da Zabe

Published

on

Jam’iyyar APC ta gudanar da zaben sabbin shugabanninta a matakin jiha a jihar Adamawa, inda Alhaji Ibrahim Bilal, ya lashe zaben a matsayin sabon shugaban jam’iyyar a jihar ba tare da hamayya ba, sai dai bangarori biyu na jam’iyyar suka gudanar da zabe a jihar.

Kamar sauran zabukan da suka gabata a jihar, zaben sabbin shugabannin ya gudana cikin tsari da kwanciyar hankali da luma, ba tare da an samu wata matsala a ya’yin zaben ba.

Da yake zantawa da manema labarai gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, ya yaba da yadda zaben ke gudana cikin kwanciyar hankali, yace dama haka shugaba Muhammadu Buhari, ya horisu (gwamnoni) da zaben ya kasance.

Yace “gashi yadda kowa ke gudanar da zabensa cikin kwanciyar hankali,wannan shine APC, na yi zabena yanzu cikin kwanciyar hankali, dama haka shugaba Buhari ya bamu shawara mu gwamnoni mu gudanar da komai bisa tsarin doka, kuma abinda mukayi kenan” inji Bindow.

Baya ga zaben Ibrahim Bilal, a matsayin shugaban an kuma zabi Samaila Tadawus mataimakin shugaba, da Wafarninyi Theman, a matsayin sakatare, da Baresta Shagnah Pwamaddi, jami’i mai bada shawara ta fuskar shari’a.

Sauran wadanda sukayi nasara a zaben shugabannin jam’iyyar na jihar, sun hada da Aliyu Bakari, mataikin shugaba na yankin Adamawa ta tsakiya da sakataren kudin jam’iyyar Sa’idu Maitalata Nera, sai kuma sakataren tsare-tsare Ahmad Lawan, da dai sauransu.

Haka shima shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC) Baresta Kassim Gaidam, yace ga yadda ya ga zaben ya gudana cikin tsari, haka ake fatan gani a gudanar da kowace irin zabe, saboda haka sun gamsu da yadda zaben ya gudana.

Shima tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa Ahmad Ali Gulak, ya bayyana zaben da cewa ya inganta,  domin kuwa masu kada kuri’a na kada kuri’a bisa tsari kkmar yadda aka tsara tun da farko.

Ali Gulak, ya shawarci wadanda sukayi nasara a zaben da cewa su yi kokarin hadekan mambobin jam’iyyar waje guda.

Da yake magana da manema labarai sabon shugaban jam’iyyar APC a jihar Ibrahim Bilal, ya godewa Allah bisa nasaran da ya samu, ya roke ya’yan jam’iyyar da su bashi hadinkai domin cimma nasaran jam’iyyar a jihar.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: