Connect with us

SIYASA

Abdulkadir Jauro Ya Zama Shugaban Jam’iyyar APC A Zariya

Published

on

 

A ranar Asabar da ta gabata, jam’iyyar APC a jihar Kaduna Kaduna ta tabbatar da Alhaji Abdulkadir Abdu Zailani a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC reshemn karamar hukumar Zariya, a jihar Kaduna.

Bayanin haka ya na kunshe ne a jawabin wakilin jam’iyyar daga reshen jam’iyyar ta jihar Kaduna, Alhaji Adamu Turaki ya bayyana jim kadan bayan kammala zaben sabbin shugabannin jam’iyyar bisa jagorancin Alhaji Abdulkadir Abdu Zailani, wanda taron zaben ya gudana a filin wasan Kwallon kafa na tunawa da marigayi Alhaji Nuhu Babajo, da ke birnin Zariya.

Alhaji Adamu ya ci gaba da cewar, sakamakon da aka samu ya  yi dai-dai da tsarin gudanar da zabe na jam’iyyar APC a Nijeriya, ba jihar Kaduna kawai ba.Sai ya umurci sabbin shugabannin da aka zaba da su rungumi sauran wadanda ba su sami nasara ba, a zaben da aka aka yi, wannan, a cewarsa, shi ne zai kara wa jam’iyyar martaba a karamar hukumar Zariya da kuma jihar Kaduna baki daya.

A jawabinsa bayan kammala zaben, sabon shugaban da aka zaba Alhaji Abdulkadir Abdu Zailani [JAURO], da farko ya nuna jin dadinsa da yadda daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Zariya, suka ba shi goyon baya, tun daga fara neman shugabancin ya zuwa zaben da aka yi ma sa a wannan rana.

Alhaji Abdulkadir Jauro ya tabbatar da cewar, a tsawon mulkin da zai yi, zai yi aiki da kowa-da-kowa, ba tare da nuna wani banbanci ba, wanda kamar yadda ya ce, salon shugabancin da zai yi, shi zai sa a sami zaman lafiya da kuma ci gaba mai ma’ana a wannan jam’iyyar a karamar hukumar Zariya baki daya.

Ya kuma yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Zariya, wato na daukacin gundumomi goma sha uku da suke karamar hukumar , da su ta ya shi addu’ar yadda ya zama shugaban jam’iyyar lafiya, ya sauka daga shugabancin lafiya, ba tare da samun wasu
matsaloli ba.

Alhaji Abdulkadir Jauro, ya tabbatar da cewar, ba shi da gefe ko kuma wani bangare da zai ce shi ne na shi,ya kara da cewar, tun da sun zo yin gyara ne tare da kawo canji mai ma’ana, ya ce, a kwai muhimmanci, duk wani dan jam’iyyar ya tashi tsaye ya rungumi sabbin shugabannin da hannu biyu, domin a ciyar da jam’iyyar gaba baki daya.

Da kuma Alhaji Jauro ya juya ga tsohon shugaban jam’iyyar APC Na karamar hukumar Zariya Alhaji Abubakar Sha’aibu Haske, sai ya jinjina ma san a yadda ya janye daga takara r sa ke neman kujerar shugabancin jam’iyyar day a ke, ya ba shi damar zama zaabben shugaban Jam’iyyar APC a karamar hukumar zariya, ya ce zai ci gaba da hada hannu da shin a ganin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’I ya ci gaba da samun goyon bayan day a dace, domin ci gaban jihar Kaduna a fannoni da dama day a sanya wa gaba.

Sauran wadanda suka yi jawabi bayan kammalazaben sun hada da Alhaji Kabiru Uba, zabababben sakataren jam’iyyar da Hajiya Hauwa’u El-Yakub, shugabar mata da Alhaji Sani Aliyu,jagoran shugabannin matasa na jam’iyyar APC na gundumomi goma sha uku na karamar hukumar Zariya.

Zaben sabbin shugabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar Zariya, ya sami halartar zababben shugaban Karahukumar hukuma Zariya, a karkashin jam’iyyar APC, Injiniya Aliyu Idris (MAGANI SAI DA GWAJI) da kuma wasu ma su wukar yankar Magana na jam’iyyar a jihar Kaduna.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: