Connect with us

KASUWANCI

Abubuwan Da Ya Kamata Masu Kiwon Dabbobi Su Fahimta

Published

on

Kiwon dabbobi shi wani al’amari ne mai sauki na kiwo, wanda ake yi a Nijeriya su kuma ‘yan Nijeriya su keyin harkar, saboda ita ma sana’a ce, idan mutum ya tsaida hankalin shi, ta hanyar ce masu kiwon suke samarwa kansu abinci.

Wani babban tagomashin da ake samu ta hanyar kiwon dabbobi  wato Tumaki shine, ba wata matsalar da ake haduwa da ita, al’amarin kiwon Tumaki. Muna yana iya kiwonsu ba tare da sun tada ma shi hankali ba.,

Malam Musa Alhassan wani kwararre ne ta bangaren kimiyyar dabbobi, wanda shi ma yana kiwon na Tumaki ne, ya bada shawarar cewar duk wanda yake son yayi kiwon Tumaki, ya dace a yanke shawarar ko su dabbobin da za a  yi kiwonsu ne , ko za a tsaresu ne, ko kuma ana bukatar su yi  kiba ne kawai.

Malam Musa ya bayyana cewar akwai Tumaki iri hudu wadanda ake kiwo a Nijeriya, wadanda suka hada da ‘’Uda’’ su kuma nan gane su net hanyar yadda suke ko dai bakake ne, ko kuma jikinsu na da ruwan kasa-kasa, da kuma akwai wata irin kamar kwalliya ce  daga goshinsu, hr zuwa tsakiyar bayansu, sai kuma, ga su kuma da manyan kunnuwa.

Sai kuma’’Balama’’  wadda yace itama kamar Udar take, amma ita kuma duk jikinta fari ne, ita ma tana da manyan kunnuwa, da kuma hanci mai tsawo suna kuma da tsawo.

Akwai kuma ‘Yankasa suma Tumaki ne, ana kuma samunsu wurare da yawa a Arewacin Nijeriya, suna kasancewa ko dai fararene, ko kuma masu ratsi ratsin baki, ko kuma ruwan kasa- kasa, ko kuma ruwan kasar,suna kunnuwa wadnada mikesuke, amma kuma su kanana ne basu kai Balama ba ko kuma Uda.

Daga karsheya kara bayyana cewar akwai gajere wadda ake kira West African Dwarf wadda Tunkiya ce, an fi samunta a Kudancin Nijeriya.

Malam Musa ya kara jaddada da akwai irin wadanda aka kawowa daga kasashen waje, ana kuma samun su ne a wurare daban daban a Nijeriya, suna kuma da girma suna da wutsiya mai fadi, saboda suna kusan taba kasa. Akwai kuma irin na kasar Sudan wadanda su gajajjera ne har ma kaho suke da shi, ko kuma wasu babu, suna kuma samar da nono mai yawa.

Idan mutum yana sha’war yin kiwon Tumaki, ya bashi shawarar ko wane Rago da Tunkiya,  saboda a samu ingantacciyar dabbar da za a Haifa, ko kuma 1:7, 1:10, amma kuma ga masu dan kkaramin karfi suna iya farawa da Rago daya da kuma Tunkiya daya.

Kwararre a bangaren kimiyyar dabbobi ya ce, ana daukar wata shida zuwa takwas lokacin da karamar Tukinya zata kai ga balaga, yayin da shi kuma Rago ya na daukare wat 10 zuwa 12 kafin ya  kai ga girma, sosai sosai.

Rabo har ila yau ya nuna Tunkiya tana daukar bkwanaki 115 ko kuma 120 kafin ta haihu, tana kuma haihuwar daya ko kuma biyu. Amma kuma yana da wuya ta haifi ‘ya’ya uku.

Danagane kuma da wurin dasu Tumakin da ake kiwo zasu ruka kwana, ya bada shawarar a barsu a wurin da ba yi mashi wani abu ba, dangane da killace su, a kuma samar masu yadda iska zai rika shiga da kuma fita, kar a sake a rika barin wurin da laima, kar kuma  abarsu rana ta damesu, duon haka ya dai kamata a aje su wurin da yake da rumfa saboda ruwan sama lokacin damina.

Maganar ‘’Kiwon dabbobi dole shi wanda yake kula dasu ya rika basu maganin macijin ciki, a kalla sau uku a shekara, ya kuam rika amfani da maganin anthelmintic, wanda za a rika badawa tsakanin wata uku zuwa hudu,  shi maganin da za a rika ba Tumaki ya danganci yadda girman Tunkiyar yake.

Sauran abubuwan yadda za a rika kulawa dasu dabbobin shine a rika kulawa da lafiyarsu, ta hanyar allurar rigakafi, kda yake dai ana iya samun wasu alluran, wadanda ba a iya samunsu anan Nijeriya.

Dangane da irin abincin  da ya kamata  abasu, ba a ce dole sai an samu wani ba, idan kuma ba a same shi ba, to shkenan, amma ya kamata  arika basu abinci da ruwa.

Malam Musan yace abincin da ake ba Tumaki ya kamata ya kunshi ciyawa, fulawar alkama, kulikuli da kuma, ganyen danakalin gida da kuma na Turawa, da kuma ciyawa kamar raugar wake, da kuma karan dawa.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: