Connect with us

WASANNI

Ba Zan Bar Real Madrid Ba, Cewar Isco

Published

on

 

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Isco, ya bayyana cewa ko kadan baya tunanin barin kuniyar kwallon kafa ta Real Madrid saboda yanajin dadin zama a kungiyar a halin yanzu.

A watannin baya dai an danganta Isco da komawa zakarun gasar firimiya wato Manchester City bayan da mai koyar da kungiyar, Pep Guardiola ya bayyana Isco a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasa Dabid Silba wanda shima dan kasar Sipaniya.

Isco dai ya buga wasanni 29 a wannan kakar sannan kuma wasanni 5 kawai aka buga minti 90 din dashi wanda hakan yake nufin bashi da tabbas ko za’a fara wasan karshe dashi a wasan karshe na gasar zakarun turai da kungiyarsa zata fafata da Liberpool sati mai zuwa.

A kwanakin baya dai Isco ya bayyana bakin cikinsa bisa yadda mai koyar da yan wasan kungiyar, Zidane baya amfani dashi yadda yakamata kuma kasarsa ta Sipaniya tana bashi cikakkiyar dama.

A karshe dan wasan ya ce har yanzu matashin dan wasa ne kuma yana son wasansa yaci gaba saboda haka yana zaune a kungiya babba.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: