Connect with us

SIYASA

Babu Gaskiya Babu Adalci A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna –Wusono

Published

on

“Wannan zabe ne ko nadi? domin zabukan da aka yi a wasu wuraren ba a yi zaben ba, amma an bayar da sakamako. Misali inda ni na fito, Karamar hukumar igabi akwatuna 360 ne, amma inda aka sanya akwaunan kila sun kai 60, kila fa, wajen 300 nan ba inda aka sanya akwati, akwai tawa mazabar, kalan akwatin ma mutane ba su gani ba, Kerawa, Gwaraje, Zangon Aya an kai wasu ba a kai wasu ba, Rigachikun, an zo da kayan ba a ma sauke a mota ba aka wuce da su wani wurin, Giwa ba a ma yi zaben ba, a Jihar Katsina ne aka kwashe akwatunan aka kai su.” Wadannan kalaman sun fito ne daga bakin, Aliyu Ibrahim Wusono, magatakardan Jam’iyyan PDP nan Jihar Kaduna.

Wusono ya ci gaba da cewa, “Inda kuma aka yi zaben, to duk inda PDP ta ci ba a bayar da sanarwar ta ci da wuri ba sai abin ya kai wani irin hali na makura. Misali karamar hukumar Kaduna ta Kudu, karshe an soke mazabu biyu ne saboda sun yi duk yanda za su yi su murde zaben mutanan suna da wayo sun tsaya sun tsare, har ta kai ga an tara malaman zaben a wani Otal, mutanan suka bi su suka fatattake su daga wajen, daganan abin da kawai muka sake ji shi ne wai an soke sakamakon wadannan mazabu biyun.

Sannan a Chikun, muna da Kansiloli takwas, amma sai aka ce zaben Kansilolin ya yi daidai na Shugaban karamar hukuma bai yi daidai ba. aka sanar da sakamakon na Kansilolin, amma aka ce za a sake na Shugaban karamar hukuma a mazabu guda biyar. Kajuru mun ci zabe da Kansiloli tara, amma yanzun an ce an soke zaben nan wai wani zaben ne za a sake. Kagarko, jami’in hukumar zabe na karamar hukuma ya bayar da sanarwar mun ci zabe, amma ita kuma Shugabar hukumar zabe ta ce a’a, ga wanda suke so. Sanga, tun da aka yi zaben malamin zaben sai ya bace, mutanan karamar hukumar da suka kada kuri’a, sai da suka kwashe kwanaki shida suna neman malamin zaben domin ya bayar da sanarwa, an bayar da sanarwar na Kansiloli amma ba a ga malamin zabe ba ya bayar da na Shugaban karamar hukuma. Mutanan sun rubuta takardar koke sun kai ma hukumar zaben mu ma mun rubuta mun kai cewa tunda ga sakamakon zaben a kasa hukumar ta nada wani yaje ya karanta sakamakon zaben ya bayar da sanarwa kamar yadda dokar zaben ta tanada, ba su yi ba, sai kawai ji muka yi sun ce wai sun baiwa Jam’iyyar APC.

In ka zo nan karamar hukumar Igabi kamar yadda na ce, ba a yi zaben ba amma an fadi sakamako, haka Giwa, hakanan in ka je Kubau ga sakamakon amma an canza mafi yawa na Kansiloli, na Shugaban karamar hukuma an yi aikin karfi da ‘yan ta’adda, mu abin da ya fi ba mu takaici, hadin bakin nan har da jami’an tsaro ake wadannan abubuwan da ba su dace ba.

A karshe mun lissafa muna da kananan hukumomi akalla 15 wadanda Jam’iyyar PDP ce ta ci zabe a cikin su, amma an ki sanarwa, sai guda hudu ne kawai suke bayar da sanarwar PDP ta samu. Mu kuma mun shiga zabe ne saboda mun ji gwamna ya ce zai yi adalci, inda mun san ba da gaske yake yi ba ba zai yi adalci ba da ba mu shiga wannan zaben ba. To amma an yi zaben, mun shiga zaben kuma Alhamdu lillahi duniya ta san mun ci zaben amma wajen bayar da sakamakon zaben sai aka ajiye sakamakon a gefe aka nada wani daban, shi kanshi wanda aka nadan ya san shi ba zababbe ne ba, shi nadadadden gwamnati ne. To abin da ya fi bata mana rai ya fi ba mu takaici, yanda muke ganin mutuncin ita shugabar hukumar zaben nan da yadda ta bamu tabbacin ita ba za a yi amfani da ita wajen karya doka ba, wajen cin mutunci ba, wajen cin amana ba. Amma abin mamaki sai ga ta da kanta, tare da ta san in dai ga jami’in zabe, to doka ba ta ba ta hurumin sanar da sakamakon zabe ba, sai ta zo tana bayar da sakamakon zabe bisa wasu dalilai wadanda ba mu gamsu da su ba, ba kuma ma mu yarda da su ba. Sun boye malaman zabe suka ce sun bace saboda mutane sun zabi PDP, wanda ta ce wannan ya ba ta daman ta fadi sakamakon zabe.

Gaskiyar magana a Jihar Kaduna ba a shirya gaskiya ba, ba a yi adalci ba, kuma mu muna nan kan zabukan da aka ce za a sake ko a ina ne muna cikin zabe, mun yarda mu ci zaben a nada wani, amma duniya ta san PDP ce ta ci zabe amma an nada wani, wannan shi ne aniyarmu. Sannan kuma mu tabbatar wa duniya cewa maganan da gwamnan Jihar Kaduna ke fada ba gaskiya ne ba, yaudara ne, ha’inci ne, cin amana ne, kuma ba da gaske yake ba. kuma su yarda cewa duk maganan da zai furta masu ka da su yarda, su tsaya su ga abin da zai aiwatar kafin su yarda da shi.

Maganan kuma na’uran zaben, wannan ta ma fi kowace hanya saukin a yi magudi da ita, saboda ba ta da wani abu da zai tantance cewa mutum daya ne ya jefa kuri’a, mutum daya ma yana iya dangwale kuri’ar akwatin gabadaya. To mu duk ‘yan Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna sun jajirce ne ta yadda duk inda aka yi nufin yin magudi ba zai yiwu ba, shi ya sanya aka sami wannan nasarar.

Saboda haka mu a Jihar Kaduna, farko muna wa Allah godiya,  na biyu muna ma al’ummar Jihar Kaduna godiya, bisa irin goyon bayan da suka baiwa Jam’iyyar PDP a wannan zaben da ya gabata. Wannan ya nu na wa duniya cewa, Jam’iyyar PDP tana nan da karfin ta a Jihar Kaduna.

Da yake amsa tambayar ko akwai wasu matakai da suke shirin dauka kan sakamakon da ita hukumar zaben ta bayyana? Magatakardan na Jam’iyyar ta PDP cewa ya yi, tabbas, mu da muke da sakamakon zabe a hannunmu. Misali, in ka dauki karamar hukumar Kagarko, ga sakamakon zabe a akwati, ga sakamako na mazaba, ga sakamako na karamar hukuma, me zai hana mu zuwa Kotu? Ka dauki Lere, ga sakamakon mazabu duka duk mun cinye amma wajen bayar da sanarwa abin takaici Farfesa da ake ganin kimar Farfesa, amma da aka gama kada kuri’a a karamar hukumar Lere Farfesan nan ya gudu ya ki bayar da sakamakon zabe, wannan abin kunya da takaici ne. yanzun muna son mu gani ne, sashen shari’a na Jihar Kaduna ita ma za ta yi aiki da umurnin gwamnati ne, ko kuwa za ta yi aiki da shari’a na gaskiya? Don haka duk za mu tattara wadannan abubuwan da suka faru mu gurfana a gaban kuliya tare da su. Wannan shi ne matakin da mu muka dauka, wuraren da za a sake zabe za  mu je mu shiga zabe, amma duk sauran da muke da hujjojin mu, mun shirya Kotu muka nufa.”

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: